29/07/2025
ANA NEMAN CINYE MU DA YAKI
A daidai lokacin da hankulan Malaman addinin Musulunci ya karkata zuwa kan siyasar Demokaradiyya da cin dunduniyar juna da yiwa juna raddi, a wannan lokaci wadanda ba Musulmai ba suke kokarin sa matan Musulmai da yaran Musulmai suyi riddah
A kalla a sanina ya kai wata uku, ana gayyatar Matan Musulmai zuwa dakunan bautar masu bin addinin nasara da sunan za'a koya musu sana'o'i, bayan an koya musu sana'ar sai ayi musu tayin shiga addinin nasara
Daga nan sai s**a zarce zuwa duba lafiyarsu, ana musu gwajin lafiya a basu magani kyauta tare da musu wa'azi su bar addinin Musulunci zuwa addinin nasara
Daga nan sai s**a kara gaba zuwa cire musu Aljanu, ka ga katon arne ya rungume matar Musulmi wai yana cire mata aljanu tana ta burgima a jikinsa yana latse ta
Yanzu sun tsallaka zuwa bada tallafin abinci, kuma an fara yaudaran matan Musulmai akan su kawo 'ya'yansu musamman marayu wai za'a kai su inda za'a basu ilimin boko kyauta, kunga daga nan shikenan za'a tafi da yaro inda za'a canza masa addini, kuma matan Musulmai zalla ake yiwa haka
Sannan idan matan Musulmai sun je dakin masu bautar addinin nasaran, idan an gama abinda za'ayi da su, sai a jerasu a dauki hotonsu a tura cewa wadannan Matan Musulmai ne da s**ayi ridda, wato ta wani bangare neman kudi ake yi da matan Musulmai
Mun yi shiru ana neman cinye mu da yaki har cikin gidajen mu
Ina Malamai? kun tsaya yiwa juna raddi ga nan makiya Musulunci suna amfani da talaucin da aka jefamu a ciki domin su raba iyayen mu mata da addini, don haka kowa ya farka daga baccin da yakeyi, idan ba haka ba za'a cinyemu da yaki
Mazan aure ku sa ido sosai akan matan ku, idan sun tambayeku zuwa unguwa ku bi diddigi ku san inda suke zuwa, domin wata zata yiwa mijinta karya ne sai ta fita taje gurin
Muna rokon Allah Ya karemu daga sharrin makiya, Ya tsare mana imaninmu
copied
Datty Assalapy