Jafar sa'ad

Jafar sa'ad alhamdulillah ala kulli halin

writer........✏✏✏

📝📝📝📝📝
📚📚📚📚
📖📖📖
WhatsApp number 👉09124400024
(6)

Aure dole......Part...... 1.............™"Dasauri ta fanno da gudu ta nufi RumfarMalam,Yana ganinta Yana ganinta yacekin...
18/12/2025

Aure dole......

Part...... 1......
.......™"Dasauri ta fanno da gudu ta nufi Rumfar
Malam,Yana ganinta Yana ganinta yace
kinyi tsi yar gidan Malam bakyajin
magana.
" Tace Malam cu habu ne yake dukana
Waina fita babu ando,kunsan dai
maganar yara bakinsu Akwai tsami Kuma
wai 'Nashiga dakinsu Nadauki wayanshi
Nayi Game shine yabugeni.
"Ai Malam idan akwai abinda yatsana bai
Wuce Adaki Dijaba Acewarshi baisaka
Sunan 'Uwarshi don adaketaba.
" Yariko Hannunta yace zo mushiga Yau
sauna bigeshi Kar ku dauka dukan wasa
dukan Kato.
"Yana shigowa Yasamu Inna Uwargida
Yacimata Mutunci Kuma Yace taja wa
danta kunne kada yakara dukar Masa
Uwa.Shiru Inna Uwargida tayi Tana
mamakin Hali irin na Malam indai kana
son kaga bacinran Malam kadaki Dije'Ta
tabe baki tawuce tana gunguni tana cewa
Yarinya daga ita har Uwarta basa laifi
Mtse tayi tsaki Tashige dakinta.
**********
" Wa cece Dije,Sunan yadauko Asaline
daga Sunan Mahaifiyar Malam,Malam
Yanada Yaya goma sha shidda,Wanda
Duk Mazane 'Dije ce kawai Mace Wacce
Amaryar shi Aishatu Wadda Suke kira Da
Indo, Kuma'Dije ce kadai Yarta, Ayanzu
"Dije tanada shekara Goma Aduniya
Wanda ko kai Idan Kaga tabarar datakeyi
saika Rike Baki.
" Sannan Tanada Wata Halitta Mai Kyau
Da tsari,'Dije dai farace tas Ga dogon
hanci siriri gabakinta Dan karamai ga ta
da gashi Irin na fulanin Asali.gata yar
duma duma komai cas cas k**ar
andasa mata Sannan duk yawan gashinta
sai Malam yazauna Akeyinshi.
"Sannan yana matukar Son mahaifiyar
Wanda son dayakeyiwa Mahaifiyarta ne
yadawo kanta.'Saidai duk son dayakeyiwa
Indo ita ko kadan bata Sonshi,Tunda Aka
haifi Indo Kulawar 'Dije tadawo Hannun
Malam Don cewa tayi bazata shayar da
itaba,Haka Malam Ya tattara Indo takoma
Dakin Inna Uwargida Mata mai hakuri Da
juriya duk suru tunda Malam Zaiyi badai
Tadaga ido ta kalleshiba Saboda
Hakurinta Da juriya,
'Ita Inna Uwargida tanada Yaya Tara Duk
Maza Sai Haule Mai 'Yaya Shidda Itace
Ta tsakiyar,Sai Indo Amarya Ita Kuma
daya, Itace " Dije Uwar Yan Rigima,"Malam Mahaifin Dije Asalinshi Ba
fullatanine Dan Asalin Jihar
Adamawa,Anan Aka Haifeshi Yagirma
Wanda tun Yana karami Mahaifansa S**a
mutu.sai Rokonshi Yadawo Hannun
Mahaifin Indo Mahaifiyar Dija.Mahaifin
Indo Aminin Mahaifin Malam ne.'Malam Hamisu Dan Borno Shine
Cikakken Sunan Mahaifin 'Indo.Mahaifin
"Indo Matanshi Hudu' Uwargida Itace
Surbajo Mahaifiyar Indo, Tanada Yaya
