26/09/2025
📢 SANARWA GA MASU NEMAN SHIRIN TVET
A jiya Laraba 24 ga Satumba, 2025
An fara tantance aikace-aikacen shirin TVET na watanni 6, kuma na shekara 1 zai biyo baya nan gaba kaɗan.
Da zarar ka shiga portal ɗinka, za ka iya ganin ɗaya daga cikin waɗannan matsayin:
✅ APPROVED (An Amince):
An ware maka cibiyar koyarwa. Za ka samu saƙo ta imel daga TVET. Ka bi umarnin ciki, sannan ka garzaya cibiyar cikin kwanaki 5 daga lokacin da ka karɓi imel. Rashin zuwa zai sa a maye gurbinka da wanda ke jira.
⏳ PENDING-APPROVAL (Jiran Amincewa):
Har yanzu ba a ware maka cibiya ba. Ka ci gaba da duba.
📤 APPROVAL-REQUESTED (Neman Amincewa):
An aika aikace-aikacenka zuwa cibiya don tantancewa. Idan sun kammala, zai koma Pending-Approval, daga baya kuma Approved.
⚠️ Invalid credentials ko Blank program:
Shirin da ka zaɓa babu shi a yanzu. Za a gyara maka.
ℹ️ Lura: Aikin yana tafiya batch by batch. Idan ba ka samu amincewa a rukuni na farko ba, zaka iya samu a na gaba. Saboda haka, ka ci gaba da duba imel ɗinka akai-akai.