
29/07/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Maganganun Omoyele Sowore Ba Abin Mamaki Ba Ne Domin Kwankwaso Ya Bi Ta Kan Kuɗaɗen Mutane A Jihar Kano, Cewar Basiru Shuwaki
Tun da farko, Basiru Yusuf Shuwaki ya fara ne da cewa "Ni ina ƙalubalantar Mudugu kan abubuwan da Sawore ya fito ya faɗa a satin nan. Duk mutumin da yake Jihar Kano kuma ya san kansa, ya san irin badaƙakar da aka yi a gwamnatin Rabi'u Musa Kwankwaso. Za a zo a yi abu da sunan aiki amma aikin ba za a yi shi ba. Ko kuma a fara aikin a watsar a kwashe kuɗaɗen". Inji shi.
Basiru wanda ya bayyana haka ta cikin tattaunawarsa da Dokin Ƙarfe TV, ya ba da misali da cewa, "Lokacin da Kwankwaso ya fara aikin gina gadoji, duk gadar da ya fara ba ya iya kammala ta sai gwamnatin Ganduje da ta gaje shi ce ta ƙarasa. Shi da ya gaji Shekaru bai ƙarasa ayyukan da ya tarar an fara ba saboda ba zai samu ko sisi ba". A cewarsa.
"Idan ka ga kuɗaɗen da ake cewa za a sayo magani kwanaki a ƙananan hukumomi, in ka ga kuɗaɗen sun fita hankali. An zo an ƙirƙiri wani abu cewa za a yi tituna na kilo mita biya-biyar a kowace ƙaramar hukuma, har Kwankwaso ya tafi babu ƙaramar hukuma ɗaya a wajen birnin Kano da aka yi wa titin. An fidda kuɗaɗen kuma ba a yi ayyukan ba". In ji shi.
Shuwaki, ya kuma ƙara da cewa, "Ba abin mamaki ba ne dan Sawore ya fito ya ce Kwankwaso ya mallaki manyan gidaje da otel-otel a Abuja da ma wasu ƙasashen ba saboda ya bi ta kan kuɗaɗen mutane. Mu da muke Jihar Kano mun san irin wannan abubuwan za su iya faruwa. Ko yanzu a wannan gwamnati da yake juyawa an zo an yi rabon tallafin Akuyoyi, kowace akuya ɗaya ta tashi ne a ƙalla kan Naira 300,000, kusan kuɗin sa, akuya in dai ba daga Makkah za a kawo ta ba ta ya za ta kai wannan kuɗin". A cewarsa.