19/02/2024
'Yan Banga Sun Kashe Shi Da Duka Kan Bashin Naira Dubu Bakwai (N7,000) Da Ake Binsa A Garin Mararraba
Daga Imran Hayatuddeen
A daren ranar Lahadi zuwa wayen garin Litinin din makon da ya gabata ne wannan bawan Allah mai suna Salisu Abubakar) da ke zaune a Shopping Centre, Mararaba dake kan iyakar Jihar Nasarawa da Abuja, ya gamu da ajalin sa sakamakon bugun da 'yan banga s**a yi masa bisa kara da wani abokin huldar sa ya kai musu kan cewa yana bin sa bashi bai biya sa ba.
Bincikke ya tabbatar da cewa mamacin ya biya naira 33,000.00 daga cikin naira 40,000.00 din da ake bin sa inda ya rage naira 7,000.00.
Abokan marigayin su bada shedar cewa ko a ranar Asabar sai da s**a gayyace shi ofishin su dake jikin tsohuwar Mr. Biggs kan Titin Keffi zuwa Abuja, inda a nan s**a fara bugun sa, inda s**a sake kiran sa a ranar Lahadi wanda s**a sake bugun sa, a nan ne da s**a fahimci sun yi masa lahani, sai s**a dauke shi zuwa wani Cemist dake tsallake a Unguwar Katsinawa inda mai Cemist ya nuna abin ya fi karfin sa sai dai asibiti, bayan da alamu ya nuna cewa ba zai kai labari ba, sai s**a yar da shi, s**a ranta a na kare.
Muna fata Allah Ya gafarta masa YA sa aljanna ce makomarsa.
A karshe muna kira ga hukuma da ta yi tsaye wajen magance irin wadannan matsaloli da ake yawan kokawa da shi kan irin wadannan kungiyoyi na mafarauta da 'yan banga tare da bin kadin wannan bawan Allah da hukunta duk mai hannu a cikin wannan danyen aiki.