22/09/2026
MARTANI CIKIN GIRMAMAWA!!
A yau, 21/09/2026, na ci karo da wani rubutu daga ɗaya daga cikin Malaman da nake girmamawa, kuma nake bibiyarsa gwargwadon iko wato Dr Ahmad Tijani Al-azhary Amma gaskiya ta fi ƙarfin kowa, kuma idan mutum ya ga abin da yake ganin ya kamata a fayyace, yin bayani cikin ladabi da girmamawa shi ne abin da ya dace.
Ga wasu daga cikin abubuwan da na lura da su:
Na farko, wannan kalamai wata shubuha ce da ta shafe sama da shekaru biyar, inda Malamai da yawa s**a Sha furta irin waɗannan kalmomi. Sai dai lokaci, tare da hankalin masu sauraro, ya taimaka wajen fahimtar wannan falsafa da kuma kin samar mata gurbi a cikin tunaninsu.
Na biyu, ina ganin akwai kuskuren fahimta a cikin wannan tunanin. Domin kuwa, bisa ga dukkan alamu, Dr. bai saurari Dr. Sheikh Abduljabbar Kabara yadda ya kamata ba. Salon karatunsa karatu ne mai ’yanci, tare da bin al’amura daki-daki wajen gina hujjoji, da kuma kawo misalai masu bayyana abin da yake nufi, waɗanda ba sa buƙatar dogon sharhi.
Bugu da ƙari, furucin da Dr. Ya yi na cewa "Ya nuna cewa Malaman Hadisi irin su Imam Bukhari da Imam Muslim... yana buƙatar a yi masa ƙarin bayani.
Domin idan aka ɗauki maganar da wannan ma’anar, kamar ana ɗaukar waɗannan manyan Malaman Hadisi a matsayin waɗanda ba sa kuskure ko s**a zama kamar maʿasumai a cikin duk abin da s**a ruwaito. Wannan kuwa ya saba da abin da malaman Usul da malaman Jarhi da Ta'adili s**a gindaya na cewa babu wani malami da ya tsira daga kuskure a dukkan abin da ya riwaito ko ya fahimta.
Haka nan, hakikanin abin da malaman Jarhi da Ta'adili s**a tafi a kai shi ne cewa ko manyan Malaman Hadisi ana iya tattauna wasu daga cikin ruwayoyinsu ta fuskar isnadi, matani, ko illolin da ke cikinsu. Wannan batu ne da aka yi masa dogon bincike a cikin littattafan Ilmul-Jarh wat-Ta'dil.
Saboda haka, tambayar da ta taso a nan ita ce:
Shin Malam Abduljabbar Kabara ne ya fara s**ar wasu daga cikin ruwayoyin da s**a zo a cikin littattafan Bukhari da Muslim, ko ma Kutubus-Sitta baki ɗaya?
Ko kuwa wannan hanya ce da Malaman Hadisi s**a daɗe suna amfani da ita wajen binciken ruwayoyi?
Shin abin da aka fada ko kuma ruwayar da ake magana a kai daidai take da yadda aka fahimce ta?
Sannan: Ina Dr Ahmad Tijani Al-Azhary yake a lokacin da Dr. Sheikh Abduljabbar Kabara yake gudanar da irin wannan bincike?
Abin da nake son tunasarwa shi ne, duk wanda yake bibiyar Sheikh Abduljabbar zai san cewa yana cike da misalai da s**a nuna cewa yana s**ar wasu ruwayoyi da s**a zo cikin irin waɗannan littattafai, Wanda tuntuni dama kuma Malamai sun yi aiki mai yawa a kan wannan fanni.
Daga cikin fitattun waɗanda s**a yi irin wannan aiki akwai Imam al-Daraqutni (الدّارقطني), musamman a cikin littafinsa al-Ilzamat wat-Tatabbuʿ.
Wannan bincike yana faruwa ne bisa tsarin da Sheikh Abduljabbar yake bi wajen nuna illolin wasu ruwayoyi: yana bibiyar isnadi, sannan ya duba matani, ya kwatanta hanyoyin riwaya, sannan ya kawo misalai da hujjoji.
MISALI NA FARKO — SAHIH MUSLIM
Daga cikin misalan akwai hadisin:
«لا يحل لامرأة أن تسافر وليس معها محرم»
Muslim ya kawo shi ta wata hanya kamar haka:
Ibn Abi Dhi'b → Sa'id → Mahaifinsa → Abu Hurayrah → Annabi ﷺ
Idan muka duba wannan isnadi, za mu ga cewa an yi bincike a kan yadda Sa'id al-Maqburi ya riwaito hadisin. A wasu hanyoyin ya riwaito shi daga mahaifinsa daga Abu Hurayrah, yayin da a wasu hanyoyin aka riwaito shi kai tsaye daga Abu Hurayrah ba tare da ambaton mahaifinsa ba.
