Lame Emirate Council, Bauchi State

Call Directions

Lame Emirate Council, Bauchi State This Is The Official Page Of Lame Emirate Council, Bauchi State

Cikin Hotuna:A yau talata 11 08/2026 Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci Tattaunawar Dimokuraɗ...
11/08/2026

Cikin Hotuna:

A yau talata 11 08/2026 Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci Tattaunawar Dimokuraɗiyya ta GJF 2026, wadda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Sir, Ahmadu Bello International Conference Centre Bauchi, tare da sauran sarakunan gargajiya na jihar Bauchi.

Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki, masana shari’a, ‘yan siyasa, wakilan ƙungiyoyin farar hula da sauran masu kishin ci gaban dimokuraɗiyya, domin tattauna makomar dimokuraɗiyya a Afirka.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙarfafa jam’iyyun siyasa, inganta dimokuraɗiyyar cikin gida, tabbatar da bin doka, ‘yancin cin gashin kan ɓangaren shari’a da kuma inganta riƙon amana a harkokin shugabanci.

Taron ya kasance wata muhimmiyar kafa ta musayar ra’ayoyi kan hanyoyin gina dimokuraɗiyya mai ƙarfi, adalci, gaskiya da kare muradun al’umma.

Hakika, haɗin kan masu ruwa da tsaki na da matuƙar muhimmanci wajen kare makomar dimokuraɗiyya da tabbatar da kyakkyawan shugabanci a Afirka.

✍️;
Lame Emirate Media Crew.

Kai tsaye daga international Conference centre Bauchi.2026 GJF Democracy Dialogue.Beyond ElectionsCan political parties ...
11/08/2026

Kai tsaye daga international Conference centre Bauchi.

2026 GJF Democracy Dialogue.
Beyond Elections
Can political parties and the judiciary save African Democracy.

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI ƘADDAMAR DA MANYAN AYYUKAN TITUNA 18 A JIHAR BAUCHI.Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji A...
10/08/2026

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI ƘADDAMAR DA MANYAN AYYUKAN TITUNA 18 A JIHAR BAUCHI.

Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci gagarumin bikin ƙaddamar da wasu daga cikin manyan ayyukan raya birane da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kammala, tare da sauran Sarakunan gargajiya na jihar.

Daga cikin ayyukan da aka ƙaddamar akwai sabbin tituna guda 18, waɗanda aka gina a sassa daban-daban na babban birnin Jihar Bauchi, domin inganta zirga-zirga, sauƙaƙa harkokin sufuri da ƙara bunƙasa birane.

Babban bako na musamman a wajen bikin shi ne tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine ya jagoranci ƙaddamar da ayyukan a hukumance.

Halartar Mai Martaba Sarkin Lame wajen wannan gagarumin taro na ƙara nuna muhimmancin haɗin kai tsakanin masarautun gargajiya da gwamnati wajen tallafa wa ayyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma.

📸 LAME EMIRATE MEDIA CREW.

KAI TSAYE: Daga wajen ƙaddamarwa da buɗe wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da Gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin ...
10/08/2026

KAI TSAYE: Daga wajen ƙaddamarwa da buɗe wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da Gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ta kammala.

30/07/2026

HUJJAR NADIN ALHAJI BASHIR YAKUBU LAME A MATSAYIN SARKIN YAKIN BAUCHI KUMA DAYA DAGA CIKIN MASU ZABEN SARKI A MASARARUTAR BAUCHI