Goma "Indo ce Kawai Mace,Sai Falmata
Itace Ta biyu Ita Yar 'Uwar Malam Hamisu
ce Sunkasance 'Yan Maiduguri Borno
State.
"Sai Habiba Ita Yar Adamawace Yayanta
Tara,Duk Mata "Sai Halima Mai "Yaya
Shidda Ita Ma yar Adamawa ce.
" Malam Hamisu Mahaifin Indo Shine Ya
karbi Abubakar Alokacinda Mahaifinshi
Yarasu.Wanda Yakasance Amininshi
Sosai.Abubakar tunda Yataso Saida Yayi
Shekara Goma Sha Biyar Sannan Aka
Haifi 'Indo Yanansonta Tun tana
Karama,Alokacin Kuma Yayi Saukar
Alqur'Ani Mai girma.
"Sanda Yakai Shekara Ashirin'Alokacin
Indo Shekararta Biyar Kuma 'Alokacin
Wani Abokin "Malam Harisu Maisuna
Jabbama Yayi Sha'awar Hada Yarsa Da
Abubakar.
" Malam Hamisu Yasan Asalin Jabbama
Mutunne Mai Hakuri Da dattaku
Sosai.Gashi Da Kyauta 'Shiyyasa Ma Da
Ya Tuntubi "Malam Harisu Da Maganar
Ya Yadda Akancewa Zai Kebe Da
Abubakar Din Yaji Ta Bakishi.Haka Kuwa
Akayi Sanda Ya nemeshi Da Maganar Ya
Amince Batareda Yace Komai Ba Saboda
Yanajin Kunyar Malam, Dan ko Kashi Yau
Malam Yace Zai Hadashi Dashi Baijin
Komai Don 'Yafi Karfin Haka
Awajenshi.Babu Bata lokaci akayi Aure.Ta
tare.
" Malam Abubakar Shima Yazama
Babban Mutun 'Inda Haryanzu "Indo Tana
cikin Ranshi. Ya Kara Aure Don
Uwargidanshi Tazo Masa Da Cewa
Kawarta Hadiza Batada Miji Kuma Dan
Allah Ya Aureta. Ta Nada kirki Don
Alokacinda Tahaifi "Mustafa Shine Danta
Nafari.Ita ke zuwa ta taya ta Aiki da
komai.Shiyyasa Take Ganin
Mutuncinta'Malam Da farko Bai
Aminceba Daga Baya "Ya Saboda Ya
Matar Tashi Ta shiga Damuwa.Bayan
Anyi Aurensu Ta Haifi Danta Namiji
Hakilu,Nanfa Hadiza Tazage Tana Yiwa
Kawar Tata Rashin Mutunci Tawa Uwa Da
Uba.
" Ita Kuwa duk Abinda Zatayi Mata Bata
Taba Kallonta Da Abinba.Hasalima Saidai
Tayi Murmushi'Ana Hakane "Indo Ta
Zama Budurwa Ayanzu Tanada Shekara
Shadaya Daidai. "Malam Kuwa Yana ta
Jiran "Indo Tagirma Dan Yanzu Har
mafarkinta Yakeyi. Yana Sunbatu
Uwargidanshi Kuwa Kuwa Kullum Yakanyi
Mafarkinta Adakinta,Yanacewa Wayyo
"Indo Kisoni Inbaki Soniba Zan mutu
Abindai Yakai Malam Kamar Zaiyi
Hauka.Hadiza Kuwa " Tace Saidai
Yamutu don Wallahi Babu Abinda
Yashafeni.Uwargida Kuwa Hankalinta
Yatashi Sosai Matuka,Babu Bata Lokaci
Tafadawa "Malam Hamisu halinda Mijinta
Yake ciki.Babu Bata lokaci yazo don
ganin jikin Nashi Yadda Yake.Ko da yazo
Kuwa Alokacin Yana sunbatu 'Yana cewa
Wayyo Allah Na "Indo ina sonki kisoni
Dan Allah,Malam Cikin Dattaku "Yace
Abubakar Meyayi Zafi hakane Malam Ya
tsugunna Yaringa Yimishi Addu'O'i Amma
k**ar Ana turaashi.
" Malam zuwa Yanzu Yagane me
"Abubakar Yake nufi Wato Yada de Yana
son " Indo Yarshi Ya jin jina kai Bayan
yaga yadda Abubakar yasamu bacci.
'Bayan ya Isa Gida yasamu Surbajo

