Yusuf Muhammad

Yusuf Muhammad A

💔 "Ƙaramar ‘yar shekara 5 ta rasa rayuwarta… amma iyayen wanda ya jawo hakan na ƙoƙarin ɓoye gaskiya!" 💔  Wannan shi ne ...
11/08/2025

💔 "Ƙaramar ‘yar shekara 5 ta rasa rayuwarta… amma iyayen wanda ya jawo hakan na ƙoƙarin ɓoye gaskiya!" 💔
Wannan shi ne mahaifin yarinya ƙaramar ‘yar shekara 5 wadda ta rasa rayuwarta sak**akon mummunar hatsarin mota da wani matashi mai suna Amir ya jawo. Wannan matashi, wanda ke da gata da dukiya a gidansu, ya fito yana wasan mota, da sunan (kilisa) ya buge su da ƙarfin tsiya har ya tarwatsa rayuwar iyali gaba ɗaya.

Sak**akon wannan hatsari, yarinyar ta sha tsananin azaba kafin ta riga mu gidan gaskiya — wuyan ta ya karye, ta samu mummunar bugun kai har idanunta s**a fito kafin mutuwarta. Ƙanwarta ta samu karaya a hannu, mahaifiyarta mai juna biyu ta sami karaya a kafanta har yanzu ba a ɗaurata ba.kuma tana dab da haihuwa. Mahaifin kuwa, shi ma yana fama da raunuka masu tsanani.

Abin takaici, duk da irin wannan bala’i, iyayen wannan yaro mai suna Amir suna ƙoƙarin amfani da kuɗi da tasirin da suke da shi wajen ɓoye gaskiyar abin da ya faru, tare da nuna halin ko-in-kula ga waɗanda s**a jikkata da s**a rasa ‘yar su. Har yanzu, babu wani matakin da hukumomi s**a ɗauka, kuma babu wani goyon baya daga gwamnati ko masu fada-a-ji a jihar Bauchi.

Saboda haka, muna roƙon al’umma da su taya mu wajen yada wannan labari, domin ya isa ga kunnuwan masu tausayi da masu ikon taimakawa wajen ganin waɗanda aka zalunta sun samu haƙƙinsu.
Mun yi ƙoƙarin tuntuɓar manyan gidajen jaridu na Bauchi domin su ba mu dama mu bayyana halin da muke ciki, amma har yanzu ba su ba mu haɗin kai ba.

Muna roƙon duk mai tausayin ‘yan’uwa da ya taya mu da addu’a, da gudunmawa, da kuma yada wannan saƙo.
Zaku iya biPrince Adamsms a shafinsa na Facebook domin ganin bidiyon mahaifin yarinyar, mai suna Bashir Umar (me gyaran waya a kasuwar Wunti, Bauchi), wanda zai bayyana muku duk abin da ya faru nan bada jimawa ba, in sha Allah.

Allah Ya saka da alheri ga duk wanda ya taimaka, ya yi addu’a, ko ya yada wannan saƙo.
Rasuwar wannan yarinya ƙarama a duniya, amma babbar fitina ce ga iyayenta.

No matter what I stand by iran 💪 Allah ya wadaran naka ya lalace ,tarayyar labarawa duk yan gayyar sodi neh 😥
13/06/2025

No matter what I stand by iran 💪
Allah ya wadaran naka ya lalace ,tarayyar labarawa duk yan gayyar sodi neh 😥

Iran ta daga jar tuta
13/06/2025

Iran ta daga jar tuta

Allah Ya Kawo Miji Nagari 🙏
19/05/2025

Allah Ya Kawo Miji Nagari 🙏

LABARIN KALALA DA KALALATULittafi: Magana Jarice 2Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar ImamAkwai wani mutum wai shi Kalala...
19/05/2025

LABARIN KALALA DA KALALATU

Littafi: Magana Jarice 2
Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar Imam

Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da qi illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da suna ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan rika cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.

Da Kalala ya ga tsegumin yafa yi yawa sai ya bar kai abincinsa wurin mabwabcin. Ya riqa fita karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa suna ci tare.

