31/12/2025
Kungiyar ZAMFARAWA FAMILY GROUP Ta Shirya Babban Taron Sada Zumunta a Bauchi
Kungiyar ZAMFARAWA FAMILY GROUP Multipurpose Cooperative Society Limited, ƙarƙashin jagorancin Sagir Adamu Alkali da Jumba Aliyu, ta sanar da shirya Babban Taron Sada Zumunta na Ƙarshen Shekara domin ƙarfafa haɗin kai, zumunci da fahimtar juna a tsakanin ’ya’yan dangin Zamfarawa da ke zaune a jihar Bauchi da maƙwabta.
A cewar shugabannin ƙungiyar, taron zai haɗa ilahirin al’ummar dangin Zamfarawa daga sassa daban-daban, tare da halartar manyan baki daga cikin wannan dangi mai albarka, ciki har da Alhaji Hussaini Ahmad, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi, da kuma Malam Yakubu Abubakar Gero, Babban Kwamishina na Ɗaya a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi.
Shugabannin ƙungiyar sun bayyana cewa an shirya wannan taro ne domin ƙara dankon zumunci, musayar ra’ayoyi masu amfani, da kuma duba hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa rayuwar ’ya’yan dangi ta fuskar zamantakewa da ci gaba mai ɗorewa.
An tsara taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 1 ga Janairu, 2026, daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma, a Masallacin Fada (Central Masjid Hall), Bauchi.
A ƙarshe, shugabannin ƙungiyar sun yi kira ga dukkan ’ya’yan dangin Zamfarawa da ke jihar Bauchi da kewaye da su fito su halarta domin samun albarkar taro, tare da roƙon Allah Ya sanya a yi taro lafiya, a kammala lafiya.