Mezanyi da ita.......Part....... 9...................©®hotel ne by morning insha Allah zan bi flight nataho and make sur...
18/12/2025

Mezanyi da ita.......

Part....... 9.......
............©®hotel ne by morning insha Allah zan bi flight na
taho and make sure kuna zuwa ka kira car wash
su d’au motar nan every thing na cikinta ya
zama clean.” Ammar ya kar’bi key had’e da
bud’e driver seat momma ta waro ido tace “
yana ina shi “ Ammar yaja numfashi don yasan
fad’an momma shi kuma yana son d’an uwansa
baya son’bacin ransa “ Momma zai zo ya tuna
akwai yana da abinda zaiyi a bauchi “. Gani yayi
kawai momman ta fita ware ido tayi tana kallon
imran jingine jikin bishiyar’kofar gidan kallo da
take masa ne yasa shi rusinar da idanunsa baya
jurewa sun saba tun suna yara da idon take
hukunta su, hanya kawai ta
nuna masa ta shige. Ransa a ‘bace ya bita
tabbas ya san dai kafin ya isa gida wani ciwon
sai ya k**ashi.
Shima Ammar d’in kallo d’aya tayi masa ya fito
ya koma d’aya seat d’in zuciyarsa fal da tausayin
d’an uwansa don ya san kam yau sai ta Allah.
A salu’be ya tada motar bayan yayi adduar tafiya
ﺍﻟﺤﻤﺪﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺳﺨﺮ ﻟﻨﺎ ... zuwa Karshe ya kuma ware
a .c don ya kore masa warin jikinta da dum da
motar tayi har da su fess turaruka. Momma tana
kallonsa tana’bata rai cikin’kyamar banzar
d’abi’arsa. Shatu kuwa kwafa tayi don sarai ta
san ma’anarsa ta hakan wato kyamarta ma yake
yi ai kuwa za tayi maganinsa kafin ta bar motar,
ba mamaki ma bayan fitsari har kashi sai tayi a
motar....😂😂.
Wani irin gudu yake shararawa duk a tsorace
suke a motar ganin yarda yake mommah kuwa
ta’ki magana sai addu’a da take a zuciyarta.
Shatu kwance take luf a cinyar mommah wani
barci ne yake fusgarta, cikin hukuncin ubangiji
kuwa cikinta ya fara murd’awa ta daddage ta
saki wata tusa da ta d’umame motar gaba d’aya
Allah ne ya kiyaye saura’kiris ya saki sitiyarin
motar yaja wani wawan burki, ammar ya
dinga’kok’arin’kinshe dariyar da ke cikinsa amma
ina sai da ta bayyana a guje ya fice tuni ya fara
kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana
aikin jera masa sannu. Momma kuwa duk da
tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu saisai
dariya take yi tana’karawa momma tace “ wallahi
shatu idan ya k**aki ba ruwana “ “ yo mommah
ba k’yamata yake ba saura gudawa ma “
Mommah ta waro ido “ kada ki fara shatu idan
ba so k**e ya kashemu a t**i ba kina ganin
wawan burkin da ya sha Ba don Allah ya kiyaye
Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu.”
Shatu ta zaro ido “ momma mutuwa kuma a
yanzun da zan fara jin dad’in rayuwa aradu ma ki
daina wagga zance yo tunda nake ban ta’ba
tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta’ ba
ganinsa ba sai yau amalanke muke shiga
garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya
Na shigo aradu dana shiga nan na zata aljannah
nake “ mommah ta girgiza kai “To kada ki sake
abinda zai zubar damu a t**i motoci su take mu
mutu.” Ta d’aga kai. Ya huta sosai kafin yace “
Ammar jeka Kai bud’e glasses d’in motar
ventilation ya shiga ka fesa air freshners tabbas
Ba mamaki mommah ta d’auko ajalina “ Ammar
ya d’an shafa bayansa “ bros ba zaka mutu ba
just because of her sai kwananka ya ‘kare Ka
dinga daurewa pls mommah bata jin dad’i the
way she looked at you ka dinga controlling
temper Dinka” hannu ya d’aga masa “ jeka kayi
abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi
muna zuwa gida I will pack everything nawa na
tare “ Ammar ya zaro ido “ saura fa 4 months
bikin ya zaka tare yanzu “ Imran tsaki yayi idan
ban tare ba so kake na mutu ko?” Ammar ya
juya yana’kunshe dariyarsa ya gama duk abinda
ya sashi sannan ya dawo yana kallon yarda yake
mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman “
Bros mu tafi kada dare yayi “ mikewa kawai yayi
ya mi’ka masa key d’in “ muje kayi driving I can’t
do it “
Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta
saki baki sai barci take har da munshari ya sauke
duk glasses d’in iska Na shiga motar a zuciyarsa
yace “ Gwara a tafi haka “ momma dake
kallonsa ta ta’be baki “ zan baka mamaki imran
kada Ka shiga hankalinka “.