Duk duniya ta san yadda Sarautar Sarkin Yakin Bauchi ta kasance masu biyayya ne da tawali’u na tsawon sama da shekaru ɗari biyu. Dangane da wannan. Alhaji Bashir Yakubu Lame, Sarkin Yakin Bauchi na yanzu, kuma Daya daga cikin masu zaben Sarki a Masarautar Bauchi, mutum ne Mai kima da daraja kuma wulakanta shi tam Kar hari ne ga Alhaji Aliyu Yakubu Lame, Sarkin Lame na Farko, ɗan Alhaji Yakubu Lame (Allah ya jiƙansa), Sarkin Yakin Bauchi na 14, wanda yake ɗaya daga cikin zuriyar Mamman Kusu. Har ila yau, hari ne ga Mamman Kusu (Allah ya jiƙansa), wanda shi ne Sarkin Yakin Bauchi wanda ya tafi Sakkwato tare da Sarkin Bauchi na Farko Malam Yakubun Bauchi don karɓar tutar ƙirƙirar Masarautar Bauchi a shekara ta 1809. Idan muka dubi sama da shekaru 200 da Mamman Kusu ya yi hidima a ƙarƙashin Masarautar Bauchi. Nadin da aka yi wa Alhaji Bashir Yakubu Lame a matsayin Sarkin Yakin Bauchi Kuma Daya daga cikin masu zaben Sarki a Masarautar Bauchi ba ya nuna komai face sakamakon aminci, ƙwazo, sadaukarwa, da kuma ladan kyakkyawan aiki da kakanninmu s**a yi wa Masarautar Bauchi.

Muna kira ga Wazirin Bauchi ya tuna cewa idan za a raba Masarautar Bauchi ga waɗanda s**a gaji masarautar, to za a bawa Mamman Kusu.

MOHAMMED KARI BAI CANCANCI ZAMA WAZIRIN BAUCHI BA

Ayyukan Wazirin Bauchi

Gaba ɗaya, kamar yadda ya kamata, sarautar Wazirin Bauchi a ƙarƙashin yanayi na al’ada, tana gudanar da waɗannan ayyuka:

· Babban Jami’in Gudanarwa: Yana kula da gudanar da masarauta ta yau da kullum, yana lura da sauran jami’an majalisa da ma’aikatan fada.
· Firayim Minista da Babban Mai Ba da Shawara: Yana zama babban amintaccen mai ba da shawara ga Sarki, yana ba da shawara akan al’amuran siyasa, zamantakewa, da ruhaniya.
· Magance Rikice-rikice: Yana zama mai sulhunta rigingimu tsakanin ’yan ƙasa, masu sarauta, da Hakimai kafin su kai ga Sarki.
· Wakilcin Al’umma: Yana isar da umarnin Sarki ga jama’a kuma yana mayar da koke-koke ko buƙatun al’umma ga shugabannin gargajiya.
· Dangantakar Diflomasiyya da Tsakanin Gwamnatoci: Yana wakiltar Sarki a ayyukan gwamnati kuma yana kula da dangantakar dabaru da sauran mukamai na gargajiya da hukumomin gwamnati.

Bugu da ƙari, mukamin Wazirin Bauchi, wanda yake da daraja fiye da na Katsina, Kano, Zazzau, Daura, da sauran Masarautu da yawa a ƙarƙashin Daular Shehu Usmanu Danfodiyo, yana buƙatar wanda ya cancanci kuma mai alhaki, wanda ya yi fice a kowane fanni, mai son jama’a da Masarauta, mai kula da maganganunsa, mai ra’ayoyin da ke haɗa kan jama’a ba wai don ruguza zaman lafiya ba. Ya kamata ya zama mutum mai gaskiya ba mai son kai ko son ra’ayinsa ba, marar son kai da neman martaba. Amma akasin haka ne a game da Wazirin Bauchi na yanzu, domin rubutun da ya yi na adawa da naɗin Alhaji Bashir Yakubu Lame a matsayin Sarkin Yakin Bauchi da Mai bayar da sarauta a Majalisar Masarautar Bauchi, yana cike da sabani da son kai, wanda hakan ya jawo masa kunya a gaban masu hankali maza da mata. Bai cancanci zama ba kwata-kwata – mutum ne mai damuwa!

Don Allah, muna ƙalubalantar Waziri ya rubuta tarihin rayuwarsa!

