
10/08/2025
Gwamnati Ta Kashe Naira Biliyan 88 Wajen Gyaran Kayan Wutar Lantarki Da Aka Lalata Tun Daga 2021
Gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 88 wajen gyara da dawo da wuraren samar da wutar lantarki da aka lalata a fadin kasar nan tsakanin shekarar 2021 zuwa yanzu.
Babban mai kula da layukan wutar lantarki na kamfanin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) reshen Legas, Seyi Onabajo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a tashar wutar lantarki ta Odogunyan 132KV, dake Ikorodu, a jihar Legas.
Onabajo ya ce adadin kudin da aka kashe kan gyare-gyaren ya yi matukar yawa, inda ya bayyana cewa maimakon a yi amfani da kudaden da aka samu daga yan kasa da gwamnati wajen inganta hanyoyin samar da wuta, sai ake amfani da su wajen gyara lalacewar da ta biyo bayan ta’addancin wasu bata gari a wuraren samar da wutar lantarki. Ya ce wannan matsala ce ke shafar yunkurin samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24 a kowace rana.
Ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen kare kayayyakin samar da wutar lantarki a yankunansu, yana mai jaddada cewa duk wani hari da ake kai wa kayan aikin na rage damar samar da wutar da kuma jinkirta shirin tabbatar da cewa dukkan yan Najeriya sun samu wadatar wutar lantarki yadda ya kamata.