Bn Ali

Directions

Bn Ali Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bn Ali, Broadcasting & media production company, Ubix, Biu.

A 2023 Haka El-Rufai yace:"Babu wani dattijo a Arewa, kuma mu gwamnonin Arewa mun lashi takobi sai Asiwaju Bola Ahmed Ti...
12/06/2026

A 2023 Haka El-Rufai yace:

"Babu wani dattijo a Arewa, kuma mu gwamnonin Arewa mun lashi takobi sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya"

Yau gashi burin El-Rufai ya cika, amma kuma bala’in da ya biyo bayan burin ya zama silar tauye mishi dukkanin yanci da hakkokin shi na ďan adam (Babu girma, babu samu).

Muna kara tunatar da shugabannin mu na Arewa cewar al’umma da cancanta ya k**ata ku goyawa baya domin samun gyara, ba cikar buri da bukatun ku na siyasa ba.

Allah ka gyara muna Najeriya.

A.M Jariri, Esq.A 2023 Haka El-Rufai yace:

"Babu wani dattijo a Arewa, kuma mu gwamnonin Arewa mun lashi takobi sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya"

Yau gashi burin El-Rufai ya cika, amma kuma bala’in da ya biyo bayan burin ya zama silar tauye mishi dukkanin yanci da hakkokin shi na ďan adam (Babu girma, babu samu).

Muna kara tunatar da shugabannin mu na Arewa cewar al’umma da cancanta ya k**ata ku goyawa baya domin samun gyara, ba cikar buri da bukatun ku na siyasa ba.

Allah ka gyara muna Najeriya.

copied ✍️ A.M Jariri, Esq.

07/12/2025

Biu, Nigeria
BiuBiu
Why Biu Borno State Nepa

07/12/2025

Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Arsenal Mohamed Elneny ya gabatar da ibadar umarah a ƙasar Saudiyya mai tsarki. Allah ya ƙara wa Annabi daraja

Ilimi kogi ne!Me yasa naman alade ya zama  haramun a MUSULUNCI?•Alade ya ce: ina cin ‘ya’yana idan sun kasance raunana k...
11/02/2025

Ilimi kogi ne!

Me yasa naman alade ya zama haramun a MUSULUNCI?

•Alade ya ce: ina cin ‘ya’yana idan sun kasance raunana ko suna dauke da cuta.
• Ina cin najasata.
• Ina cin gawar mutum, kare, beraye, da duk abin da aka ambata.
• Ni jakar shara ce mai kafa hudu.
• Ina da tsarin narkar da abinci mafi rauni da aka sani a cikin dabbobi.
• ALLAH ya gargaɗe ku kada ku ci ni ko ma ku taɓa gawata, don haka nama na ya haramta.
• Ina cin macizai masu guba, kuma sukan harbe ni, amma ba sa cutar da ni saboda gubarsu tana shiga cikin kitsena kai tsaye.
• haka kuma ana renona a cikin keji a masana'antun zamani, wanda hakan ke jefa ni cikin damuwa har ya kan sa ni hauka.
• Ina kokarin falla ko tauna sandunan kejin da ake tsare ni har sai fuskata ta zama jini.
• Ina fatan kun san cewa tsutsotsi da cututtuka da ke cikin namana suna da ƙarfi sosai, ta yadda da wuya a kashe su gaba ɗaya yayin da ake dafa ni.
• Idan an gama dafa ni k**ar yadda ake dafa naman da aka yarda a ci, to babu wani sinadarin gina jiki da ke ragewa a jikina.
• Idan har yanzu ba ku gane cewa Mahaliccinku bai halicce ni don ku ci ni ba, to ku sani cewa mutum shi ne abin da nake ci!
Allah ubangiji ka cinyar da mu daga halattaccen abinci.🙏

Zaka iya haɗiye Capsule endoscope daga bakin ka zuwa cikin ka?--Capsule endoscope wata na'aura ce yar ƙarama mai ɗauke d...
27/01/2025

Zaka iya haɗiye Capsule endoscope daga bakin ka zuwa cikin ka?

--Capsule endoscope wata na'aura ce yar ƙarama mai ɗauke da camera tare da ƙaramin hardisk da take ɗaukar hoton ƙaramin hanji dake cikin ciki (gastrointestinal).

--Likitoci suna amfani da ita ne idan anyi normal scanning an kasa ganin ainahin cutar dake cikin ƙaramin hanji, sai ayi amfani da wannan yar ƙaramar na'urar domin binciken me yake damun mutum, yadda abin yake za'a baka na'urar ka haɗiye, sai a ɗaura maka wata na'ura mai k**a da belt a ƙugun ka itace small recorder ɗin da zata dinga ajiye duk hotunan da na'urar camerar da ka haɗiye zata dinga ɗauka a cikin ƙaramin hanjin cikin ka.

--Zaka haɗiye wannan na'urar tun daga maƙogaron ka zuwa cikin ka, har ta shiga ƙaramin hanji tana ɗaukar hoto, sai ta ɗauki hoto sama da guda 1,000 akan hanya. Tana ɗaukar hoton tana turawa zuwa ga wannan belt ɗin da aka ɗaura maka, wanda kai tsaye daga wannan belt ɗin za'a iya ganin hotunan a cikin na'urar computer idan aka gama.

--Bayan na'urar ta gama aiko da hotunan wato bayan ta kammala aikinta, na'urar anyi designed nata ne daman akan da zaran ta gama turo hotunan zata bi hanyar da ake digesting na abinci domin ta fita daga jikin mutum, daganan a tsakanin kwana ɗaya zuwa kwana biyu zata wuce zuwa wurin da ake yin bayan gida, domin a fitar da ita a toilet.

