
05/09/2025
Siyasar Najeriya cike take da mayaudara da masu cin Amana — Jonathan
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin mai cike da masu cin amana da kuma masu yaudara.
“A Najeriya da wuya ka ga mutum ɗaya ya faɗi abu ɗaya da safe ya kuma tsaya a kai da yamma,” in ji shi a jiya.
Jonathan ya yi wannan jawabi ne a wurin bikin cika shekara 70 na tsohon Shugaban Ma’aikatansa, Cif Mike Ogiadomhe, a Benin, babban birnin Jihar Edo.
Ya bambanta Ogiadomhe, wanda ya taɓa zama mataimakin gwamnan Jihar Edo, a matsayin mutum mai dogaro da sahihancin magana, inda ya ce: “Na sha ganin masu cin amana, musamman a zaɓen 2015 (inda na sha kaye hannun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari), amma Mike mutum ne da zai iya tsayawa ko da za a yi masa duka saboda ni.
“Maganarsa maganar gaskiya ce da za ka iya kaiwa banki. Amma yawancin ’yan siyasa ba haka suke ba. Za su gaya maka abu ɗaya yanzu, cikin awa guda ka ga sun sauya magana.”
A ’yan kwanakin nan, shugabannin PDP da dama sun rika kira ga tsohon shugaban ƙasar da ya tsaya takara a 2027.
Cikin waɗanda ke kiran Jonathan ya tsaya takarar neman tikitin PDP akwai tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana, da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.
Sai dai Jonathan bai ce komai kan kiran ba, duk da cewa a watan Mayu uwargidansa, Patience Jonathan, ta bayyana cewa mijinta zai goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ta ce ya taimaka wa Jonathan wajen samun nasara a zaɓen 2011.