Mohammed Kari bai taɓa yin mafarkin zama Waziri ba, in ba don goyon bayan Mai Girma Gwamna, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed CON (Kauran Daular Usmaniyya), Gwamnan Jihar Bauchi, wanda ya yi hakan da kyakkyawar niyya, amma saboda halayensa tun daga lokacin da aka naɗa shi Waziri har zuwa yau Babu wani ci gaba da yakawo sai tada fitina da Hana zaman lafiya.

Muna kira ga hukomomin da abin ya shafa da a sauke shi nan take domin a a kawo gyara na irin wulakancin da ya jawo wa Masarautar Bauchi, da al’ummar Jihar Bauchi, Najeriya, da ma wajenta.

A ƙarshe, muna godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed CON (Kauran Daular Usmaniyya), don kasancewarsa mai adalci da gaskiya.
Muna Godiya ta musamman.

Nagode sosai.

Babangida Suleiman Lame
(Danlawal na Lame)
Shugaban Ma’aikatan Mai Girma Sarkin Lame na Farko.

30/07/2026

MALAM MAMMAN KUSU THE FIRST SARKIN YAKIN BAUCHI HIS ROYAL HIGHNESS ALHAJI ALIYU YAKUBU LAME THE FIRST EMIR OF LAME 1809 TO DATE (216 YEARS)
The provision of the Bauchi State Chieftaincy Law, 2025 beyond any reasonable doubt (rationally) one of the most democratically and people oriented phenomenon ever done to the entire people of Bauchi State by the abled leadership of His Excellency, Amiable, Brilliant, Charismatic and Dutiful Senator Bala Abdulkadir Muhammed (Kauran Daular Usmaniyya) Executive Governor of Bauchi State. Since the creation of the state fifty (50) years ago. The creation of additional Emirates, Chiefdom, Districts and Ward Heads across the state takes government closer to the people, and touches their lives in all ramification. This cannot be over emphasized for it will remain a monument for reference to the generations yet unborn.
LAME EMIRATE AT A GLANCE (1809 – DATE)
Lame Emirate does have a long administrative history as it dates back to 1909 when the Malam Yakubun Bauchi the first emir went to Sokoto to receive a flag that symbolized an authority for the creation of Bauchi Emirate along with Madakin Bauchi, Sarkin Yakin Bauchi (Mamman Kusu), Ajiyan Bauchi and Wamban Bauchi respectively.
For some obvious reasons, the Emir of Bauchi Malam Yakubu was the Chief Warrior of the Caliphate (Sarkin Yakin Daular Usmaniyya), and none of these wars was fought without our hero-Mamman Kusu (the First Sarkin Yakin Bauchi) playing a leading roles. In fact, the history of Bauchi Emirate is absolutely in complete without lame emirate because it was part and parcel of the Emirate. Origin and history are two things that can never be changed, hence the history of Lame Emirate is not something that can be swept under the carpet. For this reason, the history of Lame Emirate can never be separated from Bauchi Emirate. This is what is called heredity which originates from history. On a large perspective the history of Bauchi Emirate can never be separated from that of the Sokoto Caliphate simple because of the fact that Emir of Bauchi Malam Yakubu is the Chief Warrior of the Sokoto Caliphate, hence (Sokoto Caliphate) history will equally never be complete without Bauchi Emirate.
THE JUSTIFICATION OF ALHAJI BASHIR YAKUBU LAME AS SARKIN YAKIN BAUCHI AND KING MAKER BACUHI EMIRATE
