10/08/2026
Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa Ya Iso Najeriya Domin Babban Taron Ƙasa da Ƙasa Kan Tsaron Ƙasa da Dorewar Ci gaban Al’umma.
Mai Girma Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa, Babban Sakatare na Ƙungiyar Muslim World League, (RABIDA) ya iso Najeriya domin halartar Taron Ƙasa da Ƙasa kan Tsaron Ƙasa domin Dorewar Ci gaban Tattalin Arziki da Zamantakewa (International Conference for National Security for Sustainable Socio-Economic Development), wanda Ƙungiyar Muslim World League (RABIDA) tare da JIBWIS Nigeria s**a shirya.
Za a gudanar da babban taron gobe Talata, 11 ga Agusta 2026, a Abuja, inda za a tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi ƙalubalen tsaron Najeriya, da kuma muhimmancin samar da zaman lafiya da tsaro domin samun ɗorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
An tarbi Mai Girma Sheikh Dr. Muhammad Bin Abdulkarim Al-Issa a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda tawagar Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, Shugaban JIBWIS Nigeria, tare da sauran manyan baki s**a tarbe shi.
Ana sa ran taron zai haɗa manyan malamai, wakilan gwamnati, masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro, masana da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, tare da bunƙasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ɗorewa a Najeriya.
Jibwis Nigeria