
05/06/2025
HON ALIYU AMINU GARU DAN MAJALISAR TARAIYYA A HUKUMAR BAUCHI. YA BADA
MILIYAN 25,000,000
Dan Majalisa Mai tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Bauchi Hon. Aliyu Aminu Garu, Ya Raba Shanu, Raguna da kudi za'a kashe Sama da Naira Miliyan 25 don Bukukuwan Sallah
Hon. Aliyu Aminu Garu, dan majalisar wakilai mai wakiltar Mazabar Bauchi a Majalisar Tarayya, ya raba shanu, raguna da tallafin kudi da ya kai kimanin Naira miliyan 25 ga al’ummar mazabarsa domin saukaka musu gudanar da bukukuwan Babbar Sallah (Eid-el-Kabir).
A yayin rabon kayan, Hon. Garu, ta bakin Daraktan Kudinsa, Ibrahim Baba Tela, ya bayyana cewa wannan taimako na musamman an shirya shi ne domin tallafawa talakawa da marasa galihu wajen gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauƙi da walwala.
Ibrahim Baba Tela ya kara da cewa wannan tallafi ya nuna yadda Hon. Aliyu Aminu Garu ke ci gaba da nuna kulawa da jin ƙai ga jama’arsa, musamman a lokutan bukukuwa da manyan al’amuran addini da zamantakewa.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da nuna haɗin kai, soyayya da yin addu’o’i don zaman lafiya da ci gaban Jihar Bauchi da Najeriya Dama Jam-iyyarmu ta PDP ɗaya.
Wadanda s**a ci gajiyar wannan tallafi sun haɗa da:
Shugabannin jam’iyyar PDP daga matakin jiha har zuwa mazabu
Shugabannin al’umma
Yan Media
Kungiyoyin matasa da na mata
Cibiyoyin addini
Gidajen marasa ƙarfi da mabukata
Hon. Aliyu Aminu Garu ya jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafawa al’umma da aiwatar da ayyukan ci gaba a mazabarsa.