23/10/2025
DA DUMI! DUMI! : Gomnatin jihar Bauchi ta fidda sunayen Sarakuna
Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi ta Jihar Bauchi ta mika shawarar nadin sarakunan gargajiya guda goma sha ɗaya (11) ga Gwamnan Jihar Bauchi domin jagorantar sabbin masarautun da aka kirkira a jihar.
Wannan shawara na kunshe ne cikin wata takarda da Shugaban Hukumar, Alhaji Abubakar Mohammed Wabi, ya rubuta wa Gwamnan Jihar Bauchi ta hannun Sakataran Gwamnati na Jiha, bisa tanadin Dokar Sarautu ta Jihar Bauchi (Nadawa da Tube Sarauta), ta shekarar 2025.
1.Dambam Emirate Council – Alhaji Idris Bappah Musa (First Class)
2.Duguri Emirate Council – Alhaji Adamu Mohammed Duguri (First Class)
3.Gamawa Emirate Council – Alhaji Adamu Abdulkadir Adamu (First Class)
4.Ari Emirate Council – Alhaji Mohammed Kilishi Musa (Second Class)
5.Bununu Emirate Council – Alhaji Jibrin Danlami Hassan (Second Class)
6.Burra Emirate Council – Alhaji Ya’u Shehu Abubakar (Second Class)
7.Giade Emirate Council – Alhaji Mohammed Sabo Abdulkadir (Second Class)
8.Jama’a Emirate Council – Alhaji Bala Sulaiman (Second Class)
9.Lame Emirate Council – Alhaji Aliyu Yakubu Lame (Second Class)
10.Warji Emirate Council – Alhaji Ibrahim Sama’ila Boyi (Second Class)
11.Toro Emirate Council – Alhaji Adamu Umar Toro (Third Class)
Hukumar ta bayyana cewa, har yanzu ana kan aiwatar da tsarin zaben sarakuna ga Masarautar Darazo da Masarautar Lere a matakin ajin farko da na uku, da kuma Masarautar Gung-Zaar a matakin ajin farko, wadanda za a gabatar da su ga Gwamna don amincewa a nan gaba kadan.
Takardar ta kuma tabbatar da cewa ikon nadin irin wadannan sarakuna yana bisa Sashe na 16 (1) da (4) na Dokar Sarautar Jihar Bauchi ta shekarar 2025, wanda ke bai wa Gwamna damar kafa sabbin masarautu da kuma nada mutanen da s**a dace bisa al’ada da tsarin yankunansu.
Hukumar ta bukaci Gwamna ya amince da nadin sarakunan da aka zayyana tare da bayar da takardun nadin su a hukumance domin su fara gudanar da ayyukansu bisa doka.
Allah yatayaku riko ...🤲📿