The whole world knows how humbling Sarkin Yakin Bauchi dynasty has been for over two hundred years but simplicity does not mean guarantee neither does that mean cowardice. Based on this, and vis visa in injury on Alhaji Bashir Yakubu Lame, the current Sarkin Yakin Bauchi, and Kingmaker of Bauchi Emirate is an injury to the Maman Kusu’s dynasty we were left with no option than to reply. This is because an injury on Alhaji Bahir Yakubu Lame the current Sarkin Yakin Bauchi and King Maker is an attack on Alhaji Aliyu Yakubu Lame, the First Emir of Lame, and the son of Alhaji Yakubu Lame of blessed memory, the 14th Sarkin Yakin Bauchi who is one of the descendants of the great Mamman Kusu. It is also an attack on Mamman Kusu of blessed memory who is the Sarkin Yakin Daular Usmaniyya that went to Sokoto with the First Emir of Bauchi Malam Yakubun Bauchi to receive a flag for the creation of Bauchi Emirate in 1809. Looking at over 200 years Mamman Kusu served under Bauchi Emirate. The recent appointment of Alhaji Bashir Yakubu Lame as Sarkin Yakin Bauchi and Kingmaker Bauchi Emirate from the same dynasty as decendants of Mamman Kusu does not reflect anything, but to consider it as dividends of loyalty, hard work, dedication and sacrifice as well as the overall reward of excellence made by our fore-fathers to Bauchi Emirate. Just like Emir of Bauchi who is Chief of Warrior to the Caliphate. We fought for our position and deserve them humbly in all ramifications. This is our birth right not priviledge. The so-called Waziri should be reminded that if Bauchi Emirate is to be shared to those who inherits the Emirate, the dynasty of Mamman Kusu will automatically be given their own share, unlike those positions that are merely part of the Emirate which in real sense of the word, they are not to have a recognition. Those positions who do not have history at all like the so-called Wazirin Bauchi whose father’s life was with full of unfortunate behaviours. Therefore, we will not hesitate to have his biography publically published for the world to see despite the fact that Waziri does not have respect for them at all. Definitely, you will be fixed where you belong. Who is he to challenge a recognition of excellence that spanned for centuries from the inception of Bauchi Emirate to date- whose contributions given by the Mamman Kusu’s dynasty to Bauchi Emirate.
Apart from contributions made to Bauchi Emirate, one of the great descendant of the famous Mamman Kusu’s dynasty Alhaji Yakubu Lame of blessed memory is one of the makers of the then Northern Nigeria. He completed his primary education in 1937 from Lame Primary Schools, which was established in 1914 (when there were only 4 primary schools in the then Bauchi Province). To justify our assertion among others, Alhaji Yakubu Lame began his working carrier when he was first appointed as Assistant Accountant with Bauchi Native Authority in 1943. He was in the central office between 1947 – 1953, he was turbaned as Sarkin Dawakin Bauchi and appointed as Bauchi Town District Head and at the same time, Councillor for Police, Prison and Education from 1954 – 1956, he was promoted and appointed as Magajin Garin Bauchi (Administrative Secretary) and Councillor for Finance, Works and Education. He was also the Chairman of Bauchi Native Authority Committee on Finance, Appointment and Discipline.
On the political scene, he tested his popularity in October 1956 when he was elected into the Northern House of Assembly under Northern Peoples’ Congress (NPC). He was re-elected on to the same position on 04th May 1961 under the same party.
Upon serving his tenure, and because of his antecedence in both the N.A and the Northern House of Assembly, he was appointed as Provisional Commissioner, Niger Province by the late Sir Ahmadu Bello KBE (Sardaunan Sokoto) premier of Northern Regional Government in his resolve and wisdom to strengthen Provincial Administration as the bedrock of the overall Regional Administrative Structure.
Alhaji Yakubu Abubakar Lame paid a visit to the United Kingdom on a Local Government Study Tower in 1959. He was a member of Polo Club, Provincial Loans Board, and Bauchi-Dass Local Government Committee on Education.