Takun saka.......Part....... 10................©®Ciki yay batare daya amsa matabayana jan tsaki. Hibbah ta bisa da kallo...
18/12/2025

Takun saka.......

Part....... 10.......
.........©®Ciki yay batare daya amsa mataba
yana jan tsaki. Hibbah ta bisa da kallo
wasu hawaye masu zafi na sakko mata
bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Ido s**a haɗa
da Yah Usman. Ya girgiza mata kansa
alamar kar tai kuka. Dan tun tsawar da
Abban yay mata duk hankalinsu ya dawo
kansu.
Suma koda s**a gaishesa bai amsa
musu ba. Sai faman mazurai yakeyi. Basu
sakebi takansaba duk s**a kwashi
kayayyakinsu sunama Ummi sai sun dawo.
Itako amsa musu take da fara'a tamkar
batasan da zaman Abban a wajenba ma.
Yah Muhammad ne ya k**a hannun
Hibbah da ko motsi ta kasayi har yanzun.
Sai da s**azo har wajen motarsa yasa
handkerchief ya share mata hawayenta
batare daya ce komaiba. Sauran ƴan
uwansa ma kuma bai basu damar cewa
komai ɗin ba. Sai umarnin yin addu'ar fita
gida k**ar yanda s**a saba yay musu.
Suna kammalawa kowa ya hau abin
hawansa. Yah Muhammad da Hibbah.
Abubakar ya ɗauka Usman da Umar a
motarsa dansu basu da mota har yanzu
sai mashina. Ammar ma ya hau mashin
ɗinsa lifan shi kaɗai tunda yau Hibbah tabi
babban yaya......................Ƙoƙarin kauda fuskarta taketa
faman yi saboda kar Yah Muhammad ya
ga hawayen dake guje-gujen sakko mata
akan fuska tun bayan barowarsu gida. Sai
dai kuma abinda bata sani ba tuni ya
fahimci kuka takeyi, yadai mata shiru ne
domin bata damar rage nauyin zuciyarta.
Sai da ya ɗauka t**in da zai kaisu har
makarantar tasu sannan yay gyaran murya
batare da ya kalleta ba. Shiru Hibbah bata
motsa ba saboda zurfi da tai a tunani....
“Auta!”
Ya kira sunanta cike da kulawa. Nanma
shiru babu alamar ta jisa. Leɓensa yaɗan
ciza na ƙasa yana gangarawa gefen t**i.
Harya kashe motar gaba ɗaya ya juya
yana kallonta batasan mi yakeyi ba. Cikin
damuwar data bayyana sosai akan
fuskarsa ya ce, “Muhibbat!!”.
A firgice ta juyo garesa tana sauke
wata irin nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma
tai saurin kai hannunta akan fuskarta ta
shiga share hawayenta tana ƙaƙalo
murmushi. “Lah Yaya banjikaba ALLAH.
Ina can wajen kallon hanya har idanuna na
hawaye dan ƙauyanci”.Murmushin da bai niyyar yi baneba ya
suɓuce masa. A ransa yanajin ƙaunar ƴar
ƙanwar tasu da yaba halinta na manya.
Duk da rawan kanta da tsiwa ita ɗin
yarinyace data san yak**ata. Tana da
wasu nagartattun halaye da sai ka nutsu
gareta kake iya ganosu. Amma a kallo
ɗaya zaka iya dangantata da yarinya mai
rawar kai da shirme. Ya ɗanja numfashi
yana furzarwa a hankali tare da kafeta da
idanunsa irin nata.
“Mi k**e tunani Muhibbat!?”.
A yanda yay maganar babu wasa a cikinta
ne ya sata ɗago idanunta dake ƙoƙarin
tara ƙwalla ta dubesa. Sai kuma tai saurin
girgiza kanta tana ƙoƙarin maida kukan
dake son ƙwace mata.
“Ba bu komai Yayah”.
Ta faɗa muryarta na rawa.
Sosai ya sake kafeta da idanunsa
dake canja kala zuwa ɓacin rai. Sai dai
kuma cikin tausasa murya ya ce, “Kin dai
san banason ƙarya ko?”.
Kanta ta jinjina masa hawayen da
taketa ƙoƙarin makalewa s**a gangaro a
hankali bisa fuskarta.... “Yaya! Abba ne,
miyasa baya sonmu? Musamman ma ni ya
tsaneni bayason ganina”.
Takai ƙarshen maganar tata da
fashewa da wani irin kuka mai cin rai ga
ma'abocin saurare. Idanunsa ya lumshe a
hankali tare da cije leɓensa na ƙasa da
ƙarfi. Addu'a ya fara karantowa a
zuciyarsa domin samun dai-daito daga
fushi da fusatar damuwar ƴar uwar tasa.
Ya kamo hannunta cikin nashi ya rumtse
da ƙarfi.
Kamar jira take ta sake fashewa da
wani kukan, fuskarta ta kwantar akan
hannayen nasu dake cikin na juna,
hawayenta s**a shiga gangarowa har
akan fatar hannunsa data ɗora kanta a kai.
Cikin kuka ta cigaba da faɗin “Yaya
miyasa Ummi ta yarda ta auresa? Bayan
kuma tasan shi ɗin mugu ne. Miyasa bata
haƙura ta zauna damu mu kaɗai ba bayan
rasuwar Abbanmu?. Wlhy Yaya banason
Abba na tsanes.......”
“Muhibbat!”. Yay saurin katseta da ƴar
tsawa.
Ɗago kanta tai tana kalonsa, ganin yanda
ya ɗaure fuska ne ya sake sakata fashewa
da kukan.
Yaya miyasa bakwaso nace banason
Abba bayan shima baya son mu. Kullum
shike gusar da farin ciki a kan fuskokinku.
Duk randa yazo sashenmu sai Ummi tayi
kuka a ɓoye. Sannan fuskarta tana
kumbura k**ar wadda aka daka
Yayanmu”.
A matuƙar razane yake kallonta a
yanzun. Dan tabbas tun bas**ai hakaba
suke tambayar Ummi mike samunta a
fuska a maban-banta lokaci, amma sai
takan ce musu wani ciwo ne yake mata
haka akan fuska lokaci-lokaci, amma tana
shan magani. Sunsha damunta suje asibiti
amma sai taƙi yarda. Sai dai kuma yau
gashi ƙaramar ƙanwarsu tazo da wani batu
mai girma. Shin kodai da gaske ne da ake
cewa duk ƙanƙantar ɗiya mace tafi ɗa
namiji lura da maida hankali akan abu.......
“Yayanmu dan ALLAH kasa mubar
musu gidansu mu koma can wani gari da
zama mu daina ganinsu suma su daina
ganinmu.”
Hibbah ta katse masa tunani ta hanyar
girgizasa tana kuka da roƙonsa.
“Tanee! kinga nutsu muyi magana.
Maza share hawayenki na tambayeki”.
Da sauri ta shiga share hawayenta da
handkerchief ɗinsa. Duk da wasu nabin
wasu hakan bai hanata faɗin, “Yaya na
goge”.
“Auta kin taɓa ganin wani ya daki
Ummi ne?”.
Kanta ta girgiza masa.