To, Kalalatu ba ta kaunar wannan dabi’a ta mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin bakin da ya jawo ne su cinye. Ta yi, ta yi ta hana shi wannan dabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa ta ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinya rabi. Dalilai dai irin wadannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah ya zuba masa ba ya cewa kome.

Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda biyu ya sayo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya. Ta tashi, bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu ga dakwalen kaji, duk kitse yâ cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya k**a ta, da ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala. Ta sa dan yatsa ta dandana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai, wadannan kaji yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan, rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan nan ya miskile ni.”

Ta ci gaba da suya qanshi na jifarta, ta yi k**ar ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa mijin sun soyu.

Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo abokan ci.”

Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye ’yar cinyar da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon saura, sai mai ke zuba nash, nash. Ta ruga wajen kofar zaure ta leka ko ta hango mijin tafe da bakin, ba ta ga kowa ba, ta komo wajen kaji ta tura musu ido. Sai ta ce, “Af, ashe ma fikafikai guda biyu sun kone tun dazun, bari in cinye na dayar kuma don su zo daidai, kada mai gida ya gane.” Sai ta k**a fikafikai ta fiffizge ta lakwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba. Ta dawo, ta tsaya bisa kwanon da kaji su ke, ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta, ya tambaye ni, in ce me? Ba abin da yafi sai in cinye ta gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta.” Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta kwashi kasussuwa ta kai masai ta zuba.

Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba. Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare cinya guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo kome ta tafasa ta kone.” Sai ta k**a kazar guda kuma ta lakwume. Ta nufi randa ta debi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke zama ta zama.”

Ta zauna ke nan, sai ga mai gida ya shigo. Ya ce wa Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki barbada musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”

Kalalatu ta ce, “Ai ba kome, ku dakata mini dai kadan.’ Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can cikin daki, sai Kalala ya dauki wuka ya nufi manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, in an kawo.

Kalala na can na ta fama da washin wuya, sai Kalalatu ta ji ana sallama. Ta yi farat ta fita bakin zaüre wajen mai sallama, ta dube shi ta rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan ya kirawo, wai ku zo kucï abincï?”•

Bako yace, “I, Allah ya saka muku dâ alheri.”

Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai' ba ka san abin da a ke ciki ba. Kana tsammani mutum mai hankall ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana k**a gabanka ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum haka ya ke yi, motsattse ne.”

Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuka sai ya dafe qeya ya zura a guje. Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nân, ba ka san irin mutanen da ka ke jawowa gida ba.”

Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”

Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nân. Kajin da na barkadawa yaji, ko da ya gan su sai naga ya yi wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya mika, ya tasarwa kasuwa.”

Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska. Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya, don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka dauke.” Bako ya yi k**ar bai ji ba.

Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka. Duk wahalan nan da na sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka dauki alhakina.”

Sai dalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi bako yana kira, “Tsaya don Allah, daya kadai na ke so, na bar maka daya!”

Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa daya kadai ya ke so ya yanka. Ya waiwaya sai ya ga ya taso masa da wuka tsirara a hannu. Saboda haka ya kara mai, ya dai yi wa Kalala fintinkau yana ji yana gani.

Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, yana Allah ya isa. Da matar ta ganshi ya dawo yana zage-zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni.”

Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai dan banza da gudu! Ga shi k**ar tsoho, amma da ya zura sai ganinsa a ke k**ar ba ya taka qasa. Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau, ba na sake kiran dan kowa yaci abincina, tunda duniya ta sake. Mts, Allah wa- dai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi . ran biki kwa bata.”

Mutane da s**a ji wannan labari s**a fashe da dariya. Da s**a yi shiru Waziri ya soma:

13/05/2025

I got 50 reactions and comments on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

08/05/2025
🤣😂😂🤣
26/04/2025

🤣😂😂🤣

Address

Ran Road
Bauchi

Website

http://www.com.ng/, http://www.com.ng/

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yusuf Muhammad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share