08/02/2024
GWAMNAN BAUCHI YA KADDAMAR DA AIKIN HANYOYI A KANANAN HUKUMOMIN TAFAWA BALEWA, BAGORO DA TORO.
A Kokarin Sa Na Ganin Ya Sake Gina Sabuwar Jihar Bauchi Ta Hanyar Shimfida Dumbin Ayyukan Raya Kasa A Birni Da Karkara, Gwamna, Sanata Dokta Bala Muhammed, (Kauran Bauchi, Jagaban Katagum, Turakin Ningi), Ya Kaddamar Da Aikin Sabbin Hanyoyi A Wasu Garuruwa A Yankunan Kananan Hukumomin Tafawa Balewa, Bagoro Da Kuma Toro, Da Ke Shiyyar Bauchi Ta Kudu.
Wadannan Hanyoyi Masu Matukar Muhimmanci Da Gwamnan Ya Kaddamar, Wadanda Za'a Dukufa Wajen Gudanar Da Aikin Su Gadan-Gadan Sun Hada Da; Muhimman Hanyoyi Wadanda S**a Hada Al'umomi Daban-Daban A Yankin Kananan Hukumomin Tafawa Balewa Da Bagoro, Da Kuma Wata Muhimmiyar Hanya A Yankin Toro, Karamar Hukumar Taro, Wadanda Al'umomin Wadannan Yankuna Za Su Ci Gajiyar Su Ta Bangarori Daban-Daban Musamman Ta Fuskar Sufurin Kasuwanci, Fitar Da Amfanin Gonaki Domin Kaiwa Kasuwanni Da Kuma Zirga-Zirgar Yau Da Kullum.
Idan Za'a Iya Tunawa, Ko A Ranakun Litinin Da Talata, Sai Da Mai Girma Kauran Bauchi Ya Kaddamar Da Aikin Wasu Hanyoyi A Kananan Hukumomin Katagum (Azare), Jama'are Da Kuma Shira, Da Kuma Ziyarar Gani Da Ido Da Ya Kayi Zuwa Aikin Katafariyar Hanyar Nan Wacce Gwamnatin Sa Ke Gudanarwa, Wacce Ta Hade Garuruwan Itas Da Kuma Gadau, A Karamar Hukumar Itas Gadau, Duk A Shiyyar Bauchi Ta Arewa.
Gwamnan, Bai Yi Kasa A Gwiwa Wajen Dawo Da Martaba Da Kuma Kimar Jihar Bauchi A Idon Duniya, Tun Bayan Hawan Sa Kan Karagar Mulki.
February 8, 2024.
Jamilu Barau Daga Bauchi