
04/07/2025
Gwamnatin Taraiya ta buɗe cibiyar fasahar sadarwa da aka ƙona a lokacin zanga-zanga a Kano
Gwamnatin Taraiya ta kaddamar da cibiyar Fasahar Sadarwa ta Zamani (Digital Industrial Park) a Jihar Kano, wacce aka ƙone ta yayin zanga-zangar matsin rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta 2024.
Ministan Sadarwa da Fasaha, Dr. Bosun Tijani, wanda ya ƙaddamar da cibiyar a madadin shugaban kasa, ya yabawa kamfanin IHS Nigeria saboda gaggauta sake gina cibiyar ba tare da amfani da kudin gwamnati ba.
A cewar Tijani, an kafa cibiyar ne domin baiwa matasa damar koyon fasahar zamani don taimaka wa rayuwarsu.
Ministan ya ce lalata cibiyar, lokacin da ake da da buɗe ta a bara, abun takaici ne, inda ya ƙara da cewa "amma takaicin bai kashe mana gwiwa ba har sai da mu ka sake gina ta."
A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce cibiyar alama ce ta jajircewar jihar wajen tallafa wa matasa da bunkasa tattalin arzikin su.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa , Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce tun shigowarsa Gwamnati a 2023, jihar ta mayar da hankali kan shirye-shiryen da zasu tallafawa matasa a fannin sadarwa.
Hukumar NCC, ta bakin shugaban ta na ƙasa, Dr Aminu Mai ta bayyana cewa an kafa irin wannan cibiyar a Borno, Ogun da Enugu domin samar da sabbin masu fasaha a Najeriya.
Maida ya ce irin waɗannan cibiyoyin za su yi amfani wajen bincike da bunkasa ilimin fasaha don bukatar tattalin arzikin ƙasa.