16/11/2025
Masu Buƙata Ta Musamman (Guragu): Wani Bangare Na Al’umma Wanda Shima Ya Cancanci Kulawa da Girmamawa.
A cikin kowace al’umma, akwai rukuni na mutane da ake amfani da kalmar “masu buƙata ta musamman” wurin bayyana su. A cikin wannan rukuni akwai guragu — wato mutanen da Allah ya yi wa wani nakasa a ɓangaren jiki, wanda hakan ke iya shafar tafiya, motsa jiki ko wasu ayyuka na yau da kullum.
Amma duk da wannan, guragu su ma ɓangare ne na al’umma; mutane ne masu cikakkiyar hikima, ƙoƙari, baiwa, kuma suna taka rawar gani a ci gaban kowace ƙasa.
Yawanci mutane s**an yi kuskuren danganta nakasa da gazawa, ko kuma a ɗaukarsu a matsayin mabarata. Amma hakikanin gaskiya shi ne, nakasa ba rashin basira ba ce, kuma ba ta rage darajar mutum ko ƙimarsa saboda akwai guragu masu hazaka a fannoni da dama kamar, karatu da bincike, fasaha da kere-kere, kwallon ƙafa (Paralympics), ƙira da tallace-tallace, koyarwa ko wani shugabanci da sauran fannoni.
Duk da irin baiwar da suke da ita, guragu suna fuskantar kalubale da dama da ke hana su damar kaiwa ga abubuwan da suke da muradi a rayuwarsu. Wadannan sun haɗa da:
1. Kowa yana ganinsu a matsayin mabarata, ana kuma kallon kamar zuciyarsu ta mutu. Idan aka ce su daina bara su koma sana’a, idan sun koma sana’a babu wanda zai sayi kayansu. Haka kuma yawanci babu tallafin jari da zai taimaka musu su fara sana’a mai karfi.
2. Rashin damar shiga wuraren jama’a kamar Makarantu, Kasuwanni da wuraren taro da dama ba su da abubuwan da s**a dace da masu nakasa. Wannan yana hana su samun damar da sauran jama’a ke da ita.
3. Tsangwama da raini da suke fuskanta saboda wasu mutane kan yi musu kallon ƙasa ko su raina su. Wannan tsangwama kan jefa su cikin damuwa, rasa kwarin gwiwa, da kuma warewa daga al’umma.
4. Rashin ilimi mai inganci idan muka duba yawancin yara guragu ba sa samun ilimi yadda ya kamata saboda rashin kayan tallafi, rashin kekunan zuwa makaranta ko mai kaisu, rashin makarantu masu kayan bukata irin nasu.
5. Rashin guraben aiki wasu ba sa samun aiki saboda nakasa, ko a yi musu bambanci duk da cewa sun fi kwarewa fiye da wasu.
Ya kamata al’umma mu fahimci cewa guragu su ‘yan uwa ne, yara ne, malamai ne, shugabanni ne, kuma mutanen da ke da cikakken cancantar zama jigo a al’umma.
Saboda haka dole ne mu mutunta su da cikakkiyar girmamawa, mu ba su dama iri ɗaya da sauran jama’a, mu yi gine-gine da tsare tsare masu sauƙi ga masu nakasa, daina tsangwama da cin zarafinsu.
Masu buƙata ta musamman, musamman guragu, ba su zo duniya da rashin komai gaba ɗaya ba. Allah ya halicce su da hikima, baiwa, da daraja kamar sauran kowa.
Al’umma ce kawai take da alhakin samar da dama, fahimta da kulawa domin su samu damar bunƙasa.
Idan muka rungume su, muka ba su girmamawa, muka kare su daga wariya — to lallai za mu gina al’umma adilciya, mai haɗin kai, wadda kowa ke da gurbi a cikinta.
Allah ya bamu ikon gyarawa da kyautatawa kowa.
Daga
Ibrahim Kabir Abubakar (Legend).