Nagari FM B/Kebbi

Nagari FM B/Kebbi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nagari FM B/Kebbi, Radio Station, Birnin-Kebbi.

13/07/2025

Allah yayiwa Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari Rasuwa a Birnin Landon: Inji Garba Shehu

12/07/2025

Mintuna kadan da tsare Dan Bello an sallame shi ba tare da bata lokaci ba.
Me kuke tsammanin yasa aka sallame shi da gaggawa haka?
Source: DW

12/07/2025

Yanzu Yanzu Jam'ian tsaro sun k**a Dan Bello a filin jirgin Sama na Malam Aminu Kano:

Source: DW Hausa

Wasu da Ake zargi Yan kungiyar Lakurawa ne sun halaka jami'an tsaron Yan sanda Ukku a zogirma.Bayanai sun nuna cewa wasu...
12/07/2025

Wasu da Ake zargi Yan kungiyar Lakurawa ne sun halaka jami'an tsaron Yan sanda Ukku a zogirma.

Bayanai sun nuna cewa wasu da Ake zargi Yan kungiyar Lakurawa ne sun Kai hari Kan hanyar zogirma zuwa tilli dake karamar hukumar mulkin Bunza a wani yunkuri na farmakar matafiya a Kan hanyar.

Sai dai Bayan Samun labarin ne baturen Yan sanda yankin zogirma nan take yanada wata runduna ta Musamman domin Kai dauki da ganewa ido abinda yafaru tareda taimakon wata runduna ta Musamman ta jami'an kwantar da tarzoma Daga babban Birnin jaha.

Musayawar wutar da akayi tsakanin Yan bindigar da jami'an tsaro shine yayi sanadin Rasa ran jami'an tsaro na Yan sanda Ukku

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani bayani da kakakin rundunar yan sanda ya fitar Nafiu Abubakar.

Bayanin yakara dacewa Yan bindiga da dama sun halaka yayin batakashin.

Daga karshe kwamishinan Yan sanda na Jaha Bello Sani ya yabawa kokarin jami'an tsaro da kuma sadaukarwar Wadanda S**a Rasa rayukansu.

Gwamnan jaha Dr Nasir Idris Kauran Gwandu Shima ya tabbatar da faruwar lamarin lokacinda yake sanarda Batun dage Taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a babban Birnin Jaha.

06/07/2025

Shirin Qeqe da Qeqe na Ranar Jumaa 04-07-2025.

Wanda ya maida hankali Kan Batun sabuwar tafiya.

Real Madrid ta buga wasanni biyar a gasar Club World Cup amma Rodrygo bai fara wasa ko ɗaya ba, lamarin da ke sa wasu na...
06/07/2025

Real Madrid ta buga wasanni biyar a gasar Club World Cup amma Rodrygo bai fara wasa ko ɗaya ba, lamarin da ke sa wasu na ganin ƙungiyar na son sayar da shi.

Tashen matashin ɗan wasan Madrid Gonzalo Garcia na iya kawo cikas ga Endrick kasancewar waje ɗaya suke bugawa.

A hirarsa da BBC, Malam Garba Shehu ya ce Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tafi Birtaniya ne domin duba laf...
03/07/2025

A hirarsa da BBC, Malam Garba Shehu ya ce Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tafi Birtaniya ne domin duba lafiyarsa k**ar yadda ya saba, amma daga baya sai ya kamu da rashin lafiya.

Hukumar Tsaron Civil Defence ta Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da lalata layin wutar lantarki a gar...
01/07/2025

Hukumar Tsaron Civil Defence ta Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da lalata layin wutar lantarki a garin Fagam da ke ƙaramar hukumar Gwaram.

Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya fitar a ranar Litinin 30 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta ce an k**a mutanen ne a ranar 25 ga Yuni da misalin ƙarfe 12 na rana, bayan da s**a lalata layin wutar lantarki da ke kan hanyar Fagam–Lele–Kwayi.

Hukumar ta ce ta ƙwato kayayyaki da s**a haɗa da insulato 6 na high tension, tukwane 15 na insulato, ragowar insulato 11, da wayoyin layin wutar lantarki masu tsawon mita 20.7.

Haka kuma an ƙwato sandar high tension ɗaya, spana 6, ƙugiya da kusoshi 5, wuƙa, da babur nau’in Boxer mai lamba KMC 266 QN.

Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar 10 ga Yuni, hukumar ta kuma gano manyan wayoyi uku a kusa da dam ɗin Kuda na ƙaramar hukumar Babura.

Shugaban hukumar, Bala Bawa Bodinga, ya ce za a gurfanar da waɗanda aka k**a, tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da kare kadarorin ƙasa a faɗin jihar.

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa bai k**ata ace masu satar kudin talakawa suna kai kudaden kasashen tur...
30/06/2025

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa bai k**ata ace masu satar kudin talakawa suna kai kudaden kasashen turawa ba.

Dangote yace babu kasar da ba’a sata, amma banbancin misalin kasashen Asia dana Afrika shine, idan sun saci kudin suna zuba jari dasu ne a kasashen su maimakon kaiwa kasashen Turawa.

Dangote yace ba wai yana karfafawa jami’an gwamnati satar kudin talakawa bane amma yana da kyau su san cewa k**ata yayi su rika amfani da kudin a cikin gida maimakon kaiwa kasar waje dan ci gaban kasar.

Gwamnatin Borno ta karyata rahoton UNICEF na cewa yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar sun haura 2,000,000.Kwamishinan ...
29/06/2025

Gwamnatin Borno ta karyata rahoton UNICEF na cewa yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar sun haura 2,000,000.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe shi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Maiduguri.

Ya ce, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar ba su wuce 800,000 ba, sabanin rahoton UNICEF da ya bayyana cewa suna kai miliyan biyu.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, wannan alkaluma na miliyan biyu da UNICEF ta fitar ba na Jihar Borno ba ne kaɗai, illa na gaba ɗaya yankin Arewa maso Gabas.

Kwamishinan ya ce gwamnati na ɗaukar matakai don ci gaba da rage yawan yaran da ba sa samun damar ilimi, musamman ta hanyar gina sabbin makarantun firamare.

Ya kuma ce akwai buƙatar hada gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin agaji domin kawo sauyi a tsarin ilimi, musamman a wuraren da aka fi samun matsalolin tsaro.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani da kuma mutanen da aka raba da muhallansu ta Najeriya ta ce 'yan gudun...
27/06/2025

Hukumar kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani da kuma mutanen da aka raba da muhallansu ta Najeriya ta ce 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da s**a zo daga wasu kasashen zuwa Najeriya sun kai 138, 154.

Address

Birnin-Kebbi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nagari FM B/Kebbi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Nagari FM B/Kebbi:

Share

Category