Khadimul Faidha Media Team Of Nigeria

Khadimul Faidha Media Team Of Nigeria Wannan Page an kirkirshi ne Dan Yadawa Abubuwa da S**a Shafi Addinin Musulunci, Darika Da Faidha

22/10/2025

Duk Masoyin Manzon Allah S.A.W
Baya Goyon Bayan Daga Wannan Taro Na Yaumul Rasul
Kaifa? Kefa? Kufa?

22/10/2025

Shawari ga Shuwagabannin Tsaro Suzo Su Bada Tsaro Ranar Taron Yaumul Rasul Ba Dagawa Bane Mafita

22/10/2025

Bama Goyon Bayan Daga Wannan Taro Na Yaumul Rasul
Babu Dalilin da Zaisa a bar Maqiya Annabi Sunayin Abin da S**a ga Dama

Annabin dai S.A.W
21/10/2025

Annabin dai S.A.W

Masoya Manzon Allah S.A.W Kano Tayi Kira fa
21/10/2025

Masoya Manzon Allah S.A.W

Kano Tayi Kira fa

GAYYATAR MAULUDIN ANNABI (S.A.W) 🌙Sayyada Sharifa Hallum Haidara tare da iyalinta suna cikin farin ciki da gayyatar ku z...
21/10/2025

GAYYATAR MAULUDIN ANNABI (S.A.W) 🌙

Sayyada Sharifa Hallum Haidara tare da iyalinta suna cikin farin ciki da gayyatar ku zuwa Mauludin Annabi Muhammadu (S.A.W), a Abuja ranar Jumma’a 24/11/2025.

Sharifiyace — jinin Ma’aiki (S.A.W), zuriyar Sayyidatina Fatima Zahra (R.A) da Sayyidina Ali (R.A).
Ta fito daga gidan da hasken Annabci ke tashi, gidan da rahma da nutsuwa s**a mamaye.

Ku zo mu yi murna da haihuwar Rasulullahi (S.A.W) — rahma ga dukkan halitta. 🌹

21/10/2025

Yaumul Rasul 26 Oct, 2025
21/10/2025

Yaumul Rasul 26 Oct, 2025

HIMMA BATA GA RAGO 🌟Alhamdulillah, a yau Khadimul Faida Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sauka lafiya a gari...
21/10/2025

HIMMA BATA GA RAGO 🌟

Alhamdulillah, a yau Khadimul Faida Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sauka lafiya a garin Kano!

Ba tare da kasala ko gajiyawa ba, Malamin Rahma ya nufi garin Kano domin ziyartar kwamiti na shirya babban taron “1 Million Match” wanda aka shirya domin Annabi Muhammad ﷺ.

Wannan tafiya tana nuna mana yadda ƙaunar Annabi ﷺ ke cika zuciyar Khadimul Faida, domin koda gajiyar tafiya tana jikinsa, bai yi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa duk wani abu da ya shafi Annabi Mai rahma ﷺ.

Hakika, wannan shi ne misalin himma, sadaukarwa da gaskiya a cikin hidimar Annabi ﷺ.
Allah ya ƙara masa lafiya, ya tabbatar da ƙafafunsa akan tafarkin Annabi ﷺ, kuma ya sanya wannan tafiya cikin abin da zai ƙara ɗaukaka Annabi da Musulunci gaba ɗaya.

Yaumul Rasul Yaumul Rasul Taro ne da Ya Hada Dukkanin Qungiyoyi da Mazhabobi Masoya Allah Masoya Manzon Allah S.A.W, Wan...
21/10/2025

Yaumul Rasul

Yaumul Rasul Taro ne da Ya Hada Dukkanin Qungiyoyi da Mazhabobi Masoya Allah Masoya Manzon Allah S.A.W,

Wannan Taro ne Wadda Dukkanin Yan'uwa Musulmai S**a Shirya, Wadda a Kalla ana Tunanin Sama da Mutum 1million ne Zasu Halarci Wannan Taro a jihar Kano, Ranar 26 Oct, 2025

Taron Masoya Manzon Allah S.A.W Ne S**a Shirya, Sun Shirya Shine Badan Komai ba Sai Don Samun Nutsuwa da Jaddada Soyayyar mu ta Manzon Allah S.A.W a Zukatanmu, Mu Masoya Manzon Allah S.A.W

Alhamdulillah Muna Goyon Bayan Duk Wani Abu da akace an Shirya Shine Don Girmama Manzon Allah S.A.W Muddin Bai Saba Ma Shari'a ba

Wannan Taro ba Tarone na Siyasa ba, Ko Tozarta Wani Mutum, Ko na Cin Mutumcin Wani, Tarone Na Jaddada Soyayyar Shugaban Mu Abin Sonmu Abin Kaunarmu Annabi Rahama Annabi Muhammadu S.A.W

Ina Amfani da Wannan Dama Muna Kira ga Mahalarta Wannan Taro da Su Guji duk Wani Abu da Zai Tada Hankali, Su Kuma Bada Haɗin kai a Jami'an Tsaro Don ayi Wannan Taro Lafiya a Tashi Lafiya

Muna Rokon Allah Ya Tsare Mana Imaninmu
Allah Ya Tsare Mana Mutumcin mu
Allah Ya Kara Mana Soyayyar Shugaba Annabi Muhammadu S.A.W

Allah Yasa Ayi Wannan Taro Lafiya a Tashi Lafiya

Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Chairman
Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation
21 Oct, 2025

Address

Wunti Street Bauchi
Bauchi
740102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khadimul Faidha Media Team Of Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share