Uwar miji......Part....... 26...............©®Daga murya yayi yana kiran Falalu yana Fadin”Kazo gahajiya tadawo”hayaniya...
18/12/2025

Uwar miji......

Part....... 26.....
..........©®Daga murya yayi yana kiran Falalu yana Fadin”Kazo ga
hajiya tadawo”hayaniyar shiya fito dasu karime daga ciki
suma cikin murna s**a yamaimayeta suna mata sannu da
jiki,har daki s**a rakata su karime Mu”azzam ne ya Umarce
su dasu dafamata wani abu taci,bayan tasha mgani tayi
salollinta sai ta kwanta,cikin rawan jiki S**a fice suna matan
fatan samu lafiya
Sai da Ummi ta rama sallolinta kana taci abimci Tasha mgani
Awaya Mu”azzam yahadata da hajiya tana mata barka da
sauka gaisawa s**ayi sama sama kafin suyi sallama domin
kowannensu na bukatar Hutu.
Mu”azzam dakansa ya taimak**a Ummi tayi brush yarikota
har bisa gadonta ya kwantar da ita..Tare s**ayi addu”ar
kwanciya barcin kafin su shafa tare..dakinsa yatafi yayi shirin
barcinsa cikin kayan barcinsa Pjm ash colour da blanket
dinsa yazo nan kasa kan capet din dake dakin ya kwanta
yana kallon Ummi wanda ya barci yayi awon gaba da
ita..Mirmishi yayi yana Fadin”Ummi na kenan,Allah ya
barminke”Shima dai cikin lokaci barcin yayi awon gaba
dashi.
•°•°•°•°•°•°°•°•°•
MAID
Shirye shirye fa na cigaba da kamk**a A bagaren Su
bukar da yakura kota kowani fanni an shirya ma Abun,bukar
akwati guda yayi ma Zahirah na Fitar biki bayan uban kayan
dakin dayayi mata yan Dubai.
Itakuwa Zahirah cikin lokaci tachanza fatarta tayi sulbi
saboda yadda yakura ta dage babu wasa,fuskarta tayi fayau
tana Fitar da Annuri,Ko”ina ta gifta wani kamshi ne mai tsaya
azuciyar wanda yashakeshi ke binta duk inda tagifta..koda
bikin ya rage saura kwana uku An rigaya an mata kitsonta na
bare bari,yan kanakana yariyari 2step an zubomata shi har
baya,dayake ba laifi tana da suma,Ga kunshinta an zubamata
shima turbarkallah masha Allah.
Zahirah tafara tsarguwa da wannan Abubuwan da”ake
mata koda ta tambayi yakura sai dai tamata dariya
tace'”Diyata kenan ki kwantar da hankali abun alheri ne zai
sameki Matsayinki ne zai karu kinji karki damu”Ko kwalliyan
ne baki so adaina miki”Jin haka yasa ta girgiza kai tanatana
dariya.
Baffa shettima yakasa boye jin dadinsa godiya kuwa
yazubama Bukar ba adadi..game dako gayama zahirah yace
sai an daura auren In mijinta yazo tafiya da ita,zai fadamata
( Kai dai Shettima kacika son kanka da yawa yasin).Ranar alhamis Hajiya Baraka ta iso ita da matar Shureim
Zulaika tare shi Shureim din,wanda agobe zasu bi jirgi zuwa
Maiduguri daura Aure..Ummi babu wanda tafadamawa to
dawa ma take hurda zuwan hajiya yasa tama su karime
mgana kan Suyi shirye shiryen abinci gobe nasu dana bakin
maiduguri..
Sunji mamaki da Hajiya baraka ke fada musu gobene
yallabai zaiyi aure”Abunda basu taba ji ba Ummi kuwa kauda
kai tayi ranta na mata kuna,hakuri hajiya ta basu tare da
cewa abun yazo agurgujene,shiyasa basu ji ba.
Abangaren mu”azzam ko baida wani shiri Brr.Barau kawai
yafadamawa,sai Dr.Abduljabar,Shureim kuwa yazo da abokin
aikinsa Dr.Haruna kurfi,Su kadai ne zasu tafi maidugurin
gobe in Allah ya kaimu.
Ummi kuwa tayi bakan ko mganar bikin ake bata sanya
baki,shima mu”azzam din koda wasa bai taba kwatanta hirar
da ita ba,yana kiyayewa ammh duk wani motsinshi Tafin
Hannunta yake kar take kallonsa aransa tana ayyana
abubuwa dadama wanda nikaina ban sani ba.
RANAR DAURIN AURE
Rana bata karya saida Uwar diya taji kunya takowani
bangare shirye shirye,ne ke gudana tun ma bangaren su
Zahirah su abun da gaske suke don kuwa gida tuni ya cika
da yan”uwa da abokan arziki..Mahgana itama tana chan
danata gayyah ga kuma yakura wacce itace gayyah komai.
Zahirah tafara fahimtan wani abu domin Duk inda ta gifta
amarya ake cema gashi Yakura ta shiryata cikin wani ubansu
less bayan tanadeta da lifaya,.Ita kadai adaki tana tunani
domin ita tunda take bata taba yin kawa arayuwarta ba ita
kadai take rayuwarts..Duk wani shagali da sauri s**a farashi
domin Shettima yace Yakura su zama cikin shiri ana daura
aure mu”azzam zai wuce da matarsa.
Abangaren Su mu”azzam kuwa jirgin karfe goma zasu
shiga zuwa maid,shiyasa da wuri s**a kammallah shirunsu
suma anasu barayin sun safe su karime s**a tsabtace gida
s**a fada kichen domin hada hadan abinci Hajiya kuwa na
lura da ummi ko jiya batayi barci ba tarasa wannan bakar
zuciya irin na suhaima,yanzu ma tana kwance ko tashi batayi
ba gashi ita hartayi wanka zulaika ma ta cakare abunta
tashige cikinsu su lami suna aiki dayake sun santa babu
ruwanta.
goma Saura kadan Mu”azzam da Shureim s**a shigo dakin
Ummi wacce ke kwance cikin bargo hajiya na gefenta tana
mata fada kamshin daya bugi hancin tane yasata dagowa
luuu..Tayi da ido na ganin yadda mu”azzam yaci ado wata
ubansu gezner brown ammh light riga da wando yar
ciki,harda malummalum kansa dauke da wular zannah
bukar,kafafunsa kuma cikin booth suke bayan hannunsa
daure,da agogon azurfa mai kyau da kyalkyali yana daukan
ido.
Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri na dabam,anko s**ayi
domin shima Shureim irin shigan dake jikinsa kenan, domin
shiya yimusu Ankon., Ummi na ganin suna takowa gareta tayi
maza,ta maida kanta cikin blanket saboda kukan daya taho
mata.....

Tana tare dani___Part____285___________©®“A’a barshi karki damu, ya Anas yake?”“Yana bacci kema ya k**ata ki kwanta.”“A’...
18/12/2025

