
05/11/2024
MUHIMMIYAR SANARWA...!!!
Wa'azin Forum a garin Miya...
Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah reshen Miya Malam Halliru Muhammad, na farin cikin gayyatar daukacin al'ummar Musulmi zuwa wurin gagarumin Wa'azin hadin gwuiwa na Forum wanda ya saba gudana a duk karshen wata tsakanin kananan hukumomi uku na jihar Bauchi (Ganjuwa, Ningi da Warji) da kananan hukumomi hudu na jihar Jigawa (Birnin~Kudu, Buji, Dutse da Gwaram).
Gagarumin Wa'azin zai gudana ne kamar haka:
✓ Rana:
Juma'a 6/Jumada~Ula/1446AH (8/11/2024)
✓ Lokaci:
5:00 na yamma
✓ Wuri:
Filin Masallacin Center Miya, Ganjuwa LGA Bauchi State
Allah ya bada ikon halarta, Ameen.