20/03/2025
*SHARHIN DU'A'U ABI HAMZATAS SUMALIY*
Tareda Sayyid Abdullahi Ashura
Zama na daya (No. 1)
*GABATARWA:*
Bismillahir Rahmanir Raheem, mun dauki sharhin da Ayatullah Sayyid Muhsin Hussain Daharani ya yi, za mu yi karatu cikinsa, saboda ya qunshi abubuwa muhimmai,
marawaicin wannan addu'a shi ne Abi Hamzata.
*WANENE ABU HAMZATA?*
Sunansa Sabit Ibn Dinar, ya rayu da A'imma (AS) Imam Sajjad (AS), Imam Baqir (AS), Imam Sadiq (AS), a wasu riwayoyin ma har da Imam Kazim (AS), saboda haka ya rayu da A'imma (AS) kuma shi siqah din su ne daga cikin manyan marawaita, wanda A'imma (AS) suke da aminci da shi, mutum ne wanda ya kai qololuwa na daraja wajen kusanci da Allah ta yadda hatta Imam Sadiq (AS) yana fada dangane da Abu Hamzata cewa: "Abu Hamzata a zamaninsa k**ar Salmanul Farisi ne a zamaninsa." Mutum zai ga ne girman maganar ne idan yasan wanene Salmanul Farisi a zamaninsa, wurin kusanci da Allah, da abin da ya ba shi matsayi a wurin Amirul muminin (AS) da Sayyida Zahra (AS), wannan tundaga Mamzon Allah (S).
A wani riwaya Imam Ridha (AS) yana cewa: "Abu Hamzata a zamaninsa k**ar Lukmanul Hakim ne a zamaninsa."
Imam Sajjad (AS) ya kasance yana karanta wannan addu'a a dararen ramadan a lokacin sahur, (amma ana iya karantawa ko da ba lokacin).
*TARJAMA:*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*Da sunan Allah mai rahama mai jinqai*
*إلهي لاتؤدبني بعقوبتك*
*Ya Ubangijina kada ka ladabtar dani da azabarka*
*ولاتمكربي في حلتك*
*Kada kamin talala a cikin hilarka*
*من أين لي الخير يارب ولايوجد إلا من عندك؟*
*A ina zan samu alheri ya ubangiji, bayan kuma babu wurin da ake samunsa sai a wurinka?*
*ومن أين لي النجاة ولا استطاع إلا بك؟*
*A ina zan samu tsira (bayan) kuma babu wurin da ake samunta sai da kai?*
*لا الذي أحسن استغنى عن عونك ورحمتك*
*Wanda ya kyautata aiki ya zama nagartacce ko shi bai wadata ba daga barin neman taimakonka da rahamarka*
*ولاالذي أساء واجرأ عليك, ولم يرضك خرخ عن قدرتك.*
*Kuma ko wanda ya saba maka ya yi maka jur'a (tsaurin ido) bai fita daga cikin ikon ka ba, (bai fi qarfinka ba).*
*SHARHI:*
Kalmar *'Ilahiy'* wanda aka fara addu'ar da ita tana da banbanci da 'Allahumma' da 'Ya Allahu' domin 'Ilahiy' ta fi 'Ya Allahu da 'Allahumma' taushi, ta fiskacin nuna damfaruwar bawa da Ubangiji, ba kawai ya kira Ubangiji ba ne a'a, ya damfara kansa da shi, wato yana cewa "Ubangijina" ba cewa ya yi Ubangiji ba a'a, cewa ya yi Ubangijina, ko kuma Abin bautana, akwai tausasawa sosai a ciki.
Shi yasa za mu ga a cikin Du'a'u Kumail Amirul muminin (AS) ya yawaita fadin 'Ilahiy wa Maulay wa Sayyadi'.
Ko mutum za ka kira akwai banbanci tsakanin ka ce masa wane da kuma ka ce masa wanena, akwai shu'uri na cewa wanda ka kira naka ne, shi yasa ya fara wannan addu'a da Ilahiy.
*'La tuaddabniy bi uqubatika'* Kada ka ladaftar dani da uqubarka, ma'ana ya Ubangijina kada ka min tarbiya (horo) ta hanyar azaba, kada ka sanya azaba ya zama shi ne salon da za ka yi amfani da shi wajen tafiyantar dani.
