1Arewa Tv

1Arewa Tv Labarun Duniya | Arewa | Kannywood | Littafin Hausa | Wakokin Hausa | Fadakarwa Musulunci |

News l Religion Content l Sport l Jokes & quotes l Download links l Free browsing l advice and lot more

Innalillahi wainna illaihin rajiun ..Allah ya jikan Ka Abdulfatah..Ameeen
23/07/2025

Innalillahi wainna illaihin rajiun ..Allah ya jikan Ka Abdulfatah..Ameeen

Innalillahi wainna illaihin rajiun
21/07/2025

Innalillahi wainna illaihin rajiun

Natasha Akpoti ta ce za ta koma majalisar dattawa ranar TalataNatasha Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar Kogi ta tsaki...
20/07/2025

Natasha Akpoti ta ce za ta koma majalisar dattawa ranar Talata

Natasha Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta ce za ta koma majalisar dattawa a ranar Talata.

Da take magana da ‘yan jarida a ranar Asabar yayin wani shirin horaswa a mazabar ta, Akpoti-Uduaghan ta ce ta rubuta wa majalisar dattawa wasika domin sanar da su niyyarta ta komawa zauren majalisar a ranar da aka tsara.

“Ina da kusan watanni biyu kafin cikar watanni shida,” in ji Sanatan.

“Duk da haka, na sake rubuta wa majalisar dattawa na shaida musu cewa zan koma ranar 22 ga watan nan, wato ranar Talata, da ikon Allah.

“Zan je, saboda kotu ta yanke hukunci kan hakan. Yanzu suna ta cece-kuce cewa umarni ne—ba umarni bane, amma hukunci ne.”

Akpoti-Uduaghan ta ce dakatarwar ta shafi ikon ta wajen gudanar da ayyukan majalisa.

Ta ce ɗaya daga cikin manyan ayyukan sanata shine ɗaukar nauyin kudurori da motsa batutuwa a majalisar dattawa, wanda dakatarwar ta hana ta yin hakan.

Her Excellency, Senator Oluremi Tinubu in Daura, Katsina State today to commiserate with the family of late President Mu...
20/07/2025

Her Excellency, Senator Oluremi Tinubu in Daura, Katsina State today to commiserate with the family of late President Muhammadu Buhari.

Breaking NewsJami'an Tsaro Sun K**a Matashiya Ƴar "TikTok" Fatima Zahra Kan Zargin S**a Ga Marigayi Buhari Rahotanni dag...
19/07/2025

Breaking News

Jami'an Tsaro Sun K**a Matashiya Ƴar "TikTok" Fatima Zahra Kan Zargin S**a Ga Marigayi Buhari

Rahotanni daga Zaria sun tabbatar da cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun k**a wata matashiya mai suna Fatima Zahra Saidu, wadda aka fi sani a dandalin TikTok, bisa zargin yin s**a ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da ta gabata, inda aka ce an k**a ta ne a cikin garin Zaria, kuma yanzu haka tana tsare a ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari, Zaria.

Majiyoyi sun bayyana cewa abin da ya janyo wannan k**a shi ne bidiyon da Fatima Zahra ta wallafa, inda ta bayyana ra’ayinta cewa bai k**ata a yafe wa Buhari bisa abubuwan da s**a faru a lokacin mulkinsa ba.

Wannan lamari ya tayar da kura a kafafen sada zumunta, inda jama’a ke bayyana damuwa da takaici, suna ganin hakan a matsayin take hakkin fadin albarkacin baki da tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da masu rajin dimokuradiyya na ci gaba da kiran a sako Fatima Zahra ba tare da wani sharadi ba. Suna kuma rokon jami’an tsaro da su daina zama kayan aikin siyasa, su koma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Hukumomin ‘yan sanda na Jihar Kaduna dai har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, sai dai ana ci gaba da bin diddigin batun.

Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso kenan yayinda ya ziyarci jihar Katsina wajen yin ta'aziyar marigayi Mu...
19/07/2025

Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso kenan yayinda ya ziyarci jihar Katsina wajen yin ta'aziyar marigayi Muhammadu Buhari

Shugaba Tinubu Ya Sauka A Kano Domin Yin Ta'aziyyar Aminu Dantata, Inda Gwamna Abba Ya Tarbe Shi
18/07/2025

Shugaba Tinubu Ya Sauka A Kano Domin Yin Ta'aziyyar Aminu Dantata, Inda Gwamna Abba Ya Tarbe Shi

PDP ƙarfi ta ƙara bayan fitar Atiku - Damagum Mukaddashin Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa , Ambasada Iliya Damagum, ya ba...
18/07/2025

PDP ƙarfi ta ƙara bayan fitar Atiku - Damagum

Mukaddashin Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa , Ambasada Iliya Damagum, ya bayyana cewa jam’iyyar ta fi ƙarfi ba tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya yi murabus daga jam’iyyar kwanaki biyu da s**a gabata ba.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, Damagum ya ce wannan ba shi ne karon farko da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fice daga PDP zuwa wasu jam’iyyu ba, yana mai cewa matakin Atiku ya yi dai-dai da irin abubuwan da ya saba yi a baya.

Damagum ya bayyana cewa jam’iyyar ta saba ganin yadda Atiku ke shiga da fita daga PDP a lokuta daban-daban.

A cewar Damagum, matakin Atiku ba wani babban barazana ba ne ga jam’iyyar, yana mai jaddada cewa PDP za ta ci gaba da tafiya gaba c a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Daily Nigerian Hausa

Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda tareda iyalan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun dawo Katsina bayan halar...
18/07/2025

Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda tareda iyalan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun dawo Katsina bayan halartar taron majalisar zartarwa da shugaba Tinubu ya gayyace su a jiya Alhamis

Yusuf Buhari ya ce sun ji daɗin jana'iza ta girmamawa da aka yi wa mahaifin nasu kuma "hakan ya nuna cewa ba ɗan siyasa ...
18/07/2025

Yusuf Buhari ya ce sun ji daɗin jana'iza ta girmamawa da aka yi wa mahaifin nasu kuma "hakan ya nuna cewa ba ɗan siyasa kawai aka ɗauki mahaifin namu ba, an ɗauke shi matsayin aboki kuma uba.

Buhari ya ce na kula da talakawan Najeriya - Peter ObiJagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce tsohon shugaban ƙ...
18/07/2025

Buhari ya ce na kula da talakawan Najeriya - Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari ya h**e shi da riƙe amanar talakawan ƙasar.

Yayin da yake jawabi a wajen ta'aziyar rasuwar Buhari a garin Daura, mahaifar marigayin, Peter Obi ya ce yana tuna kalaman da Buhari ya faɗa masa lokacin da yake raye.

''A lokacin da nake yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, na kai masa ziyara, kuma kiran da ya yi min shi ne, ya ce Peter ka kula da talakawan Najeriya, ni kuma na faɗa masa wannan shi ne babban muradina''.

Peter Obi ya ce babban abin da shugabanni za su koya daga halin Buhari shi ne sauƙin kansa.

BBCHAUSA

Malami Ya Rasu a Otel Lokacin Da Yake Tare da Ɗalibarsa a AnyigbaWani babban malami a jami’ar Prince Abubakar Audu da ke...
18/07/2025

Malami Ya Rasu a Otel Lokacin Da Yake Tare da Ɗalibarsa a Anyigba

Wani babban malami a jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Anyigba (tsohuwar Kogi State University), Dr. Olabode Abimbola Ibikunle, ya rasu a wani otel yayin da yake cikin mu'amala da wata ɗaliba ‘yar aji biyu na jami’ar.

Rahotanni daga kafafen sada zumunta sun bayyana cewa malamin ya mutu ne yayin da suke cikin abin da aka bayyana a matsayin “aiki na musamman a dakin otel.”

An k**a ɗalibar kuma tana hannun ‘yan sanda domin gudanar da bincike, yayin da jami’ar da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.

Address

Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when 1Arewa Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to 1Arewa Tv:

Share