Al-QARYA TV

Al-QARYA TV General Media Services

17/09/2025

Yanzu-Yanzu

Ta Tabbata, Gobe Halaltaccen Gwabnan Rivers Gobe zai koma bakin Aiki, Bayan Dakatar da shi da Tinubu ya yi na wata 6.

16/09/2025

Follow
Al-QARYA TV

YANZU-YANZU: Babban Malamin Addinin Musulinci A Nijeriya, Sheikh Modibbo Dahiru Ganye, Ya Rasu.Sheikh Moddibo, Wanda Ya ...
16/09/2025

YANZU-YANZU: Babban Malamin Addinin Musulinci A Nijeriya, Sheikh Modibbo Dahiru Ganye, Ya Rasu.

Sheikh Moddibo, Wanda Ya Shafe Shekaru Yana Hidimtama Addinin Islam, Malamin Ya Rasu Ne A Yau Talata A Garin Ganye Ta Jihar Adamawa.

HOTUNA:Mai Martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya nuna inda za a binne shi a maƙabartar Sarakuna da ke Daura . Sarkin...
14/09/2025

HOTUNA:
Mai Martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya nuna inda za a binne shi a maƙabartar Sarakuna da ke Daura .

Sarkin ya faɗi hakan ne a lokacin da tsohon Gwamnan Jigawa, Dr. Sule Lamido da Janar Aliyu Gusau Mai Ritaya da Alhaji Dahiru Barau Mangal, s**a ziyarce shi a fadarsa.

Al-QARYA TV

Yansandan Katsina Sun Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Mallakar Makami da Yin Sojan GonaRundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina...
14/09/2025

Yansandan Katsina Sun Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Mallakar Makami da Yin Sojan Gona

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta cafke wani mutum mai suna Mubarak Bello, mai shekaru 38 daga karamar hukumar Kurfi, bisa zargin mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba tare da yin sojan gona a matsayin ɗan sanda.

A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na safiyar Asabar, lokacin da jami’an rundunar ke sintiri a ƙarƙashin sashen ayyuka.

Sanarwar ta ce jami’an sun tsayar da wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka, wadda ke ɗauke da lambar rajista Lagos GGE 473 BH, wadda Mubarak Bello ke tukawa. Bayan gudanar da tambayoyi, wanda ake zargin bai bayar da amsa mai gamsarwa ba, abin da ya tilasta jami’an gudanar da bincike a cikin motar.

A yayin binciken, rundunar ta gano Bindiga ɗaya da aka ƙera a gida, Alburusai huɗu masu rai, Kwarkwaron harsashi guda biyu, Katin shaida na ’yan sanda na bogi, Ƙarin lambar rajista (Kano FGE 68).

Rundunar ta ce a halin yanzu ana ci gaba da tsare Mubarak Bello don gudanar da ƙarin bincike kan asalinsa, dalilin mallakar makamin, da kuma amfani da katin bogin.

DSP Aliyu ya ƙara da cewa wannan nasara ta nuna ƙoƙarin rundunar a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Bello Shehu, na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar Katsina.

HOTUNAGwamna Bala Mohammed ya zaga sabon Babban Ɗakin taro na ƙasa da ƙasa ICC dake nan Bauchi wanda ake daf da kammalaw...
13/09/2025

HOTUNA

Gwamna Bala Mohammed ya zaga sabon Babban Ɗakin taro na ƙasa da ƙasa ICC dake nan Bauchi wanda ake daf da kammalawa.

Aikin na daga cikin manyan ayyukan da Gwamnatin sa ta samar a wani mataki na sabunta Jihar Bauchi.

A watan Oktoba ne ake sa ran buɗe Dakin taron yayin babban taron Zuba jari wato Investment Summit da za'a gudanar.

Suleiman Musa Kwankiyel
Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna Bala Mohammed Ɓangaren Sadarwa.
13-09-2025

Ɗalibar Data Yi Nasara A Gasar Turanci Na Duniya Nafisa Abdullahi, Ta Ziyarci Professor Isa Ali Pantami Daga Muhammad Kw...
13/09/2025

Ɗalibar Data Yi Nasara A Gasar Turanci Na Duniya Nafisa Abdullahi, Ta Ziyarci Professor Isa Ali Pantami

Daga Muhammad Kwairi Waziri

A ranar Juma’a, daliba mai shekaru 17 daga jihar Yobe, Nafisa Abdullah Aminu, ta kai ziyarar godiya ga Farfesa Isa Ali Pantami a kan goyon baya da jagoranci da ya ba ta.

Nafisa ta mika masa lambar yabo da ta samu a gasar TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a London, inda ta zama ta daya a duniya a fannin harshe, ta doke sama da dalibai 20,000 daga kasashe 69.

Dalibar, wadda ke karatu a Nigerian Tulip International College (NTIC), ta yaba wa Farfesa Pantami tare da rokon ci gaba da shiriya daga gare shi a fannin addini da kuma karatu.

Farfesa Pantami ya nuna farin cikinsa, inda ya gode wa iyayenta, malamanta da masu kula da ita, sannan ya bai wa Nafisa sabuwar kwamfuta mai ƙarfi (HP laptop), tare da wasu muhimman littattafai da shawarwari masu amfani ga rayuwa.

