05/08/2026
Tsohon Shugaban Rundunar Sojin kasar Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan amincewar ƙara albashin jami’ai da sojojin Najeriya, yana mai bayyana matakin a matsayin ƙara ƙarfafa jin daɗin sojoji, da kuma kara musu ƙwarin gwiwa a kan lokaci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Buratai ya yaba da amincewar Shugaban ƙasa kan sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba, 2026, yana mai cewa hakan ya nuna yadda gwamnati ke fahimtar irin sadaukarwar da jami’ai da sojoji ke yi a kullum wajen kare ƙasar nan.