Sarkinmota online Tv

Sarkinmota online Tv An Islamic centre for propagation and peace for the promotion of the nation and society

AN TSIRA DA RAI: JIRGIN SAMA NA SOJIN NAJERIYA YA YI SAUKAR GAGGAWA A MAKURDIAn sake kauce wa wata babbar musiba a yau, ...
07/10/2026

AN TSIRA DA RAI: JIRGIN SAMA NA SOJIN NAJERIYA YA YI SAUKAR GAGGAWA A MAKURDI
An sake kauce wa wata babbar musiba a yau, 7 ga Oktoba, 2026, bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (Nigerian Air Force) ya yi saukar gaggawa a wata gonar da ke yankin Utur Tse-Igboji, Bar Council Ward, Makurdi, a hanyar Welfare Quarters zuwa Mopol 13 Ring Road.
Rahotanni sun ce jirgin ya yi saukar gaggawar ne sakamakon lalacewar fasaha (technical fault).
Da lamarin ya faru, mazauna yankin sun garzaya wurin domin taimaka wa jami’an da ke cikin jirgin.
Alhamdulillah, dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun tsira da ransu, kuma ba a samu asarar rai ba.
Da ace jirgin ya yi hatsari, da hakan zai iya zama babbar musiba. Muna godiya ga Allah da Ya kare rayukan jami’an.
Allah Ya ci gaba da kare jami’an tsaron Najeriya tare da dawo da su gidajensu lafiya.

Allah ya kiyaye na gaba

📍 Rahoto daga wurin da lamarin ya faru:
Stephen Ikpam
Utur, Tse-Igboji, Makurdi.

Alhamdullahi ●Muna farin ciki sakin mambobin NYSC ☆Cewar kungiyar matasa musulmai masu hidima wa kasa ● Ana kira ga jago...
07/10/2026

Alhamdullahi

●Muna farin ciki sakin mambobin NYSC
☆Cewar kungiyar matasa musulmai masu hidima wa kasa

● Ana kira ga jagorori da masu fada aji na kasa da su dauki kwakkwaran mataki wajen kare Matasa masu hidima wa kasa duba da yanayi tsaro

Duba sashin sharhi don ganin sakon MCAN

Tsohon gwamnan jihar cross river Donald Duke dan takarar Shugaban kasa a jami'an PRP yayi Alkawarin mai farashin mai zuw...
07/10/2026

Tsohon gwamnan jihar cross river Donald Duke dan takarar Shugaban kasa a jami'an PRP yayi Alkawarin mai farashin mai zuwa naira Dari uku ₦300 idan aka zabeshi a matsayin Shugaban kasar Nigeria a 2027

Ko me Donald Duke ya taka a cikin Wannan furuci nasa ku bayyana mana a sahin sharhi

Muslim Muslim Ticket Nigeria Kowa Na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu NeAn Hango Alh. Ibrahim Kabir Masari ya karɓi ƙungiyar Jo...
07/10/2026

Muslim Muslim Ticket Nigeria Kowa Na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Ne

An Hango Alh. Ibrahim Kabir Masari ya karɓi ƙungiyar Joint Islamic First Aid Group Organization Na Reshen Abuja. Ƙungiyar ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen Bola Ahmed Tinubu a 2027, tare da son a ci gaba da tikitin Musulmi da Musulmi.

Masari ya ƙarfafa su su ci gaba da wannan matsaya, tare da yin siyasa cikin haɗin kai, zaman lafiya da gaskiya.

07/10/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Sani Idris Sk, Umar H Ali

HOTUNA DAGA WAJEN TAFSIRIN ALQUR'ANI MAI GIRMA 25/04/1448hjr 06/10/2026Alhamdulillahi ●  Imam Dr. Mahmud Isah Duguri  ta...
06/10/2026

HOTUNA DAGA WAJEN TAFSIRIN ALQUR'ANI MAI GIRMA
25/04/1448hjr
06/10/2026

Alhamdulillahi

● Imam Dr. Mahmud Isah Duguri tare da
Hafiz Yusufu Shayubu Sambo

S**a gabatarda tafsirin alqur'ani da fassara daga nan Babban Masallacin Jummah na jibwis dake kasuwan shanu nan cikin garin Bauchi

06/10/2026
MASU KARE DCP ABBA KYARI SUN GABATAR HUJJOJIN DA YAKAMATA A SAKE Duba comment zaka ji abin ya faru
06/10/2026

MASU KARE DCP ABBA KYARI SUN GABATAR HUJJOJIN DA YAKAMATA A SAKE

Duba comment zaka ji abin ya faru

JIYA KENAN Daga Cibiyar Dakin Taro na  Ƙasa da kasa na Sir Ahmadu Bello dake nan Jihar BauchiMuhimimmin taron taya murna...
06/10/2026

JIYA KENAN

Daga Cibiyar Dakin Taro na Ƙasa da kasa na Sir Ahmadu Bello dake nan Jihar Bauchi

Muhimimmin taron taya murna da cika shekaru 68 na maigirma gwamnan jihar Bauchi Muhammed Bala Abdulkadir kauran Bauchi shekaru 68.

Tare da tattauna Muhimman lammura da s**a shafi jihar Bauchi da makomar kasar mu Nigeria.

Address

Hayin Gada Opp Armour Barracks
Bauchi

Telephone

+2348066079123

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sarkinmota online Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category