30/12/2023
63 + 10 + 13 + 40.....
---------------------------------------
Shi mai gidan mu Annabi Muhammad (S.A.W) shekaru 63 yayi masu albarka. A zamanin nan namu na calculation da lissafe lissafe ai ba baza mu gaza lissafo shekarun Mai Gidan mu Mathematically daga Al-Qur'ani ba, eh mana...❤️ Toh ai normal ne mu wasa Kwakwalwa ko a cikin Surori uku ne.
~ Suratu Yunus, Suratur Ra'ad da Suratul Ghaafir, acikin su akwai wata kalma guda daya wacce aka maimaita ta a cikin kowace Surah daga cikin ukun, itace kalmar ﻧﺘﻮﻓﻴﻨﻚ (Nata waffayan naka), abin nufi "Za mu dauki ranka", wannan kalmar "Nata waffayan naka" tazo a wurare uku acikin Al-qur'ani wanda take magana game da rasuwar manzon Allah, wuri na farko shine Suratu Yunuss Surata 10, an kawo kalmar ﻧﺘﻮﻓﻴﻨﻚ
~ Wuri na biyu, Suratur Ra'adi, Surah ta 13, an kawo kalmar ﻧﺘﻮﻓﻴﻨﻚ
Wuri na uku itace Suratul Gaafir, Surah ta 40, kalmar ta sake zuwa.
Ga Ayoyin a jere kamar haka👇
1. ﻭَ ﺇِﻣَّﺎ ﻧُﺮِﻳَﻨَّﻚَ ﺑَﻌْﺾَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﻌِﺪُﻫُﻢْ ﺃَﻭْ ﻧَﺘَﻮَﻓَّﻴَﻨَّﻚَ ﻓَﺈِﻟَﻴْﻨَﺎ ﻣَﺮْﺟِﻌُﻬُﻢْ ﺛُﻢَّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺷَﻬِﻴﺪٌ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻠُﻮﻥَ
Suratu Yunus, Aya ta 36👇
2. ﺇِﻣَّﺎ ﻧُﺮِﻳَﻨَّﻚَ ﺑَﻌْﺾَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﻌِﺪُﻫُﻢْ ﺃَﻭْ ﻧَﺘَﻮَﻓَّﻴَﻨَّﻚَ ﻓَﺈِﻧَّﻤَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻚَ ﺍﻟْﺒَﻠَﺎﻍُ ﻭَ ﻋَﻠَﻴْﻨَﺎ ﺍﻟْﺤِﺴَﺎﺏُ
Suratur Ra'adi, Aya ta 40👇
3. ﻓَﺎﺻْﺒِﺮْ ﺇِﻥَّ ﻭَﻋْﺪَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺣَﻖٌّ ﻓَﺈِﻣَّﺎ ﻧُﺮِﻳَﻨَّﻚَ ﺑَﻌْﺾَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻧَﻌِﺪُﻫُﻢْ ﺃَﻭْ ﻧَﺘَﻮَﻓَّﻴَﻨَّﻚَ ﻓَﺈِﻟَﻴْﻨَﺎ ﻳُﺮْﺟَﻌُﻮﻥ
~ Suratul Ghaafir, Aya ta 77 kamar yadda aka sani Manzon Allah ya rasu yana da shekaru 63 ne, toh ka duba da kyau zaka ga Surorin da aka yi maganar mutuwar Manzon Allah da kalmar ﻧﺘﻮﻓﻴﻨﻚ guda uku ne:
Surah ta 10.
Surah ta 13.
Surah ta 40.
Toh ka hada su ka lissafa
10 + 13+ 40 = 63.
~ Shekarun da yayi kenan a duniya, 63. Mathematically, indirectly Al-Qur'ani ya nuna shekarun da Mai Gidan namu yayi.
~ Idan muka koma Suratul Gaafir, Aya ta ta 77 din, zamu ga itace Surah ta farko daga 'kasa da aka fara ambaton kalmar "Nata waffayan naka", idan ka kirga haruffan dake cikin Ayar zaka ga haruffa ne guda 63 dai dai, ka lissafa har da wurin da aka yi (Shadda), kamar yadda ka sani duk inda kaga shadda to haruffa biyu ne aka manne su wuri daya.
~ Bari mu shiga kwanar dama mu leka za muga Ayar da ta fara maganar rasuwar Manzon Allah da kalmar "Nafa waffayan naka" tana da haruffa 63 cif, adadin shekarun da yayi kenan a duniya (S.A.W).
Allahu Akbar.
~ Haka kuma idan muka mike muka je kusa da Bakin Bodar Surah ta 40 zamu ga cewa ko a tarihi Manzon Allah ya rayu shekaru 40 kafin a fara yi masa wahayin Al-Qur'ani, indirectly kamar ana nufin Surah ta 40 wato Suratul Ghaafir da muka yi magana game da ita a sama, Surah ta 40 itama tana cikin surorin da aka kawo kalmar "Nata waffayan naka", kamar ana ishara da shekaru 40 da yayi kafin a fara masa wahayin Al-Qur'ani.
~ Haka kuma idan ka lura da tarihin manzon Allah zaka ga cewa bayan an fara yi masa wahayin Al-Qur'ani ya zauna a Makkah tsawon shekaru 13, indirectly kamar Al-Qur'ani yana magana da Surah ta 13 da muka yi magana akan ta da farko , wanda itama an kawo kalmar "Nata waffayan naka" a cikin ta.
~ Bayan ya bar Makkah ya koma Madinah, ya rayu acan tsawon shekaru 10, Surah ta 10 kenan da muka yi magana game da ita da farko
1. Rayuwar sa kafin Annabta - shekaru 40.
2. Rayuwar sa a Makkah - shekaru 13.
3. Rayuwar sa a Madinah - shekaru 10.
Surah ta 40
Surah ta 13
Surah ta 10
Idan ka hada zai baka shekaru 63.
Daga nan manzon Allah ya bar duniyar (Allah ya kara masa yarda, mai gidan mu Annabi Muhammad (S.A.W), ko baka son sa ka more shi....
~ So da kaunar kadai Ibada ce me zaman kanta da zata kaika Aljannah ko shakka babu.....
Copied...😎😎