Eagle Radio Bauchi

Eagle Radio Bauchi Eagle Radio Bauchi: Mai zagaya da ku sassan duniya.

Wannan shafin mallakin Eagle Radio Bauchi ne, gidan rediyo mai zaman kansa da ke yaɗa sahihan labarai da shirye-shirye masu gamsarwa a kan mita 96.5 zangon FM daga birnin Bauchi.

Muna mika gaisuwa da fatan alheri ga dukkan masu bibiyar shafinmu, a duk inda suke a fadin duniya. Allah Ya karɓi ibadun...
25/09/2026

Muna mika gaisuwa da fatan alheri ga dukkan masu bibiyar shafinmu, a duk inda suke a fadin duniya. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya albarkaci rayuwarmu, Ya kuma sa mu dace da alherin wannan rana.

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, sun karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsoh...
25/09/2026

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, sun karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya rasu.

A cikin wata sanarwa, iyalan sun bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitar, sannan su guji yada labaran da ba su da tushe ko sahihanci.

Kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda, a cewarta, wasu mutane s**a yi amfani da sha’awar matasa kan fasahar Crypto, We...
25/09/2026

Kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda, a cewarta, wasu mutane s**a yi amfani da sha’awar matasa kan fasahar Crypto, Web3 da Blockchain wajen alakanta harkar da muradun siyasar wani ɗan takarar jam’iyyar APC a Jihar Bauchi.

Kungiyar ta ce abin takaici ne a yi amfani da sunan fasahar zamani da ake sa ran za ta taimaka wajen bunkasa matasa da tattalin arziki, wajen cimma wasu manufofin siyasa.

Ta kuma bayyana rashin amincewarta da abin da ta bayyana a matsayin amfani da sunan Crypto, Web3 da Blockchain wajen cimma manufofin siyasa, tana mai kira da a mayar da hankali kan ainihin manufar bunkasa fasahar da kuma samar da damarmaki ga matasan Jihar Bauchi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya saka tsohon Gwamnan ...
25/09/2026

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya saka tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, cikin majalisar neman kuri'un zaɓensa, duk da kasancewarsa a hannun hukumar ICPC.

Majalisar za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam, yayin da Sanata Austin Akobundu zai zama Darakta-Janar kuma Manajan Yaƙin Neman Zaɓen.

William Troost-Ekong ya karanta Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar, inda yake taka leda a ƙungiyar Al-Ahli ta gasar Qa...
25/09/2026

William Troost-Ekong ya karanta Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar, inda yake taka leda a ƙungiyar Al-Ahli ta gasar Qatar Stars League, Kamar yadda Jaridar Qatari mai suna “Al-Arab” ta ruwaito hakan.

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Muhammad Salah, ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook, inda aka ga ɗan wasan yana karanta kalmomin Shahada.

Ɗan wasan mai shekaru 33 ya koma yankin Larabawa ne a lokacin bazarar shekarar 2024, bayan ya sanya hannu a ƙungiyar Al-Khaleej ta ƙasar Saudiyya.

A watan Janairun 2026, ya koma ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar kan yarjejeniyar shekara ɗaya da rabi. Tun daga lokacin ya buga wasanni 14 a dukkanin gasa, ciki har da wasa guda a kakar bana.

A matakin ƙasa, Troost-Ekong ya buga wasanni 83 da Najeriya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025, inda ya zura ƙwallaye takwas.

Ya kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 da aka gudanar a Côte d’Ivoire, inda aka kuma zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasa na gasar.

Troost-Ekong ya kuma wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA da kuma wasannin Olympics, inda ya zama ɗaya daga cikin ƙwararrun masu tsaron baya da Najeriya ta samu a cikin shekaru goma da s**a gabata.

Cibiyar Habaka Kirkira Ta TISNI Ta Ziyarci Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi A cigaba da shirin taron baje kolin fa...
25/09/2026

Cibiyar Habaka Kirkira Ta TISNI Ta Ziyarci Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

A cigaba da shirin taron baje kolin fasaha da cibiyar habaka kirkira ta hanyar amfani da fasaha (wato Tech Innovators & Solution Network Initiative TISNI), Komitin shirya taron ya ziyarci Kakakin Majalisar Dokikin Jihar Bauchi Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman, domin tattauna muhimman batutuwa da kuma neman goyon bayan majalisar ta sa don gudanar da taro cikin nasara.

Taron wadda zai gudana a ranar 15 ga watan Oktoba, ya samu hadin wgiwa da gwamnatin Jihar Bauchi ta Ofishin Mai ba wa Gwamna Shawara kan Harkokin Matasa, kuma taro ne da zai ba da dama ga matasa yan kasuwa da ma su fasaha don su baje koli domin bunkasa su su zama ma su zaman kansu.

Da ta ke jawabi, Shugaban TISNI wadda ta jahgoranci tafiyar Hajiya Aisha Kwaku ta bayyana kudurorin taron da kuma yadda Majalisa za ta shigo da gudumawarta, inda Kakakin ya ba da tabbacin ba da goyon bayansa wajen tabbatar da nasarar taron.

