13/11/2025
Ɗaruruwan Al’umma Sun Halarci Taron Khatamar Mauludin Manzon Allah (S) a Alƙaleri
A daren Laraba, 12 ga Nuwamba, 2025, ɗaruruwan al’umma daga sassa daban-daban na Alƙaleri sun halarci taron Khatamar Mauludin Manzon Allah (S) da almajiran Shaikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky (H) s**a shirya a filin makarantar firamare ta Alƙaleri.
Taron ya gudana cikin natsuwa da tsari, inda aka fara da bude taro daga babban limamin masallacin Juma’a na Maimadiri, sai karatun Alƙur’ani daga Malam Tasi’u, sannan Malam Ashiru Murtala Kazaure ya jagoranci ziyarar Manzon Allah (S).
An samu gagarumar gudanarwa daga kungiyoyi da dama ciki har da Ittahadu Shu’ara, Harisawa, ƴan Taekwondo, ƴan Intizar, da ƴan Fudiyya Alƙaleri waɗanda s**a gudanar da fareti domin girmama Manzon Allah (S).
Babban jawabin taron ya fito daga bakin Shaikh Muhammad Adamu Abbare (Gombe), wanda ya jaddada cewa mafitar al’umma tana cikin komawa ga sakon Allah da ManzonSa (S) wato Alƙur’ani Mai Girma. Ya kuma yabawa Shaikh El-Zakzaky kan jajircewarsa wajen kare gaskiya duk da wahalhalu da ya fuskanta.
Taron ya ƙare lafiya, inda mahalarta s**a godewa Allah bisa nasarar gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana.
RAHOTO: SULAIMAN ALKALERI