Tana tare dani___
Part____285____
_______©®“A’a barshi karki damu, ya Anas yake?”
“Yana bacci kema ya k**ata ki kwanta.”
“A’a nikam, se hankali a kwance ake iya bacci
ai.” D’an murmushi Fannah ta sakar mata “toh
ga Qur’ani ki karanta” ta miqa mata. “Nagode
kema kije ki huta wannan hawa da sauqan ze
dameki kinga already k’afafuki sun kumbura.”
“Toh Ummimi.”
“Nace yaushe ne jikan nawan ze fito?” D’an
dariya ta saki dan kunya ma takasa fad’a mata.
“Surikar tawa tana jin kunya na ne?” Ummimi tayi
teasing nata.
“Nanda wata uku in shaa Allah.”
“Ahh ashe ma kin kusa toh Allah raba lafiya ‘yata
Allah ya sauk’eki lafiya.”
“Ameen Ummimi nagode barinje in huta nima.”
“Yawwa ‘yata” ahaka s**a rabu beside Anas taje
ta kwanta alokacin har ya tashi. “Flower ina
kikaje?”
“Gun Ummimi.”
“Baraki koyi zama gu d’aya ba ko kinga
k’afafunki kuwa? Wai bakiya jin tausayin kanki
ne?”
“Habeebi please ya isa ai dama kumburin dole
ne kaide kace kanason min surutu ne saboda
gun Ummimi naje inda toilet nace na shiga ai
barakayi magana ba.”
“Ohkayyyy haka kika ce? Toh har mu isa
banason kisake sauk’a wajenta am not asking
you am ordering you as your husband.”
“Sekayi ai” tayi maganar k’asa k’asa.
“Kuma najiki nide na fad’a miki.” Baya ta juya
masa ba tare da tace komai ba haka tundaga
nan bata sake masa magana ba kodaya tasheta
Sallan Azahar haka La’asr ma shima be mata
magana ba.
10 hours ya d’aukesu sannan s**a iso Nigeria
inda s**a sauk’a a Sandralia Hotel Abuja har
anan Fannah bata sake ma Anas magana ba,
ruwa ta watsa taso shiga duban Ummimi amman
Anas ya hanata. Bayan ta shirya cikin kayan
baccinta ta zauna kan gado tana ma kanta tausa
a k’afafunta, fitowan Anas daga wanka kenan
singlet da nickers yasa ya hauro gadon yana
k’are mata kallo.
“Flower.” Shiru tayi bata tanka sa ba. Kusa da ita
ya matso “Flower bara kimin magana ba?”
Nanma shiru se massaging kumburarrun
k’afafunta take hannunta ya d’aga daga kan
k’afan nata nanma bata ce masa ko k’ala ba.
“Flower wai barakimin magana?” Nanma shiru.
“Okay I’m sorry kinji? I’m sorry.”
“Kasakemin hannu as you can see am
massaging my legs.”
“Flower I said I’m sorry.”
“Naji sakeni toh.”
“Bari zan miki.”
“Banaso zanyi abuna da kaina.”
“I’m sorry” ya sake hannun nata tare da k**a
kunnuwansa ko kallonsa batayi ba ta cigaba da
massaging k’afanta. “Flower please.”
“Wai hak’urin me kake bani? Nace kamin laifi
ne?”
“Baki fad’a ba amman nasan na miki laifi and I’m
sorry kije kisameta in kinaso.”
“Banaso” ta fad’a stubbornly.
“Yi hak’uri mana Mom Hanan” ya sake matsowa
kusa da ita closing the gab between them,
gashin kanta data barbaza a kafad’anta yahau
shafawa. “Yi hak’uri kinji barin sake ba.” Kallonta
ta miyar garesa “I’m sorry sweetheart” d’an
murmushi ta sakar masa ma’anan ta huce.
“Thats my woman!” Lips nata yasoma laluba
bata hanasa ba se dab da bakinsu ya kusa
had’iye tasa hannu ta k**a mai baki “no kisses
today thats your punishment” tayi maganar tare
da miqewa daga kan gadon ta sanya hijabinta.
“Oh common please Flower ko peck ne.”
“Nace NO! Gobe zaka sake repeating abinda
kayi yau.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin
Ummimi.
Some minutes later ta dawo har anan Anas beyi
bacci ba yana jiranta, a nitse ta cire hijabin ta
haye gado ta kwanta ganin bata matso kusa
dashi ba yasa ya matso dakansa tare da zama.
K’afanta ya miqar kan cinyansa sannan ya fara
mata massaging.
“Ta nan ka b’ullo kenan? Saboda in ka gama in
baka kiss as token of appreciation, uh-uh yau ba
kiss na fad’a maka smart guy, wannan logic
nakan bareyi aiki ba yau.” Dariya yaso yi
dankuwa ta k**asa amman seya matse.
“Ni ba haka nace miki ba am massaging your
legs because I love to”
“Humm! Allah sa de, nagode” bayan daya gama
yaja d’ayan ma yamata godiya ta masa sannan
ya kashe musu wutan ya koma ya kwanta
agefenta yana wasa da gashin kanta duk wani
salo nashi yayi applying amman Fannah tak’i bari
yayi kissing nata haka yatayi har ya gaji seda
tajishi yayi shiru sannan ta juyo tana kallon shi
unexpectedly tayi pecking nasa a lips. Kafin ta
d’ago kanta ya riqeta gagam yasoma sarrafata
haka s**ata romancing junansu har seda bacci
b’arawo yayi gaba dasu.

Aure kwangila____Part____194________©®Ummy kau cikin harde qaffafu ta Isaqasa, kitchen ta zarce don ahalinyanzu bata buq...
18/12/2025