(Kamar yadda mu ka sani Allah Ta'ala yana da hanyar ladaftarwa na azaba da hanyar da ba azaba ba, idan mutum ya saurari wa'azi ya ji nasiha ya gyaru ya ladaftu, to wannan hanya ne na ladaftarwa, akwai kuma hanya wanda mutum zai hawala ya gamu da musibobi da bala'o'i, sai hakan ya sanya shi ya ladaftu, ita ma wannan wata hanyar ce).
To shi Imam (AS) a nan yana roqon a ladaftar da shi ne amma ba da azaba ba.
*'Wala Tamkurbiy fiy hilatika'*
Ma'ana kada kamin talala saboda abinda yake wajenka na gwaninta da kuma zurfafa biyayya gareni.
Abinda za mu iya fahimta daga nan shi ne, Allah Ta'ala yana iya ladaftar da mutum da azaba, kuma zai iya yi wa mutum talala domin ya k**ashi cikin talala da ya yi masa, akwai buqatar mu fahimci menene ake nufi da talalan, mu kuma ga menene uquba na Allah Ta'ala da yake ladaftar da dan adam da ita.
Idan mu ka lura bai ce kada ka ladaftar dani ba kawai, cewa ya yi, kada ka ladaftar dani ne ta hanyar azabanka, a nan sai ya bayyana mana Allah Ta'ala yana da salo guda biyu na ladaftarwa, daya daga cikinsu shi ne ladaftarwa ta hanyar uquba, dayan kuma ba da uquba ba, shi yasa Imam (AS) yake roqon Allah Ta'ala ya ladaftar da shi amma ba da uquba ba, (idan muka lura ladaftarwan Allah Ta'ala yana tarbiyantarwa ne ga mutum, k**ar yadda yazo a hadisi cewa "Ubangijina ya tarbiyantar dani kuma ya kyautata ladaftarwan).
Sayyid Muhsin ya ce: "Wannan jumla tana da ban mamaki, kuma tana nuni zuwa ga wani abu mai girma, kenan tana iya yuwa Allah ya yi wa mutum ladabi ta hanyar uquba?. Abinda ake fahimta da ladaftawa shi ne, daidaita mutum a dawo da shi kan hanya madaidaiciya, da fadaka da farkawa, sabanin wadanda ba su samu tarbiya ba, lallai kowani muhalli yana da irin ladabinsa da ake buqata.
Wadannan da ba su sami tarbiya ba, ba zai zama suna kan hanya madaidaiciya ba sai ka ga sun wuce iyaka, ko sun gaza, ko sun yi gaggawan wani abu ko sun yi jinkirin yi, ko ya zama ba sa kiyaye ladabin wurin da s**a sami kansu a ciki, ko su kasance gafalallu dangane da al'amarin Allah Ta'ala, suna masu jahiltarsa su wadannan marasa tarbiya ba su da iddila'i akan sharidodin bauta da kuma hakkin ubangijiyanka na Allah Ta'ala.
Amma bawa mai ladabi shi ne wanda yasan wadannan abubuwa ya fahimce su, kuma ba zai buya ba dole ne bawa ya zama ya siffantu da ladabi datarbiya a hanyar bautar Allah, domin ba a ba da dama ga mara ladabi ya shiga cikin haramin Allah Ta'ala.
Idan Allah Ta'ala ya dubi bayinsa da rahama sai ya ladaftar da wadanda yake son su domin su sami damar shiga cikin haraminsa, domin wanda bai da ladabi ba ya shiga cikin haramin, (ka ga kenan bawa yana buqatar wannan ladabi daga Allah), sai ya bude musu qofa domin shiga wata duniyar da albarkar sunansa Rahamaniyyah.
Bayan wadannan ba yi sun zama masu tarbiya to zai zama akwai alaqa da ubangijisu a bisa asasi na ubudiyya sai ka ga bawa ya wayi gari ya yi nutso a cikin cancanta na tsayuwa a hanyar Allah da munajatinsa, sai ya samu dama wajen samun matsayi a haramin Allah Ta'ala.