Al-Daraqutni ya kawo hanyoyi daban-daban na riwayar wannan hadisi daga Sa'id, ciki har da hanyoyin Malik, Yahya ibn Abi Kathir da Suhayl.
Saboda wannan bambancin ne aka binciki batun ambaton “mahaifinsa” a cikin isnadin.
Idan aka lura da wannan misali, za a fahimci cewa al-Daraqutni ya bibiyi isnadin sosai, ya kwatanta hanyoyin riwaya, sannan ya nuna abin da yake ganin akwai buƙatar a tattauna a cikinsa.
MISALI NA BIYU — SAHIHUL BUKHARI
Akwai kuma hadisin da Imam Bukhari ya kawo game da Abdullah ibn Mas'ud da maganar duwatsu uku lokacin da aka ambaci yadda Annabi ﷺ ya je bayan gida.
Al-Daraqutni ya binciki isnadin wannan hadisi, musamman yadda aka riwaito shi daga Abu Ishaq, da kuma batun Abu Ubaydah da ko ya ji wannan riwaya kai tsaye daga mahaifinsa, Abdullah ibn Mas'ud.
Wannan ma yana daga cikin misalan da aka tattauna a cikin ilimin ʿIlal.
KUMA BA AL-DARAQUTNI BANE KAWAI YAYI IRIN WANNAN RUBUTU
Ba Al-Daraqutni kaɗai bane ya yi irin wannan aiki . Akwai wasu manyan malaman Hadisi da s**a yi bincike a kan wasu ruwayoyi da s**a zo cikin Sahihayn, daga cikinsu akwai:
- Abu Ali al-Ghassani al-Jayyani, wanda ya yi magana a kan wasu matsaloli da s**a shafi Sahihayn.
- Ibn al-Qattan al-Fasi, wanda ya tattauna wasu wurare a cikin Bayan al-Wahm wal-Iham.
- Haka kuma Ibn Hajar ya ƙididdige wasu daga cikin hadisan da aka tattauna a kan su dangane da Sahih al-Bukhari; an ambaci cewa adadinsu ya kai 110, daga cikinsu 32 kuma Muslim ma ya riwaito su.
DAJIYA!
Duk wanda yake bibiyar Sheikh Abduljabbar zai fahimci cewa tsarin bincikensa ba wai fara s**a kai tsaye ba ne. Yana fara ne da bibiya da nazarin isnadin hadisi, sannan ya koma ga matani, ya kwatanta ruwayoyi da juna, ya kawo misalai, sannan ya auna abin da ya zo cikin ruwayar da abin da hankali salimi zai iya fahimta.
Haka kuma, Malam ya Gina wadannan al'amura bisa dogaro da umarni na ruwaya, da ta zo daga Imam Ahmad da sauran masu riwaya domin ƙarin bayyana abin da yake nufi.
Hadisin Iza Samitumul Hadisa....
Tabbas wanann hadisi yasa mun gane cewa kazanta ce a cikin hadisin Anas na Ummu Haramin.
Kanzanta ce a cikin hadisin: Kewaya mata
Kazanta ce a cikin sifar Auren Nana Safiyya da s**a fada.
Kazanta ce acikin yanayin da aka shiga Kahibar.
Cin zarafin ne a cikin Ruwayar Magabatan SHUGABA(SllaHu AlaiHi W AliHi W Sallam)
Saboda haka, ina ganin abin da ya fi dacewa shi ne a saurari maganar Sheikh Abduljabbar gaba ɗaya, a fahimci tsarin bincikensa, sannan a yi hukunci kan abin da ya faɗa bisa cikakkiyar fahimta, ba wai a ɗauki jimla guda ɗaya a yi mata fassarar da ba ta dace da sauran bayaninsa ba.
Hankali salimi, tare da ingantacciyar Hausa, yana buƙatar a kawo misali da harshen da mai sauraro zai fahimta. Wannan shi ne abin da ya sa Hausawa da dama s**a fahimci saƙon da Sheikh Abduljabbar yake isarwa, tare da fahimtar cewa yana ƙoƙarin kare wannan janabi mai tsarki, wato Annabi Muhammad ﷺ, ta hanyar bincike da tambayar ingancin ruwayoyin da ake dangantawa gare shi.
Dan uwanku a Allah
Annabhaan 2026