Jannat Online TV

Jannat Online TV Domin samun labarai da dumi duminsu ziyarci shafin Jannat Online TV

"Babu abu marar tabbas   kamar duniya, "yan uwa murage izza da dagawa yau in kai ne gobe bakai bane,  duniya kamar rawar...
22/09/2025

"Babu abu marar tabbas kamar duniya, "yan uwa murage izza da dagawa yau in kai ne gobe bakai bane, duniya kamar rawar "yan mata ce na gaba ya koma baya, kada ka raina taimako domin bakasan waye zai maka rana ba, kada kuma kasa ran kayi alkhairi dole sai an ma zaka mutu da bakin chiki in ka sa ran sai an maka halacci".

*Ya Ubangiji ka kara hadamu da abokai nagari da zamu girnama junan mu da Amana*🙏🏻

"Damuwa tayi yawa muke sawa zuciyar mu hakuri da juriya da dangana, domin wannan yanayi ko kai baka da damuwa toh damuwa...
21/09/2025

"Damuwa tayi yawa muke sawa zuciyar mu hakuri da juriya da dangana, domin wannan yanayi ko kai baka da damuwa toh damuwar wani dan uwanka ta dameka da irin mugwayen labarin da muke ji idan kuma babu damuwar kowa data dame ka to ka binciki Imaninka, sai dai wanda yake sa rai da rahma ubangiji kada wani abu ya dameshi domin wata rana komai zai zama tarihi".

*Ya ubangiji ka yayewa duk yan uwa musulmi duniya ko wacce damuwa Ameen*🙏🏻

18/09/2025

"Yan uwa kada muke hange mu tsaya iya inda Allah ya tsaidamu, kada kuma muruɗu da tsayin rayuwa, kullum muɗauki kowace rana a matsayin tamkar itace ranarmu ta ƙarshe a duniya zamu iya tafiya ko yaushe, hakan shi ne zai ba mu damar aiwatar da kyawawan ayyuka nagari domin mu yi guzuri ga lahirarnu".

*Allah ka datar damu karshen mu yayi kyau mucika da imani Ameen*🙏🏻

RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYABabban Daraktan cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPC                 ...
11/09/2025

RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA

Babban Daraktan cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundi
ya Gwangwaje tsohon shugaban Hukumar NPC Dr. Raji Mustapha da wasu Daraktocin ma'aikatar ta NPC guda biyu da s**ayi ritaya daga aiki da Sabbin motoci na zamani

Idan zaku iya tunawa yau shekera guda daidai dayin handover aiki tsakanin Dr. Raji Mustapha da kuma Dr. Baffa Babba Dan'agundi wanda Dr. Baffa yayi alkawarin zai gayyaci tsohon shugaban dan shirya masa walima ta musamman da kuma alkawarin cigaba da mu'amala dashi cikin mutunci,
yau Shekera guda kenan yau kuma Dr. Baffa ya gayyaci shi tare da shirya masa walima ta musamman da bashi kyautar mota, bayan shi kuma akwai wasu Daraktocin guda biyu s**ayi ritaya Dr. Baffa Babba Dan'agundin yayi musu alkawarin cewar duk Daraktan da yayi ritaya daga aiki a ma'aikatar ta NPC zai bashi kyautar mota maimakon ayi musu Gwanjon wacce suke amfani da ita wanda ta gwamnati ce, kuma za'a iya wayar gari babu motocin da za'ayi aiki dasu a ma'aikatar wanda yin hakan ya saɓawa doka hakan tasa Dr. Baffa Babba Dan'agundin yayi alkawarin kyautar mots ga duk Daraktan da yayi ritaya a ma'aikatar kamar yadda kuke gani
1. Dr. Titilola Oshati da
2. Resomary Omoyeme
sunyi ritaya kuma yabasu kyautar mota kamar yadda yayi alkawari kuma yayi musu fatan Alheri.

Taron yasamu Hallartar Dr. Hashim Akko Wanda tsohon Babban Darakta ne na wannan ma'aikatar ta NPC da sauran manyan baki daban, kuma Alhamdulillahi kowa yatafi yana farin ciki tare da fatan Alheri.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
Wednesday 10 September 2025.

