06/08/2025
Gwamnan Jihar Kebbi ya baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ƙauran Gwandu Football Club kyautar Naira miliyan ashirin (₦20m) bayan da s**ayi nasarar lashe wata gasa da aka gudanar a jihar;
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Maigirma Gwamnan Jahar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ƙauran Gwandu Football Club kyautar kuɗi Naira miliyan ashirin (₦20m) bayan da s**a lashe wata gasa da aka shirya a jihar ta Kebbi.
Gwamnan yayi musu wannan kyautar ne bisa hazaƙar da s**a nuna wajen lashe gasar a akai-akai ta Birnin Kebbi Youths Soccer League.
Ƙungiyar ta Ƙauran Gwandu Football Club ce ta lashe wannan gasar ta Birnin Kebbi Youths Soccer League a gasar ta shekarar 2023/2024 da kuma ta wannan shekarar ta 2024/2025 a jere.
Gwamnan ya baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafar wannan kuɗin ne a lokacin da ƴaƴan kungiyar karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar Abubakar Sadiq (Bullet) s**a gabatar masa da kofin da s**a lashe na gasar a fadar Gwamnatin Jihar dake cikin garin Birnin Kebbi ranar lahadi 3/8/2025.
Da yake jawabi, Maigirma Gwamna ya jinjinawa ƴan wasar da kuma shugabannin kungiyar bisa hazaƙar da s**a nuna.
Gwamnan ya kuma bayyana cewar yana alfahari da wannan kungiyar kwallon kafar saboda tun kafin ya shiga siyasa ko ya zamo Gwamnan Jihar Kebbi aka kafa wannan kungiyar da sunansa.
Gwamnan ya bayyana cewar tun a wancan lokacin yake ɗaukar nauyin kungiyar, saboda haka wannan kungiyar kwallon kafar tashi ce bata Gwamnati ba.
Gwamnan ya jinjina musu inda yayi kira garesu dasu ƙara ƙoƙari da himma wajen samun nasara a wasu wasanni harma a wajen Jihar Kebbi.
Gwamnan ya kuma bayyana irin muhimmancin da wasannin motsa jiki suke dashi ga lafiyar al'umma maza da mata da kuma tattalin arzikin al'umma.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cigaba da baiwa kungiyar dukkanin gudummawar da take bukata domin ƙarin samun nasara.
Gwamnan ya bayyana cewar, kowace gasa, akwai nasara da rashin nasara, inda yayi kira a garesu dasu tabbatar koda basuyi nasara a wasa ba, to abokan karawarsu, su tabbatar su ba kanwar lasa bane.
Daga karshr Gwamnan ya baiwa ƙungiyar da ƴan wasar kungiyar gudunmawar kuɗi Naira miliyan ashirin (₦20m) domin kara musu kwazo da himma.
Shima shugaban ƙungiyar, Abubakar Sadiq (Bullet) da yake gabatar da kofin ga Maigirma Gwamna, ya bayyanawa Maigirma Gwamna cewar kungiyar tayi nasarar lashe kofin a shekaru biyu a jere inda kuma yanzu kungiyar tayi nasarar lashe wasan karshe ta kofin Dutsinmari Cup Competition.
Haka kuma ya bayyanawa Maigirma Gwamna cewar shugabanni da ƴan wasar kungiyar suna godiya bisa irin gudunmawa da tallafin da yake basu da kuma ita kungiyar kanta.
Haka kuma ya ƙara da cewar babban maƙasudin zuwan su a yau shine gabatar da kofin da s**ayi nasarar lashewa a gasar da aka saka ta Birnin Kebbi Youths Soccer League da kuma godiya akan irin gudunmawa da tallafin da Maigirma Gwamna yake baiwa kungiyar.
Shugaban ƴan wasan kungiyar ne ya gabatar da kofin ga Maigirma Gwamna kuma yasa masa kambun nasarar kungiyar
Signed Ahmed Idris