
08/07/2025
ASUU ta fara yajin aiki a fadin ƙasar sak**akon rashin biyan albashi.
Ƙungiyar Malamai ta Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta umurci mambobinta a jami’o’in tarayya da na jihohi da su dakatar da ayyukansu a fadin ƙasar, bayan da gwamnati ta ƙi biya albashin watan Yuni 2025, wanda ya wuce kwanaki 3 ba tare da an biyan ba wanda hakan ya sanya ƙungiya ta ayyana ƙa'idar yajin aikin “ba a biya ba, ba a aiki ba” .
Prof. Chris Piwuna, shugaban ƙasa na ASUU, ya bayyana cewa wannan jinkiri ba saboda matsalar fasaha ba ne, sai dai saboda rashin mayar da kuɗaɗen ga jami'o'i, wanda hakan ya sanya malaman suke bin gwamnatin kimanin Naira biliyan 10 na ƙarin hakkokin da ba'a biya ba .
A Jami’ar Jos (UNIJOS), Shugaban reshen ASUU, Prof. Jurbe Molwus, ya sanar da shiga yajin aiki tun daga 4 ga Yuli 2025, saboda ba a biya albashin Yuni ba haka ma Jami’o'in Abuja (UniAbuja) da ATBU Bauchi sun bi sahun wajen dakatar da ayyukansu bisa wannan sharadi.
-Zamani TV