
10/12/2023
Rundunar Ζ΄an sandan jihar Bauchi ta cafke wani dan kasuwa kan yunkurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.
Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan matar tasa da nufin kashe.
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai matar Asibitin Kwararru da ke Bauchi domin kulawar da ita a sakamakon munanan raunukan da mijin ya yi mata da tabaryar.