17/07/2026
NAGARI NA KOWA – BAUCHI LGA 2026
Hakika al'ummar Karamar Hukumar Bauchi sun samu jajirtattun shugabanni. Hon. Umar Aliyu Zungur (Wakilin Tsaftan Bauchi ) ya nuna nagarta tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin Karamar Hukumar Bauchi, inda cikin ƙanƙanin lokaci ya aiwatar da ayyukan alheri da dama tare da samar da daidaito tsakanin al'ummar cikin gari da na wajen garin Bauchi LGA.
Haka kuma, Hon. Sani Mahmood (Wakilin Jarmai), wanda ke riƙe da muƙamin Sakataren Shugaban Karamar Hukumar Bauchi, mutum ne mai riƙon amana, jajircewa da ƙwazo wajen gudanar da ayyukansa.
Tabbas, waɗannan shugabanni zaɓin al'umma ne, kuma muna fatan Allah Ya ci gaba da ba su hikima da ƙarfin guiwar ci gaba da yi wa al'umma hidima.
✍️
Lukman Yakubu Bayara
(Talban Nasarawan Bayara)