02/03/2026
KWAMITIN KASAFIN KUƊI NA MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI YA FARA BINCIKEN KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 8.16 NA KARAMAR HUKUMAR DASS A 2026.
Kwamitin Kasafin Kuɗi da Kula da Kasafi na Bauchi State House of Assembly ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da bin ƙa’idojin kashe kuɗi da gudanar da aiki cikin gaskiya da riƙon amana, yayin da ya fara nazari kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Ƙaramar Hukumar Dass da ya kai Naira 8,163,525,195.22 (Biliyan Takwas da Miliyan Dari da Sittin da Uku da Dubu Dari Biyar da Ashirin da Biyar da Dari da Casa’in da Biyar da Kobo Ashirin da Biyu).
Shugaban Kwamitin, Hon. Wanzam Mohammed, ya bayar da wannan tabbaci a ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026, yayin zaman kare kasafin kuɗin tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Dass, Muhammad Abubakar Jibo. Ya jaddada cewa Majalisar na tsaye tsayin daka wajen kare dukiyar jama’a, tabbatar da rarraba albarkatu yadda ya kamata, da kuma inganta ci gaban al’umma a faɗin jihar.
A cikin gabatarwarsa, Comr. Jibo ya bayyana cewa za a samu kuɗaɗen kasafin ne daga ragowar kuɗi na Naira 1,520,000.00 (Miliyan Daya da Dubu Dari Biyar da Ashirin); rabon FAAC na Naira 6,724,847,169.22 (Biliyan Shida da Miliyan Dari Bakwai da Ashirin da Hudu da Dubu Dari Takwas da Arba’in da Bakwai da Dari da Sittin da Tara da Kobo Ashirin da Biyu); kuɗaɗen shiga na cikin gida Naira 87,581,652.00 (Miliyan Tamanin da Bakwai da Dubu Dari Biyar da Tamanin da Daya da Dari Shida da Hamsin da Biyu); tallafi da gudummawa Naira 162,179,068.00 (Miliyan Dari da Sittin da Biyu da Dubu Dari Daya da Saba’in da Tara da Sittin da Takwas); da Asusun Ci gaban Ayyuka na Naira 1,187,397,306.00 (Biliyan Daya da Miliyan Dari da Tamanin da Bakwai da Dubu Dari Uku da Casa’in da Bakwai da Dari Uku da Shida).
Dangane da kashe kuɗi, an ware Naira 823,268,220.26 (Miliyan Dari Takwas da Ashirin da Uku da Dubu Dari Biyu da Sittin da Takwas da Dari Biyu da Ashirin da Kobo Ashirin da Shida) domin albashin ma’aikata, da Naira 520,806,785.96 (Miliyan Dari Biyar da Ashirin da Dubu Dari Takwas da Shida da Dari Bakwai da Tamanin da Biyar da Kobo Casa’in da Shida) domin alawus-alawus. An kuma ware Naira 392,526,798.00 (Miliyan Dari Uku da Casa’in da Biyu da Dubu Dari Biyar da Ashirin da Shida da Dari Bakwai da Casa’in da Takwas) domin fansho da hakkokin ritaya, inda ake kashe kusan Naira miliyan 45 a kowane wata wajen biyan fansho. Jimillar kuɗin da ake kashewa kan ma’aikata ya kai kusan Naira miliyan 200 a wata, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.4 a shekara.
Kashe kuɗin ayyukan raya kasa (Capital Expenditure) ya kai Naira 4,408,471,634.00 (Biliyan Hudu da Miliyan Dari Hudu da Takwas da Dubu Dari Hudu da Saba’in da Daya da Dari Shida da Talatin da Hudu), domin bunƙasa ababen more rayuwa da ci gaban tattalin arziki.
Manyan ɓangarorin da aka ware wa kuɗi sun haɗa da Gudanarwa Naira 1,358,813,845.00 (Biliyan Daya da Miliyan Dari Uku da Hamsin da Takwas da Dubu Dari Takwas da Goma Sha Uku da Dari Takwas da Arba’in da Biyar); Noma Naira 375,000,000.00 (Miliyan Dari Uku da Saba’in da Biyar); da Kuɗi Naira 100,000,000.00 (Miliyan Dari Daya).
Sashen Haraji da Kuɗaɗen Shiga zai samu Naira 248,000,000.00 (Miliyan Dari Biyu da Arba’in da Takwas), yayin da Ayyuka da Gidaje zai samu Naira 1,227,589,172.00 (Biliyan Daya da Miliyan Dari Biyu da Ashirin da Bakwai da Dubu Dari Biyar da Tamanin da Tara da Dari Daya da Saba’in da Biyu). Sashen Tsare-tsare da Kasafi zai kashe Naira 149,750,000.00 (Miliyan Dari Daya da Arba’in da Tara da Dubu Dari Bakwai da Hamsin).
A ɓangaren Ilimi da Ci gaban Jama’a an ware Naira 390,118,597.00 (Miliyan Dari Uku da Casa’in da Dubu Dari Daya da Goma Sha Takwas da Dari Biyar da Casa’in da Bakwai). Fannin Lafiya kuwa zai samu Naira 349,000,000.00 (Miliyan Dari Uku da Arba’in da Tara), wanda ya kai kashi 8 cikin 100 na kasafin baki ɗaya, domin kula da lafiyar matakin farko. Haka kuma an ware Naira 210,200,000.00 (Miliyan Dari Biyu da Goma da Dubu Dari Biyu) domin ayyukan Ruwa, Tsafta da Lafiya (WASH).
A ƙarshe, Comr. Jibo ya bayyana cewa kasafin ya yi daidai da manufofin “My Bauchi Project 2.0” na Senator Bala Abdulkadir Mohammed, tare da nuna fatan Majalisar za ta amince da shi domin ci gaban al’ummar Ƙaramar Hukumar Dass.
Zakariyya Aliyu Gwaram
New Media Unit,
Information and Publication Directorate
BAHA
2nd March,2026