Iyalin Farfesa Pantami sun karfafa mata gwiwa da ta ci gaba da karatunta har ta kai matakin digiri na farko, na biyu da na uku (PhD), inda s**a ce al’umma na matukar bukatar ci gaban ilimin mata a wannan lokaci.

Farfesa Pantami ya amince da ci gaba da kula da Nafisa a matsayin wata mai hazaka da ke da makoma mai haske.

13/09/2025

Martanin Muddasir Abba Kan Maganganun Husaini Galawa

Masu aikata laifi a Nijeriya sun yi mana fintinkau – Kayode Egbetokun ....By Our Reporter.Babban sufeton ‘yan sandan Nij...
12/09/2025

Masu aikata laifi a Nijeriya sun yi mana fintinkau – Kayode Egbetokun ....

By Our Reporter.

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke addabar ƙasar sun fi jami’an tsaro shiri ta fuskar kayan aiki, kuɗi da kuma dabaru.

Egbetokun ya bayyana haka ne a babban ofishin ‘yan sanda na ƙasa da ke Abuja, lokacin da ya gana da kwamandojin sashen kula da iyakokin ƙasar, yace ‘yan ta’addan da ake fuskanta a yau ba irin ƙananan kungiyoyin da ake gani a baya ba ne.

A cewarsa, suna da kuɗi, suna da makamai masu ƙarfi, kuma suna amfani da sabbin fasahohi, takardun bogi da hanyoyin sadarwa na zamani a boye.

Sufeton ya jaddada cewa jami’an tsaro ba za su iya yaƙar irin wadannan mutanen da tsoffin kayan aiki ba.

Ya jaddada cewa jami’an tsaro na buƙatar kayan aiki na zamani domin su iya tunkarar waɗannan ƙungiyoyi masu tsari da haɗin gwiwa daga wasu ƙasashen ketare.

Tsohon ɗan Majalisar Dokoki ta jihar Kano, Ayiye ya rasu Tsohon Ɗan Majalisar Dokokin jihar Kano, mai wakiltar mazaɓar ƙ...
11/09/2025

Tsohon ɗan Majalisar Dokoki ta jihar Kano, Ayiye ya rasu

Tsohon Ɗan Majalisar Dokokin jihar Kano, mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Fagge, Muhammad Idris Ayiye ya rasu.

Iyalin Ayiye, wanda tsohon shugaban kwamitin kasafin kuɗi ne na Majalisar Dokokin Kano, su ka sanar da rasuwar ta sa a jiya Laraba da daddare.

Za a yi jana'izar sa a safiyar yau Alhamis a gidan su da ke Dogon Layi, Fagge A.

Allah Ya yi masa rahma, Ya kyauta namu zuwan.

Gwamna Bala Mohammed ya amince da Gyara da Ɗaga Darajan Kwalejin Kimiyyar Lafiya Dake Ningi, da wasu Cibiyoyin kiwon Laf...
11/09/2025

Gwamna Bala Mohammed ya amince da Gyara da Ɗaga Darajan Kwalejin Kimiyyar Lafiya Dake Ningi, da wasu Cibiyoyin kiwon Lafiya a Jihar Bauchi

A wani yunkuri na ɗaga darajar kiwon lafiya da Magance matsalolin dake fannin ke fuskanta a jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya gana da Kwamishinan Lafiya da sauran Shugabannin Hukumomin lafiya dake ƙarƙashin Ma'aikatar.

Bayan Ganawar, Kwamishinan Lafiya Dr. Sani Dambam ya zayyana wasu daga cikin ababe da Ganawar ta mai da hankali.

Acewar sa Gwamnan ya rashin jin daɗin sa bisa halin da wasu Asibitoci ke ciki a jihar Bauchi har ma ya amince da matakin gyara su nan take.

A ɓangaren ƙarancin ma'aikatan lafiya, Gwamnan ya amince da cigaba da yunkurin ɗaukar Sabbin Likitoci harma ya amince da sabon tsarin albashi mai tsoka don a janyo hankalin kwararru zuwa jihar Bauchi.

Haka zalika, Gwamna Bala Mohammed ya bada umurnin soma shirin Gyara da Ɗaga Darajan Kwalejin Kimiyyar Lafiya dake Ningi bisa manufar samar da ƙarin kwararru a fannin lafiya a jihar Bauchi.

Yanzu haka ana cigaba da gyara a kwalejin Koyon aikin Jinya da Ungozoma ta Aliko Ɗangote dake nan Bauchi inda ake samar da Ɗakin kwanan Ɗalibai da sauran muhimman ababe da ake bukata.

Gwamna Bala Mohammed yayin Ganawar, ya jaddada Himmatuwar Gwamnatin sa wajan magance matsalolin Da sashin ke fuskanta ta hanyar cigaba da zuba jari don inganta lafiyar al'ummar jihar Bauchi.

Suleiman Musa Kwankiyel
Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna Bala Mohammed Ɓangaren Sadarwa
10-09-2025

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya Malamin mu Dr. Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa murnar bashi Digirin Girmamawa da Jami...
10/09/2025

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya Malamin mu Dr. Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa murnar bashi Digirin Girmamawa da Jami'an Sokoto ta bashi.

Address

New GRA Bauchi
Bauchi
1234

Telephone

+2349052103812

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-QARYA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share