14/07/2025
Mutuwar Buhari Rashi Ne Na Afrika Gaba Ćaya, Cewar Shugaban Ćasar Kenya, William Ruto
Shugabannin Afrika da dama sun gabatar da taâaziyya tare da bayyana kalmomin yabo ga tsohon shugaban Ćasar Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya mutu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025, yana da kimanin shekaru 82.
Buhari wanda ya mulki Najeriya daga 2015 zuwa 2023, bayan ya shugabanci Ćasar a matsayin soja a 1980, sun bayyan shi a matsayin mutum mai tsari da Éaâa, sannan kuma jajirtaccen shugaba, kamar yadda Dokin Ćarfe TV ta ruwaito.
1. "Na kaÉu da samun labarin rasuwar tsohon shugaban Ćasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a madadin gwamnati da alâummar Tanzaniya, ina miĆa saĆon taâaziyya".
Cewar shugabar Ćasar Tanzaniya, Samia Saluhu Hassan.
2. "A matsayin Ćasar Afrika ta Kudu, muna tare da Ćasar Najeriya kan alhinin da kuke ciki. Shugabancin Buhari ya haÉa Ćasashenmu biyu kusa da juna. Sannan kuma, kamar yadda muka so, wannan alaĆa ta ba da gudunmawa wajen samun ci gaba da bunĆasar Afrika".
Cewar shugaban Ćasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
3. "Ina miĆa saĆon taâaziyya a madadina da alâummar Ćasar Burkina-Fasa ga alâummar Najeriya da iyalan shahararren marigayin. Ina jinjina wa wannan soja, kuma dattijon Ćasa wanda ya yi aiki domin gina Ćasarsa".
Cewar shugabar Ćasar Burkina-Fasa, Kaftin Ibrahim Traore.
4. "Mutuwar shugaba Buhari ba rashi ne na iya alâummar Najeriya ba, rashi ne na Afrika gaba Éaya, gagarumin rashi ne na hikimarsa, da tsayuwar dakansa kan Ć´anci da samar da arziĆi da walwala ga alâummar Najeriya".
Cewar shugaban Ćasar Kenya, William Ruto.