19/10/2025
ELKANEMI WARRIORS TA DOKE WIKKI TOURISTS DA CI 2–1 A MAIDUGURI
Kungiyar Elkanemi Warriors ta samu nasara a gida bayan ta doke Wikki Tourists ta Bauchi da ci 2–1 a wasan NPFL26 Matchday 9 da aka buga a filin wasa na Elkanemi da ke Maiduguri.
Wasan ya kasance mai cike da zafi da gogayya, inda Wikki Tourists ta fi rinjaye a ɓangaren mallakar kwallo, amma ta kasa amfani da damar da ta samu bayan tafaɗa cikin rashin sa’a a farkon wasa.
Elkanemi ta zura kwallon farko ne a minti na 9 ta hannun Emmanuel Jonas, wanda ya ci daga cikin akwatin Wikki bayan rikice-rikicen da ya biyo bayan bugun kusurwa. Sai kuma a minti na 36, Samaila Bello ya kara na biyu ga masu masaukin baki bayan wata gaggawar kai hari da ta rikita tsaron Wikki.
Da yake ƙoƙarin dawo da martaba, Wikki Tourists ta samu nasarar rage tazarar cin a minti na 45 ta hannun Abdullahi Usman (Pepe), wanda ya ci daga kyakkyawan taimako da Jonathan Mairiga ya bayar kafin a tafi hutun rabin lokaci.
A zagaye na biyu, Wikki Tourists ta mamaye fili sosai, tana taka kwallo da natsuwa da kwarewa, amma duk da hakan, kwallon da za ta kawo daidaito ta ki shiga. Tsaron Elkanemi Warriors ya tsaya daram har zuwa minti na ƙarshe, inda s**a kare da nasarar gida.
Da yake bayyana ra’ayinsa bayan kammala wasa, Koci Abdu Maikaba na Wikki Tourists ya ce yana takaicin sakamakon, duk da cewa ‘yan wasansa sun nuna jajircewa da kwazo.
Ya kuma yabawa ingancin alkalancin wasannin bana na NPFL, yana mai cewa hukumar ta nuna gaggawa wajen gyara kura-kurai a wasu wasanni da s**a gabata.
Shi ma kapitan kungiyar, Mohammed Guda, ya ce rashin sa’a ce ta hana su tashi da maki daga Maiduguri, amma yana da kwarin gwiwar cewa ƙungiyar za ta dawo da kuzari a wasannin gaba.
Da wannan sakamako, Wikki Tourists za ta mayar da hankali kan wasan Matchday 10, inda za ta karɓi Shooting Stars (3SC) daga Ibadan a Bauchi wasa mai matuƙar muhimmanci domin neman dawowa kan turbar nasara a gaban masoyan ta.
-Zamani TV