--An ƙirƙiri na'urar ta yadda bazata cutar da ɗan'adam ko kaɗan ba dan ya haɗiye ta, kawai dai za'a iya samun matsalar stuck a cikin ciki ta yadda na'urar zata iya maƙalewa a wani wuri a cikin ƙaramin hanji taƙi wucewa, wanda dole sai anyi surgical removal, wato sai anyi tiyatar cirewa.

Shin zaka yarda ka haɗiye wannan na'urar a cikin ka?
Facebook
everyonefollowme

Abubuwa 15 Da Za Su Kankaro Maka Mutunci A Zamantakewarka Da Mutane:1- Idan ka kira mutum a waya sau ɗaya ko biyu, amma ...
18/01/2025

Abubuwa 15 Da Za Su Kankaro Maka Mutunci A Zamantakewarka Da Mutane:

1- Idan ka kira mutum a waya sau ɗaya ko biyu, amma bai ɗauka ba, kada ka sake kira, kuma ka kyautata masa zato, la'alla bai gani ba ne, ko kuma yana cikin yanayin da ba zai ɗauka waya ba, sai dai idan kana da tabbacin dalilin da ya sa bai ɗauka ba.

2- Ka mayar da kuɗi ko wani abu da ka ara, kada ka bari sai an tambaye ka.

3- Kada ka yi wa mutum tambaya da take da alaƙa da sirrin rayuwarsa, idan ma buƙatar hakan ta k**a, to ka fara da neman izininsa.

4- Idan abokinka ya biya muku kuɗin mota ko abinci ko wani abu, to ka yi ƙoƙari ka biya muku na gaba.

5- Idan mutum yana magana kada ka katse shi, ka ba shi dama ya gama faɗin duka maganarsa koda ba ka yarda ba.

6- Idan ka yi wa mutum raha ko barkwanci, sai ka kula ba ya so, to kada ka sake, kuma ka nemi afuwarsa.

7- Idan mutum yana magana da kai, kada ka riƙa ba shi amsa alhali idonka na kan waya, zai ga ka raina shi.

8- Idan mutum ya gaya maka zai je asibiti, kada ka tambaye shi me zai je yi, ka yi masa addu'a kawai, idan yana son ka sani, zai gaya maka da kansa ba sai ka tambaye shi.

9- Kada ka riƙa saurin ba da shawara idan ba a nema daga gare ka ba.

10- Idan ka sanya glass mai duhu, to ka cire shi idan kana magana da wani.

11- Idan mutum ya ba ka wayarsa domin ka ga photo ko video ko wani abu, to kada ka yi scrolling gaba ko baya, don ba ka sani ba ko sirrinsa ne a wajen.

12- Idan ka fahimci ba a so ka ji magana, to koda ka ji, ka yi k**ar ba ka ji ba.

13- Idan mutum ya yi kuskure a gabanka, sai ya yi sauri ya gyara, to ka yi k**ar ba ka fahimci ya yi kuskuren ba.

14- Idan mutum ya ɗauki nauyin biya maka kuɗin abinci ko wani abu, kada ka ɗauki mai tsada sosai.

15- Idan mutum ya rubuta abin da ya burge ko ya amfanar da kai, amma ba ka yaba masa ba, to idan ya rubuta wanda bai burge ka ba, kada ka soke shi, hakan ƙaranta ne.
15/01/2025
✍️Abdul Bn Ali

Idan kana amfani da layin Airtel ka danna *996 # bayan ya bude zai baka options sai ka danna number 3 inda aka rubuta "V...
18/01/2025

Idan kana amfani da layin Airtel ka danna *996 # bayan ya bude zai baka options sai ka danna number 3 inda aka rubuta "View Linked Number(s)" kana dannawa zaka ga list na numbers da akayi linking NIN dinka dasu sai ka duba shin kasan lambobin domin sanin masu lambobin yanada fa'ida sosai, domin kuwa wanda akayi linking NIN dinka da lambarsa duk laifin da zai aikata da layin nashi to idan aka tashi k**ashi ta amfani da NIN kai za'a kamo tunda da NIN dinka akayi linking, idan bakan masu lambobin ba sai kayi kokari ka cire su saboda tsaro.

Idan MTN kake amfani dashi shima dai sai ka danna *996 # zai baka options sai ka zabi wurin da aka rubuta "View NIN Status" zai sake baka options sai ka zabi "View Numbers Linked To NIN" nan take zasuyi maka message na lambobin da akayi linking da NIN dinka.

Screenshort muga naka a comment.

Allah yasa mu dace.
Abdul Bn Ali
MTN Nigeria
Airtel Nigeria

Charlie Chaplin lived 88 years and left us with four profound statements:1. Nothing is forever in this world, not even o...
09/01/2025

Charlie Chaplin lived 88 years and left us with four profound statements:

1. Nothing is forever in this world, not even our problems.

2. I love walking in the rain because no one can see my tears.

3. The most lost day in life is the day we don't laugh.

4. Six best doctors in the world:

• The sun

• Rest

• Exercise

• Diet

• Self-respect

• Friends

STICK TO THEM AT ALL STAGES OF YOUR LIFE AND ENJOY A HEALTHY LIFE.

If you see the moon, you will see beauty.

If you see the sun, you will see strength.

If you see a mirror, you will see the finest creation. So believe it.

We are all tourists, and life has already mapped out our routes, bookings, and destinations. Trust the journey and enjoy every moment.

Life is just a journey! Therefore, live today—tomorrow may not be.

Address

Ubix
Biu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bn Ali posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share