07/06/2025
MUTANEN ZAMFARA DA SOKOTO GA AIKIN ALLAH: CALLING FOR JUSTICE!
Abin tausayi, wannan yarinya sunanta Bashariyya Abdullahi 'yar shekaru 14, ita da iyayenta ta'addancin barayin daji yasa sun gudu daga garinsu a jihar Zamfara zuwa sansanin 'yan gudun hijira dake Gwiwa Eka a jihar Sokoto
Akwai wata matar Babban Alkali a jihar Sokoto mai suna Fauziyya, sunan mijinta Barrister Abbakar Zaki Alkali ne a jihar Sokoto, Fauziyya ta je sansanin 'yan gudun hijira ta nemi a bata Bashariyyah domin ta dinga mata aikin gida a Abuja
Bayan ta tafi da ita Abuja ta dinga gana mata ukuba da azaba, shekaran jiya ta dawo da yarinyar gurin iyayenta a sansanin gudun hijira, sannan ta gargadi yarinyar akan kar ta kuskura ta bayyana irin azabar da ta gana mata
Mahaifin yarinyar shi ya bayyana abinda aka yiwa 'yar sa, duk da ita Fauziyya matar Alkali Abbakar Zaki tace ko sun bayyana babu abinda zai faru, domin wai sune da doka masu yin hukunci
Babu halin na saka bidiyo anan saboda Facebook zasu iya cirewa domin akwai cin zarafi sosai, zaku iya ganin bidiyon hira da akayi da yarinyar a Telegram channel ta nan
👇
https://t.me/DattiassalafiyTech
Muna kira ga mutanen Zamfara da Sokoto da duk wanda sakon nan ya riskeshi, don Allah a taimaka a yada ta sigar da ta dace domin ya kai ga masu iko da Gwamnatin jihar Zamfara da Sokoto, saboda a tabbatar wa Fauziyya matar Alkali cewa babu wanda ya fi karfin doka
Akwai wasu irin mutane da basu goge a sanin jarrabawan rayuwa ba, idan sun samu dama sai su wulakanta kowa su ci zarafin wanda s**a ga dama, basu sani ba cewa idan rayuwa ta juya zasu iya shiga cikin kaskanci na rayuwa su zama abin tausayi
Muna rokon Allah Ya isar wa Bashariyyah akan ta'addancin da Fauziyya matar Alkali Abbakar Zaki ta aikata mata