Samun wannan matsayi baiyuwa, rabo ne kawai na bawan da ya lataftu, amma wadanda ba su samu wannan ladaftarwan ba su suna nesa ne da rahamar Allah. Ba sa cikin abinda za mu tattauna a karatun mu.
Ka ga kenan daga nan za mu fahimci cewa wannan ladaftarwan muhimmin al'amari ne ta yadda za mu ga Imam Sajjad (AS) yana cewa "Ya Allah kayimin ladabi, amma kada ka ladaftar dani da azabarka."
Kenan wajibi ne a samu wannan ladaftarwa, rashin ladaftarwan mummunae abu ne, shi yafi komai muni ga mutumin da yake suluki yake so ya isa zuwa ga Allah, domin idan bawa ya fita daga hanyar ladaftarwa ba zai kai zuwa ga haske da kishi na Allah ba, sai bawa ya fado daga dukkan muqamominsa, saboda haka wannan ladaftarwayana nufin tsayuwa daidai a matsayi ta yadda mutum ba zai yawaita magana ba, ba kuma zai qaranta magana ba, zai yi shi daidai ne, kuma ba zai taba siffanta ubangijinsa da wata siffa wanda ubangijin baya so ba, amma zai siffanta Allah Ta'ala ne da abinda yake daidai babu ragi babu qari.
Saboda haka a ladabi mutum ba zai ce 'Ilahiy Nafsi lakal fidha' ba, domin idan ya ce haka to Allah zai iya ce masa to zo ka sadaukar da kanka din a matsahin fansa gareni, saboda haka shi bawa mai ladabi yasan matsayinsa kuma zai tsaya ne akan matsayinsa wanda ya tabbata shi ne iyakarsa.
Akwai Sayyid Jamaluddin Golfagani (RH) yana daga cikin malaman Najaf kuma Marji'i ne, masani kuma ya sifffantu da tarbiya, kuma salihi ne. Ayatullah Sayyid Muhsin ya ce nakasance ina zuwa wurinsa
Watarana Sayyid Jamaluddin Golfagani yana fada wa Sayyid Muhsin cewa: "Wani lokaci nakan je na k**a jikin raga raga na kabarin Amirul muminin (AS) sai in girgiza da hannuna sannan na ce "Ya Imam! ka saukarmi da kowani irin bala'i, ka kawomin duk wani musiba da ka ga dama, amma ni dai ka biyamin buqatana kaza, na kan tafi a lokacin hunturu cikin tsananin sanyi, kafin kiran sallah da awa daya ko biyu, na tsaya a qofar wurin na jingina jikina da wannan qofa har sai an bude qofar sai na zama nine na farko da zan shiga, sai naje ina kuka ina cewa, a jarabceni da kowani irin talauci da kowani irin tsanani da kome ka ga dama, amma ni dai ka bani abinda nake nema"
Wannan magana da Sayyid Golfagani yake roqa dagaske yake fada ba qarya yake yi ba ko kuma yana fada ne saboda halin da ya sami kansa a ciki, misali yana cewa Ka yi min komai k**ar dutse ta fadomin a kai, ko a daddatsani gunduwa gunduwa, ko kuma talauci ya lullubeni, ko na rasa duk iyalina, ko kuma ka kawomin kowani irin bala'i da ya sauka akan Annabi Ayuba (AS), da duk wani bala'i da ya sauka akan Annabi Yaqub (AS) ko wasu Annabawa, amma ni dai ka bani buqatana.
sai kuwa alamomin wadannan abubuwa s**a fara zuwa sannu dannu, taqaitacciyar muqaddima sai ta zo ta fiskacin talauci, aka jarabce mu da qarancin kudi, babu abinda muke samu na kudi duk abinda muka taba baya yuwa.
Lokacin da muke a Najaf wurin neman ilimi ba abinda yake zuwa mana na tsawon watanni ba abinda muke samu, mu kanje mu ci bashi ne har sai da masu abinci s**a daina ba mu bashi, har muma kanmu mu ka ji kunyar zuwa mu ci bashi, ga kudin gidan haya na watanni ba mu biya ba, sai ga mai gida yazo ya yi fatali da kayan mu a waje, mu ka dibi kayanmu muka tafi wani daki a masallacin kufa muka sanya kayanmu mu ka mai da shi dakin mu, muna rayuwa ni da iyali a wajen, kuma wurin yana da nisa da makaranta, sai ya zamo ina zuwa Najaf da asuba na yi karatu, sannan na komo masallaci kufa cikin wannan tsanani na nisa.