After the coup in 1966, and the creation of States in 1967, Alhaji Yakubu Abubakar Lame Sarkin Yakin Bauchi, was appointed as the Commissioner for Finance in the newly created North-Eastern States and performed with dignity. He was a very strong and pleasant character with a natural resolve to always get things done properly. He died on 6th June, 1994.
MOHAMMED KARI DOES NOT DESERVE TO BE THE WAZIRI OF BAUCHI
The Roles of Wazirin Bauchi
By and large, as it should have been, the title of Wazirin Bauchi under normal circumstance, performs the following roles:
Chief Administrative Officer: he manages the day-today administration of Emirate, supervises other Council officials and palace staff.
Prime Minister and Principal Adviser: Acts as the closest confident and think-thank of the Emir, offering counsel on political, social spiritual matters.
Conflicts Resolution: he acts as a mediator of disputes amongst citizens, traditional title holders, and District Heads before reaching the Emir.
Community Representation: he conveys the Emir’s directives to people and relays the community’s grievances or needs back to the traditional leadership.
Diplomatic and Inter-Governmental Ties: he represent the Emir at state functions and maintains strategic relationship with other traditional roles and government bodies.
Moreover, the position of Wazirin Bauchi, the Emirate that is higher in rank to that of Katsina, Kano, Zazzau, Daura and lots of other Emirates under the Shehu Usmanu Danfodio Caliphate needs to be held by a reasonable and responsible personality who excels and distinguishes himself in all ramifications, have the people and the Emirate at heart, who is always mindful of his words, who is always with ideas that unite people together not to destroy the peaceful co-existence. He needs to be someone who is objective not self-centred or subjective and biased, who is not over-ambitious and with full of individualism. But the reverse is the case, when it comes to the current Wazirin Bauchi for his write-up against Alhaji Bashir Yakubu Lame to be appointed as Sarkin Yakin Bauchi and Kingmaker, Bauchi Emirate Council, is full of contradictions and egocentrism which brings him shame to the faces of right thinking men and women. He does not deserve to be at all- a nuisance!
Please, we challenge him to write is odyssey!
Mohammed Kari would not have dreamt of becoming one, if not because of the support of His Excellency, Senator Bala Abdulkadir Mohammed CON (Kauran Daular Usmaniyya) the Executive Governor of Bauchi State who did it with a good mind, but with his antecedence since his appointment as Waziri to date, we wish to humbly forward our sincere call for his immediate removal in order to sanitize the damages, shame and disgrace he brought to the Bauchi Emirate and indeed, to the people of Bauchi State, Nigeria and beyond.
A stranger who does not know his origin from both sides is opportune to be part of Bauchi Emirate, had the gut to cause crises and chaos in the Bauchi Emirate as well as challenging the authority of a highly reputable dynasty without whom, the history of the Caliphate will never be complete.
The so-called Waziri of Bauchi is a benefactor of the reputable dynasty he challenges when rationality takes the inevitable contributions being given to Bauchi Emirate since its inception to date.
In conclusion, our heartfelt appreciation as a dynasty to His Excellency, The Executive Governor of Bauchi State, Senator Bala Abdulkadir Muhammed CON (Kauran Daular Usmaniyya) for being this fair and just to adequately reward nobility with nobility is exceptionally appreciated.
Thank you so much.

