19/09/2025
HANYAR MIYA ZUWA SORO A ƘARAMAR HUKUMAR GANJUWA;
SHIN MUN RASA GATA A GWAMNATIN KAURA NE, KO KUMA KAURAN NE BAYA SON MU?
Abu ne a fili ba sai an tsaya ana dogon nazari ba, Kaura yana cikin Gwamna na gaba-gaba da jihar Bauchi ta taɓayi acikin Gwamnonin ta inma bai zama na ɗaya ba wajen shinfiɗa ayyuka a Jihar Bauchi, musamman ma dai ɓangaren tituna.
Komai adawar ka da Kaura kasan yayi ko ince yana kan yin ayyuka a Jihar Bauchi, koda kuwa akwai wata gazawa a tare da Gwamnatin tasa, ana iya cewa gazawa ce ta ɗan Adam, da kuma yadda yanayin shugabannin mu na yau yake, yanada wahala ka bawa wani shugabanci baka ga gazawar sa ta bayyana ba, adai wannan zamanin. Amma baza'a rasa masu taɓukawa ba, wanda ko shakka babu baza'a cire Kaura acikin su ba.
Amma kassh, mu Ganjuwa LGA har yau da wannan Gwamnati ta fara jin ƙanshin karshen wa'adin ta na biyu, mun rasa irin wannan garaɓasa na ayyukan alkhairi da Gwamnatin Kaura takeyi.
Wannan kuma baya nufin cewa Kaura baiyi mana aiki bane kwata-kwata, amma idan akayi la'akari da ayyukansa a sauran ƙananan hukumomi to muna iya zuwa na karshe a list.
Ya mai girma Gwamna, cikin girmamawa, muna roƙon ka, kafin ƙarshen wa'adin ka, don girman Allah inma laifi ƴan Ganjuwa muka maka, kayi hakuri ka dube mu kamar yadda kaima kake fatan Allah Ya taimake ka duk da kuwa kana masa laifi, muma mun zaɓe ka, domin akwai ƙuri'un wasun mu a cikin nasarar tun ma wa'adin ka na farko, b***e na biyu da kaci zaɓen ƙaramar hukumar da tazara mai yawa.
Tun farkon aikin wannan hanya, ana yinsa ne tamkar dama anaso ne a ruɗe mu kawai, domin bawai aikin hanyar yana matakin sub-standard bane kawai ba, aiki ne da muna iya cewa daga babu gara ba daɗi.
Tun a baya, bawai aikin yayi tafiyar hawainiya bane kawai, hatta wanda aka samu nasara yin nasa ma rashin ingancin sa yakai ace kamar ba'ayi bane ba, domin kasa da shekaru uku zuwa huɗu da yinsa, guraren da kayin ma ya koma kamar ba'ayi ba, koma ana iya cewa lalacewar sa ta wuce ta kafin a fara shi.
Mai Girma