18/10/2025
YANZU-YANZU: Hedkwatar tsaro ta ƙaryata labarin yunkurin juyin mulki a Nijeriya
Hedkwatar Tsaron Najeriya ta karyata rahotannin karya da na mugunta da ke danganta soke bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai da zargin yunkurin juyin mulki da wasu jami’an soji s**a yi.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa an k**a jami’ai 16 — daga mukamin Kyaftin zuwa Birgediya Janar — ta Hukumar Leken Asirin Tsaro (DIA) bisa zargin gudanar da tarurrukan boye don kifar da gwamnati.
Haka kuma, kafar ta zargi cewa soke bukukuwan ranar ‘yancin kai ta Oktoba 1 na da nasaba da wannan zargin shirin juyin mulki.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Asabar, sojojin sun bayyana cewa wannan rahoton da ya ambaci k**a jami’ai 16 kwanan nan, an tsara shi ne domin tayar da hankalin jama’a da kuma haifar da rashin amincewa a tsakanin ‘yan Najeriya, k**ar yadda Punch ta ruwaito.