(Shi Sayyid Golfagani mutum. ne lafiyayye).
Ya ce "A wannan hali sai matana ta fara raki tana cewa, wannan wani irin rayuwa ne, wannan wani irin musulunci ne wani irin addini ne ka ke yi? wannan wani irin mazhaba ne?, shin Allah ne ya umurceka da wannan quntatawa da ka shiga, ka tashi ka je ka nemi abin yi.
Sai ya ce mata "Ki tashi muje hadaran Amirul muminin (AS) ki fada masa duk wannan damuwar naki, a lokacin ana tsananin zafi, sai mu ka fita daga masallacin kufa zuwa Najaf, sai na nemi wani waje a gefe na zauna, ita kuma sai ta shiga haramin domin ta koka lamarinta ga Amirul muminin (AS), lokacin da ta dawo wurin ajiye takalma sai ta samu an sace takalminta (ya bata), tana tafiya qafarta babu takalmi, sai ta ce "A wajen Amirul muminin din ma ga abinda ya faru dani" a taqaice dai kawai hanyoyin mu sun gama toshewa, to yanzu ya za mu yi?, talauci ya yi mana yawa ya mamaye mu har zuwa wani matakin da ina zuwa (ina komawa) jikin raga raga na kabarin na girgiza na ce ya Amirul muminin na yi kuskure cikin abin da na roqa yanzu na janye maganata, ban mallaki kowani irin iko ba, ba za mu iya tabuka komai ba lallai na yi kuskure"
Sayyid Muhsin ya ce: "Lokaci da mutum yazo ya ce lallai na yi kuskure ya Allah, to a nan ne za a ce masa ya yi kyau tunda ka yi i'itirafi da kuskurenka.
Tattare da cewa wannan ba wani abin damuwa ba ne, kawai an dan toshe musu arziki ne.
To a nan abinda za mu fahimta shi Allah yakan bayyanar ne ga mutum cewa shin abinda ka fada dagaske ne kana so a saukar maka da bala'in?, za ka ga muna karantawa a cikin du'a'ul Kumail cewa: "Ya Ubangiji a qaddara na jure azabanka to ya zan yi na jure zafin rabuwa da kai, ya Ubangiji a qaddara na jure zafin wutarka to ya zan jure zafin rashin kallon karamcinka, Ya ubangiji qaddara yayin da ka saukarmin da azabarka ka jefani cikin jahannama ni zan yi haquri amma ya zan iya suranta kaina alhali na nesanta da kai, qaddara ka jefani a wuta ka jarabceni da azabobinka da zafin wutarka, to amma ya zan iya haquri da rashin kallo da za ka yi min na jinqai"
Shin dagaskw ne wannan abinda muke fada cikin wannan addu'a?
Imam Ali yana yin wannan addu'a muma sai ka ga mun zo muna yi muna cewa: "Ya Allah Aljannah na yara ne, mu munfi qarfin mu roqeka aljannah ko Hurul iyn, ko wasu bishiyoyi, mu abinda ya dace mu roqeka shi ne k**ala.
Haka abin yake dangane da tsoron wuta, muna cewa "Wannan na wadanda ba su samu wusuli ba ne, amma mu zababbu mun wuce wadannan matakai, mu yanzu Husuli zuwa ga Allah mu ke nema, amma dangane da azaban jahannama bai damemu ba"
To ba kunga abinda Imam Ali (AS) yake fada a cikin Du'a'u Kumail ba, to amma sai ka ga mun bude shafi daya biyu uku mun rufe mu ce mun karanta Du'a'u Kumail (cikin qanqanin lokaci), mun dauka abin ya qare a kalmomi ne na magana kawai, to Allah Ta'ala zai ce 'Tafaddhal' yanzu za a yi maka tambaya akan abinda ka roqa, wadannan da rusa da ka roqa yanzu za mu yi maka jarabawa, mu ga zuwa wani mataki ka ke.
*Zamu ci gaba*
✍️Huzaifa Bauchi