Rayhaan Radio Birnin Kebbi

Rayhaan Radio Birnin Kebbi Welcome to Rayhaan 99.9FM Radio Birnin Kebbi

05/09/2025

I got over 100 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

14/08/2025

Saurari Yadda ta Kaya a zaman Kotu, Kan Shari'ar Abba Yarima

👇👇👇👇👇👇

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ziyarci iyalan marigayi Aminu Alhassan Dantata a jihar Kano ranar Juma’a domin ta’azi...
19/07/2025

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ziyarci iyalan marigayi Aminu Alhassan Dantata a jihar Kano ranar Juma’a domin ta’aziyyar rasuwarsa.

Cikin hotunan akwai ɗan marigayin Tajudeen Dantata da attajirin mai kuɗin Afirka Aliko Dangote da kuma dattijon ƙasa Tanko Yakasai.

📸 - Fadar Shugaban Ƙasa

Jami'ar Kogi ta tabbatar da mutuwar malami a otel yayin da yake tare da É—alibaRahotanni sun bayyana cewa malamin mai sun...
19/07/2025

Jami'ar Kogi ta tabbatar da mutuwar malami a otel yayin da yake tare da É—aliba

Rahotanni sun bayyana cewa malamin mai suna Olabode Abimbola Ibikinle, ya je wani otel da ke Anyigba tare da wata É—aliba mai suna Miss Glory Ojochegbe Samuel amma ya rasu yayin da suke lalata.

Ba za Mu Lamunci Cin Muntucin Gwamnan Kebbi ba--- TKT ta ja Kunnen  Yan AdawaKungiyar TKT ta lashi takobin daukar Mataki...
19/07/2025

Ba za Mu Lamunci Cin Muntucin Gwamnan Kebbi ba--- TKT ta ja Kunnen Yan Adawa

Kungiyar TKT ta lashi takobin daukar Matakin doka kan duk wani Mai s**ar Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Nasir Idris batare da kwakkwarar hujja ba.

Kakakin Kungiyar Honorabul Umar Namashaya Diggi ne ya bayyana hakan yayin da yake zan tawa da manema labarai a Ofishin Kungiyar dake Birnin Kebbi.

A cewar Namashaya, Kungiyar ba za ta lamunci yadda wasu ke amfani da siyasa wajan cin mutumcin Manyan mutane a jihar ba, musamman Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris.

Ya kuma kara da cewa, akwai bukatar Yan adawa su yi amfani da hujjoji wajan yin s**a batare da cin munci ko kazafi ba

Sai dai tun da fari, Honorabul Umar Namashaya Diggi ya mika sakon ta'aziyyar kungiyar ga Daukacin Al'ummar Najeriya bisa rasuwar Tsohon Shugaban Kasa Muhammad Buhari.

A karshe ya kuma bukaci Yan Najeriya da su daura damar yin Rajistan Katin zabe da zarar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bada damar yin hakan.

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rasu
13/07/2025

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rasu

Yanzu-Yanzu: Wata Sanata Ta Fice Daga Jam'iyar LP zuwa ADCSanatar Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja Ireti Kingibe da...
12/07/2025

Yanzu-Yanzu: Wata Sanata Ta Fice Daga Jam'iyar LP zuwa ADC

Sanatar Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja Ireti Kingibe da ke cece-kuce da ministan Abuja ta shiga jam‘iyyar hadaka ta ADC.

Idan ba amanta ba, Yar siyasar ta yi nasarar zama sanata a zaben 2023 a karkashin jam‘iyyar LP, an kuma ruwaito cewa, tana yawan samun sabani da ministan Abuja Nyesom Wike musamman kan rusau da kwace filayen mutane da ake zargin ministan na yi ba bisa ka‘ida ba.

12/07/2025

I got over 500 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

Yanzu-Yanzu: Mintuna kadan da tsare shi, an sallami Dan Bello ba tare da bata lokaci ba.Me kuke tsammanin yasa an sallam...
12/07/2025

Yanzu-Yanzu: Mintuna kadan da tsare shi, an sallami Dan Bello ba tare da bata lokaci ba.

Me kuke tsammanin yasa an sallame shi da gaggawa?

Yanzu Yanzu : Rahotanni na nuna cewa,  Wasu Jami'an tsaro sun k**a Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ...
12/07/2025

Yanzu Yanzu : Rahotanni na nuna cewa, Wasu Jami'an tsaro sun k**a Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello a Kano.

DW HAUSA ta ruwaito cewa, an k**a Dan Bello ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Address

14 Sani Abacha Bypass Road
Birnin-Kebbi
860101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rayhaan Radio Birnin Kebbi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Rayhaan Radio Birnin Kebbi:

Share

Category