'Yan Sandan Jihar Bauchi sun ce sun k**a wani mutum mai shekaru 27, Muhammad Garba Ladan, bisa zargin shake jaririyarsa ...
25/09/2026

'Yan Sandan Jihar Bauchi sun ce sun k**a wani mutum mai shekaru 27, Muhammad Garba Ladan, bisa zargin shake jaririyarsa mai watanni huɗu, Fatimah Muhammad, har ta mutu a Azare.

A cewar sanarwar ’yan sandan, mahaifiyar jaririyar ta kai rahoton lamarin bayan ta dawo gida ta tarar da jaririyar ba ta numfashi, yayin da ta ga mijinta yana fitowa daga ɗakin.

Likita a Babban Asibitin Azare ya tabbatar da cewa jaririyar ta mutu sak**akon shake maƙogwaronta. Wanda ake zargin yana ci gaba da fuskantar bincike.

25/09/2026

Here is President Bola Ahmed Tinubu’s full address to world leaders at the 81st United Nations General Assembly in New York, delivered on his behalf by Vice President Kashim Shettima.

1. Najeriya ta sake tabbatar da ƙudirinta na amfani da diflomasiyya, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa wajen magance r...
25/09/2026

1. Najeriya ta sake tabbatar da ƙudirinta na amfani da diflomasiyya, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa wajen magance rikice-rikice, maimakon amfani da ƙarfi ko tilastawa.

2. Tinubu ya yi kira da a gyara Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC), yana mai cewa tsarin rarraba iko na shekarar 1945 bai yi daidai da yanayin duniya na yanzu ba.

3. Najeriya ta buƙaci Afirka ta samu kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaro, tare da cikakken haƙƙin mamba na dindindin, ciki har da ikon veto idan ana ci gaba da amfani da shi, da kuma kujeru biyar marasa dindindin.

4. Ya bayyana shirin Najeriya na ƙara taka rawa a harkokin duniya, bisa tarihin ƙasar wajen wanzar da zaman lafiya, sasanci da ayyukan tsaro a Afirka.

5. Ya danganta manufofin harkokin wajen Najeriya da gyare-gyaren tattalin arzikin cikin gida, tare da jaddada muhimmancin ƙarfafa hukumomi, saka hannun jari da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu.

6. Najeriya ta yi watsi da ra’ayin cewa ƙasashe masu tasowa dole su zaɓi tsakanin ci gaban tattalin arziki da yaƙi da sauyin yanayi, tana mai cewa ya k**ata su samu damar bunƙasa masana’antu, rage talauci da faɗaɗa samar da mak**ashi.

7. Tinubu ya yi kira da a samar da ƙarin tallafin kuɗi, fasaha da ƙwarewa domin yaƙi da sauyin yanayi cikin adalci.

8. Najeriya ta sake jaddada Energy Transition Plan da burinta na cimma net-zero nan da shekarar 2060, ta hanyar mak**ashi mai sabuntawa, tsaftataccen girki, iskar gas da sauran hanyoyin kare muhalli.

9. Tinubu ya yi kira da kada tsoron Artificial Intelligence (AI) ya hana duniya amfani da damar da fasahar ke da ita wajen inganta kiwon lafiya, ilimi, noma, shugabanci da tattalin arziki.

10. Ya gayyaci ƙasashen duniya su ƙara haɗin gwiwa da matasan Najeriya a fannin fasaha da kirkire-kirkire, tare da saka hannun jari a harkokin dijital, broadband, bincike da kasuwancin fasaha.

11. Najeriya ta yi kira da a yi sauyi a tsarin kuɗaɗen duniya, tare da samar da sauƙaƙan rance da ingantaccen tsarin kula da basuss**a domin ƙasashe masu tasowa su iya saka jari a ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

12. Najeriya ta bayyana AfCFTA a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen sauya tattalin arzikin Afirka, tare da kira ga nahiyar ta mayar da hankali kan masana’antu, ƙara darajar albarkatun ƙasa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin da ilimi ke jagoranta.

13. A fannin tsaro, Najeriya ta yi kira da a ƙarfafa musayar bayanan sirri, dakile hanyoyin tallafa wa ta’addanci da safarar mak**ai ba bisa ƙa’ida ba, tare da magance matsalolin tsaro ta hanyar ilimi, damar tattalin arziki, shugabanci na gari da kare haƙƙin ɗan Adam.

14. Tinubu ya yi kira da a gaggauta amfani da diflomasiyya wajen magance rikice-rikice, musamman a Sudan, tare da kare fararen hula da tabbatar da isar da agajin jin ƙai.

15. Najeriya ta sake jaddada ƙudurinta na fifita haɗin gwiwa maimakon faɗa, tattaunawa maimakon rarrabuwar kai, da haɗin kai maimakon warewa, tana mai cewa Majalisar Ɗinkin Duniya mai inganci da haɗa kowa na da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, adalci da ci gaba mai ɗorewa.

24/09/2026

Jawabin Gambo Hassan "Anahaka" da ake zargi da aikata laifuka da s**a hada da fyade, fashi da makami, garkuwa da mutane, harma da karbar kudin fansa daga mata fiye da 35 a jihar Bauchi.

Address

No. 22 Buba Yero Street Behind Matrix Filling Station Along Yelwa Road Bauchi
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Eagle Radio Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category