Babangida Suleiman Lame
(Danlawal of Lame)
Chief of Staff to His Royal Highness, The First Emir of Lame.

CIKIN HOTUNA📸 :MAI MARTABA SARKIN LAME YA KASANCE UBAN TARO, A WAJEN HORAS DA MA'AIKATAN BATV, A BAUCHI.A yau, Litinin, ...
28/07/2026

CIKIN HOTUNA📸 :

MAI MARTABA SARKIN LAME YA KASANCE UBAN TARO, A WAJEN HORAS DA MA'AIKATAN BATV, A BAUCHI.

A yau, Litinin, 28 ga Yuli, 2026, Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci babban taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa ma'aikatan Gidan Talabijin na Jihar Bauchi (BATV), wanda aka gudanar a Babban Dakin Taro na Sir Ahmadu Bello International Conference Centre, Bauchi.

Mai Martaba Sarkin Lame ya kasance Uban Taron, lamarin da ya ƙara wa taron armashi da kima, tare da nuna cikakken goyon bayansa ga duk wani shiri da ke da nufin bunƙasa aikin yaɗa labarai da haɓaka ƙwarewar ma'aikatan kafafen yaɗa labarai a jihar.

An shirya wannan horaswa ne domin ƙara wa ma'aikatan BATV ilimi, ƙwarewa da sabbin dabarun aikin jarida na zamani, ta yadda za su ci gaba da samar da sahihan labarai da ingantattun shirye-shiryen talabijin waɗanda za su amfanar da al'umma.

Taron ya samu halartar manyan baƙi, ƙwararru a fannin yaɗa labarai da ma'aikatan BATV, inda aka gabatar da muhimman darussa da shawarwari kan hanyoyin inganta aikin jarida da kuma ƙarfafa ayyukan Gidan Talabijin na Jihar Bauchi.

Daga:✍️
Sashen Yaɗa Labarai na Masarautar Lame.

Yayin da Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ke bankwana da Mai Martaba Sarkin Ningi bayan kammala wata z...
23/07/2026

Yayin da Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ke bankwana da Mai Martaba Sarkin Ningi bayan kammala wata ziyara ta musamman da ya kai zuwa Fadar Masarautar Ningi.

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI BIKIN KADDAMAR DA SHIRIN RABON TAKIN ZAMANI NA SHEKARAR 2026 A GARIN BUNUNU.Mai Marta...
21/07/2026

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI BIKIN KADDAMAR DA SHIRIN RABON TAKIN ZAMANI NA SHEKARAR 2026 A GARIN BUNUNU.

Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci bikin kaddamar da shirin rabon takin zamani na shekarar 2026, wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya jagoranta a garin Bununu, domin kara inganta harkar noma da bunkasa samar da abinci a fadin jihar Bauchi.

Bikin ya samu halartar manyan sarakunan gargajiya, ciki har da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Dr. Rilwanu Suleimanu Adamu, Zaar, Mai Martaba Sarkin Duguri, Mai Martaba Sarkin Bununu, Mai Martaba Sarkin Lere, Mai Martaba Sarkin Toro, Mai Martaba Sarkin Jama'a, tare da sauran masu rike da sarautun gargajiya da jami'an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Kaddamar da wannan shiri na nuna ci gaba da jajircewar Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed wajen tallafa wa manoma, karfafa bangaren noma, da tabbatar da wadatar abinci tare da bunkasa tattalin arzikin jihar.

✍️
Lame Emirate Media Crew⚔️
20/07/2026

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI DAURIN AUREN SARKIN GABAS DIN LAME.A yau, Asabar, 18/07/2026, Mai Martaba Sarkin Lame...
18/07/2026

MAI MARTABA SARKIN LAME YA HALARCI DAURIN AUREN SARKIN GABAS DIN LAME.

A yau, Asabar, 18/07/2026, Mai Martaba Sarkin Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, ya halarci bikin daurin auren Alhaji Shagari Bala Nabardo (Sarkin Gabas Din Lame).

Mai Martaba Sarkin Lame ya kasance Waliyin Ango, inda ya karɓi auren bisa koyarwa irin na addinin Musulunci.

An gudanar da daurin auren ne a Sabon Masallacin Juma'a na tsohowar kasuwa a cikin garin Nabardo, da ke Ƙaramar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi.

Muna addu'ar Allah ubangiji ya sanya albarka a wannan aure, ya bawa ma'auratan zaman lafiya, fahimtar juna da zuri'a ta gari. Amin ya rabbi.

✍️:
Lame Emirate Media Crew.
18/07/2026

Address

Lame Emirate Council Gumau, Toro LG
Bauchi

Telephone

+2348024371388

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lame Emirate Council, Bauchi State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share