Bauchi Daily Post

Bauchi Daily Post Jarida ce da za ta riƙa kawo muku labaran jihar Bauchi da kewaye daga 5STARS MEDIA PRODUCTION.
(1)

13/03/2026
RABON KAYAN KIRSIMETI :Uwargidan Gwamnan jahar Bauchi  Dr. Aisha Bala Mohammed ta Sanya farinciki wa al'umman kiristoci ...
25/12/2025

RABON KAYAN KIRSIMETI :
Uwargidan Gwamnan jahar Bauchi Dr. Aisha Bala Mohammed ta Sanya farinciki wa al'umman kiristoci a jihar Bauchi a yayin bikin kirsimeti.

Uwargidan gwanmnan Tayi rabon kayan abinci wa yan uwa ma abota addinin kirista don ganin cewa kiristoci a jihar sunyi bikin na bana cikin farin cikin.

Yanzu-yanzuMashigar Abuja daga Nyanya ta cushe, matafiya da ma’aikata sun maƙale cikin cunkoson ababen hawa a yanzu haka...
20/10/2025

Yanzu-yanzu

Mashigar Abuja daga Nyanya ta cushe, matafiya da ma’aikata sun maƙale cikin cunkoson ababen hawa a yanzu haka sak**akon tsaurara matakan tsaro da gwamnati ta yi kan zanga-zangar da ake yi na neman sakin jagoran ƴan neman kafa ƙasar Biyafara Nnamdi Kanu.

DA DUMI-DUMI: Shahararren Mawakin Gargajiya Na Bauchi, John Zuya, Ya Mûtû An bayyana mutuwar fitaccen mawakin gargajiya ...
19/10/2025

DA DUMI-DUMI: Shahararren Mawakin Gargajiya Na Bauchi, John Zuya, Ya Mûtû

An bayyana mutuwar fitaccen mawakin gargajiya kuma mai barkwanci daga garin Tafawa Balewa, jihar Bauchi, John Zuya, wanda aka fi sani da John Mai Molo, bayan da ake zargin an sa masa guba.

Rahotanni sun nuna cewa John Zuya, wanda kwanan nan ya dawo daga jihar Lagos inda ya je yin sana’arsa ta waka, ya rasu da safiyar jiya bayan da wasu da ake zargin abokansa ne s**a kai shi gidan cin abinci, s**a sanya masa guba mai karfi ba tare da ya sani ba.

Shaidu sun bayyana cewa mamacin ya fara nuna alamun ciwo mai tsanani kafin daga bisani ya riga mu gidan gaskiya. An kai gawarsa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, domin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsa da kuma wadanda ke da hannu a lamarin.

Marigayi John Zuya ya kasance mutum ne mai fara’a, barkwanci da baiwa ta musamman a fagen waka. Ya shahara a yankin Bauchi da sauran sassan ƙasa saboda irin wakokinsa na gargajiya da nishadantarwa.

Ina yan Bauchi, kun ganesu kuwa?
19/10/2025

Ina yan Bauchi, kun ganesu kuwa?

YANZU-YANZU: Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran ya sanar da cewa martanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan hare-haren ...
27/11/2024

YANZU-YANZU: Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran ya sanar da cewa martanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan hare-haren baya-bayan nan na Isra'ila zai wuce tunanin gwamnatin Isra'il@.

Iran ba za ta taba lamuntar keta huruminta ba, in ji Manjo Janar Mohammad Baqeri yayin wani taro da manyan kwamandojin sojoji da ya gudana a birnin Tehran a ranar Talata.

A cikin jawaban nasa, Janar Baqeri ya bayyana cewa gwamnatin Isra'il@ tana cikin matukar rudani a wannan lokaci a Gaza da kudancin Lebanon.

Jaridar Arewa

DA ƊUMI-ƊUMI: “Addini na ya hana hakan” Khadijah taƙi amincewa da musafaha da shugaban bankin UBASunanta Khadijah Abdulh...
24/11/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: “Addini na ya hana hakan” Khadijah taƙi amincewa da musafaha da shugaban bankin UBA

Sunanta Khadijah Abdulhamid, Husna daga makarantar Sakandaren Sweet Haven ta Jihar Kano, ta ki amincewa da musafaha da Oliver Alawuba, Shugaban Kamfanin UBA, a wajen gabatar da lambar yabo ta UBA Foundation Nigeria, inda ta ce Addininta ya hana hakan.