10/09/2025

"In ka lura cewa mutane sun zabi su yi maka mummunar fahimta da gangan to fita batunsu kawai ka ci gaba da harkokinka, don duk wani kokari da zaka yi na gamsar dasu karin bata lokaci ne kawai a kan wani abinda ba zai bada wani kyakkawan sakamako ba".

*Ya Allah ka dade mu da abokan kirki masu Amana Ameen*🙏🏻

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta NPC                Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundiYa naɗa Hon. Sagir ...
10/09/2025

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundi
Ya naɗa Hon. Sagir Soja Rano amatsayin mataimaki na musamman a harkar kungiyoyi a kananan Hukumomin Rano Kibiya da Bunkure wannan nadin ya biyo bayan irin gudunmawar da yake bayarwa dan cigaba tsarin kungiyoyi a wannan yankin.

Hon. Sagir Soja Congratulations

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
Tuesday 09 September 2025.

09/09/2025

"Jahili mara ilmi shike wulakanta mutane dan yana da wata damaa hannun sa, sakarai kuwa shike cusa kanshi inda za,a wulakanta shi kawai dan zai samu wani abun, mu rike mutunchin mu bazamu wulakanta kowa ba amma muma karmu sake a wulakanta mu"

*Allah ka tsaremu ka tsare kimar mu Allahumma Ameen*🙏🏻

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa kuma Babban Daraktan yakin neman zaben Shugaban kasa mai kula da...
05/09/2025

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa kuma Babban Daraktan yakin neman zaben Shugaban kasa mai kula da kungiyoyi na Shiyyar arewa maso yamma
Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundi
Ya isa har jihar Katsina dan ziyarar dubiya ga Babban Mashawarcinsa a harkar kungiyoyi kuma mai taimakawa Gwamna jihar Katsina na musamman akan harkar kungiyoyi Hon. Aminu Funtuwa wanda yayi haɗarin mota har yagamu da karaya a kwanakin da s**a gabata.

Mai Girma DG muna godiya bisa nuna kulawa da kuma dubiya ta kafa da kafa da kajewa wannan dan uwa har jihar Katsina Allah yasaka maka da alheri
Amin

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
Friday 5 September 2025.

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta NPC                  Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundiYa jagoranci wani...
04/09/2025

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundi
Ya jagoranci wani zama na musamman da manyan Daraktatocinsa da Shuwagabannin sassa daban daban dake ma'aikatar dan tattauna Al'amuran ma'aikatar da kuma yadda ake gudanar da aikace aikace na yau da kullum kamar ya saba ako wanne lokaci.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
3rd September 2025.

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar ayyuka ta kasa NPC               Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundiyayin da yake j...
04/09/2025

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar ayyuka ta kasa NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan'agundi
yayin da yake jawabi a wajen taron Samar da jari da kayan Sana'a ga Al'ummar Nijeriya a gaban Ministan Kwadago da Nagartar Ayyuka na kasa.

Taron Wanda ya gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma an shirya shine domin kaddamar da Samar da jari da kayan koyon Sana'a ga al'ummar Kasa musamman masu kanan jari.

A nasa jawabin Babban Mininstan Kwadago da Nagartar Ayyukan ya yabawa Babban Daraktan na NPC Dr. Baffa Babba Dan'agundi bisa yadda yake kokari a harkokin siyasa da wajen tallafawa da koyar da sana'oi ga Al'ummar Kasa musamman a yankin arewa maso yamma da tarayyar ƙasa baki ɗaya,
Ministan kuma ja hankalin mahalarta taron da suyi koyi da shi wajen hidima ga masoya shugaban kasa.

Taron dai ya samu halattar manyan bakin da s**a hadar da Mininstan Ma'aikatar Kwadago Muhammadu Maigari Dingyadi da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, da Kuma Shugaban Kwamitin Kwadago na majalisar Dattijai Senator Sulaiman Nazif, da takwaransa na majalisar wakilai Hon. Adegboyega Adefarati.

Sauran sun hadar da Shugaban hukumar Samar da ayyukanyi ta kasa His Excellency Salis Agara da Babban Sakataren Ma'aikatar Kwadago ta kasa
Dr. Salihu A. Usman.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
4th September 2025.

Address

Birnin-Kebbi

Telephone

8135460004

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jannat Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share