28/10/2025
Yadda 'yanbindiga daga jahar Katsina ke tsallakawa suna kai hare-hare a jahar Kano
Mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano sun koka game da yadda 'yanbindiga ke kai musu hare-hare tare da sace mutane da dabbobinsu.
A ranar Alhamis ne wata ƙungiyar mazauna ta yi taron manema labarai domin shaida wa duniya yadda s**a ce 'yanbindigar na tsallakawa daga Katsina domin kai musu hare-hare.
Yayin taron manema labaran a ranar Alhamis, shugaban al'ummar Farin-Ruwa Alhaji Yahaya Bagobiri ya nemi gwamnatin taayya da ta jihar su kawo musu ɗauki.
"Muna neman Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf su kawo mana ɗauki saboda tuni wasu mazauna yankin s**a fara barin gidajensu zuwa birnin Kano da maƙwabtan garuruwa," in ji shi.
Bagobiri ya ce wasu hare-hare da 'yanfashin s**a kai musu ranar Talata da Laraba sun yi sanadiyyar raunata mutane da kuma sace shanu da dama.
Taskar Hausa News
Taskar Hausa Nws
Bauchi city
Arsenal