11/08/2026
Ɗan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Tudun Wada, Sule Lawan Shuwaki, ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa PDP.
Kakakin majalisar dokokin Kano, Ismail Falgore, ne ya karanta wasiƙar murabus ɗin Shuwaki a zaman majalisar na ranar Litinin.
A cikin wasiƙar, Shuwaki ya ce ya yanke shawarar barin APC ne bayan “nazari mai zurfi da shawarwari” da ya gudanar da abokan siyasarsa, magoya bayansa da iyalansa.
Ya kuma gode wa shugabannin APC daga matakin mazaba zuwa na ƙasa kan damar da s**a ba shi da goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikin jam’iyyar.
Sai dai ya ce ya zaɓi wata sabuwar hanyar siyasa da ta dace da ƙa’idoji da ra’ayinsa.
Bayan karanta wasiƙar, Kakakin majalisar ya tambayi Shuwaki ko shi da kansa ne ya gabatar da wasiƙar, inda ɗan majalisar ya tabbatar da hakan tare da bayyana cewa ya koma PDP tun watanni da s**a gabata, sai dai shawarwari na siyasa s**a jinkirta sanar da hakan a hukumance.