11/08/2026
Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Abia yace zai sanya jihar ta zama wuri mara daɗi ga masu aikata laifuka.
Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Abia, CP Wilfred Afolabi, ya bayyana cewa jihar ba za ta zama mafakar masu aikata laifuka ba.
Ya kuma yi alƙawarin gudanar da rundunar ’yan sanda mai gaskiya, ƙwarewa da kuma amfani da bayanan sirri wajen yanke shawara, tare da mayar da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Afolabi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, a lokacin taronsa na farko da manyan jami’an rundunar ’yan sandan jihar.
Ya gargadi jami’an kan karɓar kuɗaɗen na goro daga mutane, tare da yin alƙawarin cewa zai sanya jihar Abia ta zama wuri mara daɗi ga masu aikata laifuka.
Da yake jawabi ga jami’an, Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce ya zo Abia ne da manufa guda ɗaya, yin hidima cikin gaskiya da riƙon amana, aiwatar da doka ba tare da tsoro ko nuna wariya ba, da kuma kare rayuka da dukiyoyin kowane mazaunin jihar.