22/08/2026
Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, ya ba da labarin wani lamari mai ban mamaki da ya faru a lokacin da yake matsayin DPO a Ago Iwoye, Jihar Ogun.
Disu ya ce wani tsohon soja ya taɓa zuwa ofishin ’yan sanda yana matsa musu lamba da su kashe ɗansa, wanda ɗalibin jami’a ne, bayan an k**a shi bisa zargin kasancewa cikin ƙungiyar asiri.
A cewarsa, mahaifin ya shafe kusan yini yana roƙon jami’an su kashe ɗan nasa, yana mai cewa ba ya son ya koma gida saboda abin da ya aikata.
Sai dai abin mamaki shi ne, washegari mahaifin ya sake komawa ofishin ’yan sandan, amma wannan karon ya zo ɗauke da abinci domin ya kai wa ɗansa da ake tsare da shi.
IGP Disu ya ce lamarin ya nuna irin yanayin da wasu iyaye kan tsinci kansu a ciki, inda fushi da takaici kan haɗu da ƙauna da kulawar da suke yi wa ’ya’yansu.
Ya bayyana wannan labari ne a Abuja yayin wani taron matasa mai taken National Youth Leadership and Security Dialogue, wanda Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta shirya.
Taron ya mayar da hankali ne kan rawar da matasa za su taka wajen shugabanci, inganta tsaro da kuma hana tashin hankali da daba.
Disu ya ƙara da cewa duk da matsalar da matashin ya fuskanta a lokacin, daga bisani ya kammala karatunsa, ya yi aure, sannan ya zama uba.
Ya ce labarin ya kasance darasi mai nuna cewa kuskuren da mutum ya aikata a wani lokaci bai k**ata ya zama ƙarshen rayuwarsa ba, musamman idan aka samu damar gyara da komawa kan turba.