09/09/2025
Ƙorafin Canjin Miji Bayan Aure
Yawancin mata suna cewa: “Mijina ya canza tun bayan da muka yi aure, ba irin yadda yake da ni kafin aure ba.” Amma gaskiya ita ce, sau da yawa ita matar ma ta canza ba tare da ta lura ba.
Da farko kafin aure, miji ya saba zuwa ya same ki a gida cikin tsafta, sanye da kaya masu kyau, ƙamshi yana tashi, kin yi ado kin yi shigar mace ta musamman. Amma bayan aure, musamman bayan haihuwa, abubuwa suna sauyawa.
• Adon da kika saba yi, sai ya ragu.
• Tsafta ta gida sai ta fara samun matsala saboda gajiya ko sakaci.
• Kiran suna mai daɗi da kika saba yi masa kafin aure (“Honey, Sweetheart, Ango na”) sai ya canza zuwa “Kai”, ko kuma kawai idan kina buƙatar kuɗi.
• A maimakon murmushi da nishaɗi, kullum sai kuka da korafin “ba kudi, ba wane abu, ba wane abu.”
A hankali, miji ma yana jin kamar abubuwa sun canza a wurin ki. Idan ya rasa nishaɗi, tsafta, da kulawar da ya saba samu a wurin ki, ba abin mamaki bane idan shima ya sauya halayya ko kuma ya rage ƙoƙarinsa.
Mata na da muhimmiyar rawa wajen riƙe da gidan aure. Eh, gaskiya akwai wahalar haihuwa, akwai gajiya, akwai rashin kuɗi, amma idan mace ta yi ƙoƙari ta kiyaye tsafta, ta ci gaba da nuna soyayya da mutunci, aure yakan yi daɗi sosai.
Miji baya buƙatar abu mai tsada kullum, wani lokaci kalaman kirki, kallo da murmushi, da ɗan shigar ado mai kyau, shi kaɗai ya isa ya sa zuciyarsa ta huce.
Idan kina so mijinki ya kasance kamar yadda yake kafin aure, to ke ma ki ci gaba da kasancewa irin matar da ya gani kafin aure. Aure ba ya tafiya da soyayya kawai; yana tafiya da ƙoƙari, fahimta, da kula da juna.
A ƙarshe: Mata ku daina sa ran mijin ku ya kasance cikakke, ku ma ku yi ƙoƙarin zama cikakkun abokan tafiyarsa. Idan kowa ya gyara nasa gefe, gida ya kan zauna lafiya.
—Rubutun; Maryam Ibrahim Bununu