Aure kwangila____
Part____194____
____©®Ummy kau cikin harde qaffafu ta Isa
qasa, kitchen ta zarce don ahalin
yanzu bata buqatar ta hadu da daya
daga cikinsu
Maid dinsu tajuyo ganin yadda
tafado kitchen din k**ar wanda
aka jefo
Hakan yasata fara tambayarta lfy
ganin yadda duk take a burkuce
Saurin saita kanta tayi tawani sha
murr cikin basarwa tace mata
bakomai ta tafi bari ta ida breakfast
din
Bin umarninta tayi ganin ba wasa a
fuskarta ta wuce sumi sumi tabar
kitchen din
Dafe kanta ummy tayi bayan fitarta
tana mammakin irin wannan rashin
kunyar ta 'ya'yan zamani
Yanzu su rasa inda zasu baje kolin
iskancinsu sai a dakinta?
Dama tun dawowarshi gidan tana
lure da take takenshi
Ko tsiramata idanun dayake a dining
duk lokacin cin abinci tana sane
shiyasa wani sa'in idan abun yaso
yin yawa saita tashi tabarmasu
dining din
Su ke abinsu amma ita ke jimasu
kunyar
Jiya jiyan nan tazo ta taddasu zaune
afalo qasa k**ar su shige jikin juna
saidai tajuya tafasa yin abinda ya
sauko daita, daga baya ma saidai ta
aika baby takirata ganin har isha'i
na niyyaryi bata dawoba.
Hakan be isaba sai gashi the same
day da daddare ganin har kusan 10
bata shigoba k**ar yadda tasaba
yasata fitowa ta leqa dakin baby
taga wayam sai babyn kadai daketa
sharar barcinta
Fitowa tayi tana wondering ina take
Ganin kwayakwan falo a kunne
yasata Saukowa taga ko tana anan
saidai me kafin ta qarasa ta
hangosu manne dajuna a dining
hakan yasata juyawa bashiri takoma
inda tafito
Yanzu kuma wulaqancin nasu harya
kai yanzu su rasa inda zasu baje
kolin rashin kunyarsu sai a dakinta?
Kai gaskiya tana ganin rayuwa,
dolene ma ta tarkatasu ta korasu
kafin sujamata abin kunyar dayafi
wannanWasa wasa tun tana tsumayen
fitowarshi har abin yafara bata tsoro
jin shirun yayi over
Jan stool tayi ta zauna ta zabga
tagumi tana jiran taji koda motsin
daya daga cikin su ne
Ita sai yanzu ma take danasanin
riqe saudart, dama ummar sadeeq
taja mata kunne akan haka tace
tsakanin miji da mata sai Allah
qarshenta tazo taji kunya gashi
hakan kau yafaru
Ita wai nan riqeta tayi don ta garashi
yasan muhinmmancin ta Ashe ja'irar
6ulamata qasa a ido zatayi
Aiko tunda abin hakane gwara suzo
Susan inda dare yayi masu, bata
iyawa
Jin qauri ya turnuke kitchen din
yasata saurin tashi ta kashe gas
cooker din tana bude tukunyar dake
akai
Ganin abin ciki yafara kamu yasata
jan tsaki ta dauko wurin kwashewa
ta kwashe tana ayyana dolene ma
suzo su k**a gabansu bazasu
maidata uwar banza ba
Tana cikin jiqa tukunyar datayi
kamun a sink taji motsi abakin kofa
Waigowa tayi s**a hada ido da
ashraf da saika rantse da Allah ba
shi ta k**aba ya saka Yar mutane
a corner don yawani maze k**ar
babu abinda yafaru
Dauke kai tayi tacigaba da abinda
take
Qarasowa ciki yana cewa
"Ummy yau ke ke breakfast din?
Ina maid din?"
Bata ko dagoba tace
"Na aiketa" a gajarce
"Ayyah nashiga dakine naga ban
gankiba shine nace bari nazonan
Ashe kina ciki ma"
"Hmm" kawai tace don ita bawai
son firar takeba ita in so samune
ma yatafi yabata wuri
"Ummy to nidai zan wuce office
munada aiyuka masu yawa baxan
iya tsayawa yin break ba, nayi a
office"
Cikin zuciyarta tace
"Jikayi nace katsaya dama?"
Amma a zahiri tace
"To Allah ya tsare, take care"
batareda ta juyoba
Da amin ya amsa yafice yana
mammakin wannan tsare gidan na
ummy, watsar da tunanin yayi
tinawa dayayi aidama haks take yan
kwanakin nan dukdan saudart
amma yasan maganinta Ai idan
tasan wata Ai batasan wataba
Koda yafita saida ta jima sosai a
kitchen din kafin tafito tayi shahadar
komawa saman
Kamar yadda tazata bata taddataba
dakin hakan yasa ta maido dakinta
ta rufe tana sauke Ajiyar zuciya
Bin dakin tayi da kallo taganshi tsab
tsab. Kada kanta tayi ta wuce toilet
tana ayyana dolene ma su tattara
subarmata gida😆
A bangaren saudart tana samu
ashraf yafita tayi sauri ta ida gyara
dakin, batajin tana iya hada ido da
ummy dukda batasan meya faruba
amma gani take data kalleta zata
gano abinda yafaru, hakan yasa
tana gamawa ta lalla6a tabar dakin
takoma na baby
Ummy kau maid dinsu takira akan
taje tasamu saudart dakinsu
tayimata maganar breakfast don
ahalin yanzu batajin zata iya facing
dinta
Saudart kau bata kawo komai
aranta ba ta sauka tayi break dinta
abubbuwan das**a faru dazun
naqara dawomata a qwanya,
dolene tadan ja dabaya da ashraf
idan ba hakaba watarana kunya
za'aji, yanzu ace dazu ummy
tashigo ta gansu ahakan ina zatasa
kanta? Dolene ta tak**ashi birki
tunda taga k**ar kunya be
isheshiba (ruwa k**e yarinya😒)
Yinin ranar ummy bata fitoba bare
su hade, gwara gwara ma da baby
tadawo sun shigo tareda saudart
dakinta akan lunch sai cemasu tayi
suje suci kawai she's busy
Ba wanda yakawo komai aranshi
s**a fita don zuwa suci, baby na
bata labarin yadda exam din yau
yayi zafi.
***
Zaune take a dakinta tana dudduba
wasu kaya da za'a kawomata sari
daga China aka bubbugo kofa
Saida tadanyi jimm sannan tabada
izinin shigowa
Ashraf ne yashigo cikin shigarshi ta
jallabiya ash colour da alama daga
massallaci yake don dama ba'a
dade da idarda isha'i ba

18/12/2025

Good morning everyone

Mezanyi ita da ita....Part...... 8.................©®Momma ta sake gyara murya cikin kwantar dakai ta furta “ Don Allah ...
17/12/2025

Mezanyi ita da ita....