Daga Usman Umar Katsina

Gwamnan jihar Jigawa ya jagoranci jana'izar mutane sama da 100 da s**a kone sanadiyar tankan Fetur jiya da dare a garin ...
16/10/2024

Gwamnan jihar Jigawa ya jagoranci jana'izar mutane sama da 100 da s**a kone sanadiyar tankan Fetur jiya da dare a garin Majia jihar Jigawa.

Inda aka tona babban kabari aka saka duka gawarwacin ciki. Muna Addu'ar Allah ya jikansu ya yafe musu kura kuransu, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

KAJI RABO: An Naɗa Umar Bush Sarautar "Lakakan Zazzau"Wane fata zaku yi masa?
04/10/2024

KAJI RABO: An Naɗa Umar Bush Sarautar "Lakakan Zazzau"

Wane fata zaku yi masa?

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sanata Buba ya caccaki Gwamnan Bauchi Bala Mohammed kan zargin fashi da makamiSanata Buba ya caccaki Gw...
04/10/2024

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sanata Buba ya caccaki Gwamnan Bauchi Bala Mohammed kan zargin fashi da makami

Sanata Buba ya caccaki Gwamnan Bauchi Bala Mohammed kan zargin fashi da makami Yana cewa Zargi maras tushe, mara tushe, kage

Sanata mai wakiltan Bauchi ta Kudu Sanata Shehu Umar Buba, ya bayyana a matsayin mara tushe, kage da kuma zage-zage, zargin da Gwamnan Jihar Bauchi Sen Bala Mohammed Abdulkadir ya yi na cewa yana goyon baya da daukar nauyin ayyukan ‘yan fashi.

Ku tuna cewa Gwamnan ya a wata wasika da ya aike wa Shugaban kasa, Sen Bola Ahmed Tinubu mai kwanan wata 19 ga Satumba, 2024, ya yi zargin cewa Sanatan na daya daga cikin masu goyon bayan ‘yan fashi da makami a kasar nan, inda ya bukaci a k**a shi, a gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.

Sanatan wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro da Leken Asiri na Majalisar Dattawa ya tabbatar da cewa ba zai ji tsoro da irin wadannan ikirari da ba su da tushe b***e mak**a.

A wata sanarwa da mai taimaka masa na majalisar, Hassan Gajin Duguri ya fitar a ranar Alhamis, Sanata Shehu Buba ya bayyana koke-koken da Gwamnan ya kai wa Shugaba Tinubu a matsayin abin dariya ne kuma abin takaici ne.

Sanatan ya bayyana cewa da ba zai mayar da martani ga wannan zargi maras tushe ba amma ya ga ya zama dole a daidaita batun domin a karyata labarin.

Ya caccaki Gwamna Mohammed kan yadda yake ci gaba da zagi da cin mutuncin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a yayin da yake tunzura ‘yan kasa kan gwamnatin tarayya, yana mai tambayar ta yaya zai kuskura ya mika koke ga dan majalisar da ke mayar da martani ga hargitsin da ya yi maras tushe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, A matsayinsa na Sanata mai wakiltan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dokoki ta kasa, Sanata Buba ya jure wa Gwamna Bala Mohammed girman kai, wuce gona da iri, da dabi’un da ba su dace ba, wadanda s**a hada da kage-kage marasa tushe da s**a samo asali daga yadda Sanatan ke kare Shugaban kasa kan wasu kalamai na batanci.

Jagoran Addinin Musulunci a Iran Ayatollah Ali Khamenei zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin Imam khomeini dake birn...
04/10/2024

Jagoran Addinin Musulunci a Iran Ayatollah Ali Khamenei zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin Imam khomeini dake birnin Tehran.

Ayatollah Khamenei ya shafe shekaru huɗu bai jagoranci sallar Juma'a ba tun shekarar 2020, bayan martanin Iran kan Isra'ila bisa kisan babban jami'in juyin juya halin Iran Qasem Soleimani.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ta daura damarar yaki da Isra'ila, da kuma kare kanta daga hare-haren ramuwar gayya da Isr̃à'ilàr ta ce za ta kai a lokacin da ya dace.

Address

Ahmadu Bello Way
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bauchi Daily Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bauchi Daily Post:

Share