22/07/2026
ISWAP ta tabbatar da mutuwar babban mai ɗaukar hotunanta, Abu Salim al-Barnawi
Ƙungiyar ISWAP ta tabbatar da mutuwar babban mai ɗaukar hotuna da bidiyonta, kuma tsohon kwamandan kai hare-hare, Abu Salim al-Barnawi, wanda aka kashe a wani yunƙurin kai hari da bai yi nasara ba kan sansanin sojojin Najeriya a makon da ya gabata.
Ƙungiyar ta fitar da sanarwar ta'aziyyar mutuwar Abu Salim al-Barnawi, inda ta tabbatar da cewa yana cikin mayaƙan da sojojin Najeriya s**a kashe yayin arangamar.
Abu Salim na ɗaya daga cikin fitattun jami'an yaɗa farfagandar ISWAP. Shi ne babban mai ɗaukar hotuna da bidiyo na ƙungiyar, wanda ke da alhakin ɗaukar hotunan hare-haren yaƙi da kuma samar da kayan yaɗa farfaganda da ake amfani da su wajen jan hankalin sababbin mambobi da kuma ƙarfafa gwiwar mayaƙan ƙungiyar.
Kafin ya shiga sashen yaɗa labarai na ISWAP, an ce ya jagoranci hare-hare da dama har zuwa ƙasar Kamaru, inda ya kai farmaki kan jami'an tsaro kafin daga bisani ya koma aikin yaɗa labarai.
Mutuwarsa na ɗaya daga cikin manyan koma baya ga tsarin farfagandar ISWAP, domin yana taka muhimmiyar rawa wajen ɗaukar hotuna da bidiyon ayyukan ƙungiyar da kuma yaɗa su.
Tabbatar da mutuwarsa daga bakin ƙungiyar ta zo ne bayan da sojojin Najeriya s**a dakile yunƙurin harin da aka kai kan sansanin soji, inda s**a yi wa maharan mummunar asara tare da kashe wasu manyan jami'an ƙungiyar.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa kashe Abu Salim al-Barnawi na nuna yadda ƙarfin ISWAP, musamman ta fuskar ayyukan yaƙi da yaɗa farfaganda, ke ci gaba da raguwa yayin da hare-haren sojoji ke ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wace irin addu'a za ku yi wa Abu Salim?