
22/05/2025
Matasan Bauchi Ta Arewa Sun Roki Siraj Ibrahim Tanko Ya Sake Neman Kujerar Sanata a 2027
Matasan Bauchi T Arewa sun bayyana roƙon su ga tsohon ɗan takarar Sanatan Bauchi Ta Arewa a zaɓen 2023, Siraj Ibrahim Tanko, da ya sake tsayawa takara a babban zaɓen 2027. Wannan ƙiran na zuwa ne sak**akon gazawar Sanata Sama’ila Dahuwa Kaila, wanda ke wakiltar shiyyar a halin yanzu, wajen samar da ci gaba tun daga lokacin da aka rantsar da shi har zuwa yau.
A cikin wata sanarwa da Matasan s**a fitar bayan wani taron gaggawa da s**a gudanar, matasan sun nuna damuwa kan yadda yankin Bauchi Ta Arewa ke fuskantar koma baya a fannoni da dama na rayuwa.
“Muna roƙon Siraj Ibrahim Tanko da ya saurari kiran al’umma, ya sake fitowa takara a 2027. Shi matashi ne mai kwazo da hangen nesa, kuma muna da tabbacin cewa zai wakilci yankinmu da cancanta da gaskiya,” in ji shugaban Matasan, a cikin sanarwar.
Matasan sun bayyana cewa ƙoƙarin da Siraj Ibrahim Tanko ya yi a baya, da irin goyon bayan da ya ke samu daga matasa da dattijon yankin, su ne ke karfafa masu gwiwar neman dawowarsa fagen siyasa. Matasan sun bayyana cewa sun himmatu wajen ganin an dawo da martabar wakilci na gaskiya a yankin, ta hanyar goyon bayan Siraj Ibrahim Tanko a zaɓen mai zuwa.