Part...... 8.......
..........©®Momma ta sake gyara murya cikin kwantar da
kai ta furta “ Don Allah mama ki bar min ita kinga
ke kina da wasu y’an matan ga hafsa ga nahnah
ni kuwa Allah bai bani haihuwar d’iya mace
haihuwar ma daga ‘ya’ya biyun ba saketa nayi
ba.” Mama ta girgiza kai “ Gaskiyar magana
addarsu ba zan iya ba su wadancan da k**e
magana ina na gansu kun kwashe kun kai can
uwa duniyar turkey karatu, yanzu kuwa ita zan
dinga gani k**ar maryama da na rasa “. Dada
taja tsaki “ kaji min wani zancen shirme Idan da
wanda ya dace ya ri’ke wannan ‘ya ai dijama ce
yo fisabilillahi tana da wata uwar ne bayan ita a
duniya ai itace take da iko da yarinyar nan ba ke
ba daga kawai kin haifi uwarta, don haka na
zartar da hukunci dijama ki tafi da ita ke kad’ai
zaki iya da wannan bararojin mai ido a tsakar ka
ko samarinki sa ladabtar da ita musamman
wancan miskilin kafi mahaukaci ban haushi da
idanunsa kad’ai sun isa hukunta ‘yar banza idan
ta’k**arta ido ai gidan ta tarar.” Wani kallo shatu
ta watsa mata a zuciyarta tace “ sai nayi
maganin wannan tsohuwar kafin ta sheka
barzahu “. Liman da lamid’o murmushi kawai
suke ganin yarda mama ta had’a rai alamar sam
hukuncin dada baiyi mata ba sai dai ba yarda za
tayi da ita. Momma kuwa sai murmushi take
tana sake jan shatu a jikinta. Daga gefe kuwa
imran ne yake ta watso mata harara k**ar ya
sha’keta ta mutu tabbas banda an kusa bikinsa
zai bar ‘kasar da amaryarsa ‘yar abuja zubin
london inji dada da barin’kasar zaiyi kafin a sake
ganinsa kuwa sai an yara. Ya kalli agogo yana
mi’kewa “Momma ya k**ata muyi haramar
komawa saboda akwai abinda dada ya sani a
company ban kai ga hattamawa ba kuma kinga
mota muka biyo “ Duk wannan dogon zancen
yayi shine saboda baya so dada tace kwana za
suyi yamma tayi. Dada ta zabga masa harara da
ficificin idonta na tsoffi “ Ma’karyacin banza Ka
dai ce ba zaka iya kwana anan ba saboda
shegen gwalangwasonka kada kayi
ubanka’karya salihin bawa dashi ko da yake
shima ya zamad’an banza watansa nawa bai zo
ya dubani ba ko don bani na haifo wanda ya
haifi ubansa ba amma ko bakomai ai ubannasa
aminin lamid’o ne, shikkenan dai Allah raka taki
gona ban kuma ce Ka gaya masa ba bare kasa
ya daina min aiken wata da ya saba ko bakomai
ai d’an albarka ne tsiyarsa ta rashin zuriya ta
bishi sahura dai taga takaici da jikanta baya son
ziyara”. Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya
ba har shatu idan Ka d’auke imran da ya sake
kicin-kicin da fuska ya d’aureta tamau ya mayar
da kud’in da yayi niyyar bawa mutanenta da ita
kanta aljihu, yasa kai ya fice bayan yayiwa liman
da lamid’o sallama. Dadah ta gyad’a kai
“jarababbe umma ta gaida aisa gayyar na ayya
ke dai dijama kin haifi ala’ka’kai.” Murmushi
kawai tayi ta mi’ke tana ri’ke da hannun shatu ta
furta “Allah dai ya shirya mana zuri’a bari mu
wuce kada dare yayi don ma mugun gudu yake
a motar “. “ wani irin gudu ki gaya masa ya tafi a
hankali bana son shashanci “ lamid’o ya fada
yana kallon babbar d’iyar tasa cike da kulawa ya
san sosai take jin zafin rad’ad’in mutuwar nan “
kuma ki cire damuwa a ranki kada kije kiyi tunani
har ciwonki ya tashi maryama addua take
bu’kata yanzu, ita ta dace ko bakomai tayi
mutuwar shahada tsakaninmu da ita addu’a
dafatan muma mu cika da imani “ lamid’o ya
sake fad’a yana kallon’yar tasa ba tare da dubi
da hararar da dada take watsa masa ba “ Ba
shakka zamani wato lamid’o a gabana kake
lallashin ‘yarka ta fari kai Allah da ya tsinewa
nasara da ya kawo boka har tayi sanadin rusa
al’adarmu da dane ko inuwa d’aya ba zaka had’a
da dan fari ba b***e har zance ya shiga
tsakaninku tur da wannan wayewa, ko da yake
har gwara kai ba gani ba na tsaya ina magana
da kai da iyayenan zasu dawo da sunyi tur da
haihuwata kai ku tashi ku tafi kada wanda ya
sake dawo min nan b***e ku sake sakani rashin
kunya wai da bakina nake kiran sunan lamid’o
waliyazubillah duk da dai na uku ne kai amma
wa ya san na farko da na biyun Allah na tuba tun
kan ayi suna s**a mutu ai dai kai ne dai na
farkon....” gaba d’aya gurin dariya ake s**a fice
suna mata sallama Momma tace “ Danger
number one “
Ta mudubin motar ya hango fitowarsu da sauri
ya waro sexy eyes ganin da yarinyar aka fito mai
hakan yake nufi wai wannan’yar dajin motarsa
zata shiga kai ina impossible ai da sake.
Ya fito daga motar daidai lokacin’karasowarsu
mommah tace “bud’e motar mana imran,
yamma fa tayi “ ya ‘bata fuska sosai “ Momma
yamma fa tayi kuma gaskiya gudu zanyi sosai
why not ku kwana anan idan yaso gobe nayi
muku booking flight ku taho.” Momma ta watsa
masa wani kallo ta san sarai nufinsa Aysha ce
baya son ta shiga motar bai kuwa isa ba zata
nuna masa ita ta haifeshi “ sannu ubana to yau
d’in za mu tafi idan yaso’karewar gudu ka mayar
da motar taka jirgi bud’e mana malam “ fuska a
d’aure tamau tayi maganar tana mamakin
halayen imran da sam bata san inda ya kwaso
su ba. Jiki a salu’be ya bud’e motar had’e da
mi’kawa Ammar key d’in “ kuje I will manage ko
a hotel ne by morning insha Allah.

Address


2233

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jafar sa'ad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share