Imam karafi sani

Imam karafi sani ANNABI NE MAFITA
(3)

Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Roberto Carlos, ya karɓi addinin Musulunci, a cewar rah...
18/08/2026

Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Roberto Carlos, ya karɓi addinin Musulunci, a cewar rahotannin da s**a fito a ranar Talata.

Rahotonnin sun ce Sheikh Jihad Hammadeh, wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke zaune a São Paulo, Brazil, kuma wanda aka sanya cikin jerin mutane 500 mafi tasiri a duniyar Musulunci, ne ya bayyana hakan.

Sheikh Hammadeh ya ce Roberto Carlos ya daɗe yana hulɗa da shi, kuma kimanin makonni huɗu da s**a gabata ya ziyarce shi tare da furta Shahada, inda ya karɓi Musulunci.

Shin wani fata kuke yiwa Roberto Carlos?

MARHBAN BI MAULIDI
16/08/2026

MARHBAN BI MAULIDI

A dai-dai wannan wuri ne Manzon Allah SAW yayi Sallah a wannan Masallacin Sahabi Utbān bn Mālik (RA)Wurin yana kusa da M...
07/08/2026

A dai-dai wannan wuri ne Manzon Allah SAW yayi Sallah a wannan Masallacin Sahabi Utbān bn Mālik (RA)

Wurin yana kusa da Masallacin Jumu'a da Masallacin Qubā'. Utbān bn Mālik (RA), wanda yake daga kabilar Banū Sālim bn Awf ta Khazraj, ya roƙi Annabi ﷺ da ya zo gidansa ya yi Sallah a wani wuri na gidan, domin ya riƙa amfani da shi a matsayin masallaci. Dalilin haka kuwa shi ne, idan ruwa ya yi ambaliya, yakan kasa zuwa babban masallaci. Utbān (RA) kuma makaho ne, amma shi ne limamin mutanensa.

Ya ce: «"Ya Manzon Allah! Lokacin duhu da ambaliya suna hana ni isa masallaci, ni kuma makaho ne. Don haka ina roƙonka ka yi mini Sallah a wani wuri a gidana domin in mayar da shi wurin ibadata."»

Sai Manzon Allah ﷺ ya zo gidansa ya ce: «"A ina kake so in yi Sallah?"» Sai Utbān (RA) ya nuna masa wani wuri a cikin gidan, sannan Manzon Allah ﷺ ya yi Sallah a wurin.

Yayin kallon irin waɗannan wurare masu albarka, ya dace mu tuna wannan lamari mai girma tare da zurfafa tunani da ƙara ƙaunar Manzon Allah ﷺ, muna jin kusanci da tarihin rayuwarsa mai albarka.

Allah ya bamu albarkan ANNABI Muhammadu saww ya sanya albarka a rayuwar mu. Amiin Yaa ALLAH

Fityanu Islamic Centre
August 07, 2026

"Tsarkake Allah Maɗaukaki (Tasbihi) yana nufin tabbatar da cewa Allah Ya ɗaukaka kuma Ya tsarkaka daga duk wani abu da b...
07/08/2026

"Tsarkake Allah Maɗaukaki (Tasbihi) yana nufin tabbatar da cewa Allah Ya ɗaukaka kuma Ya tsarkaka daga duk wani abu da bai dace da Cikawarsa da Kamalarsa ba. Ana yin hakan ne ta hanyar ambaton abubuwan da Allah Ya kuɓuta daga gare su, wato duk wani aibi ko nakasu.

Amma yabon Allah (Hamd), dole ne ya kasance ta hanyar ambaton Cikakkun Siffofinsa, Kamalarsa, da dukkan kyawawan halayensa waɗanda s**a dace da Girma da Cikawarsa."

Yadda Salatin Annabi (SAW) ya zama sanadin biyan bashin wani da ake shirin ɗaurewa Labari mai ban al'ajabi daga Kano.Sal...
05/08/2026

Yadda Salatin Annabi (SAW) ya zama sanadin biyan bashin wani da ake shirin ɗaurewa Labari mai ban al'ajabi daga Kano.

Salatin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) na yaye baƙin ciki da damuwa, kuma Allah yana sanya mafita ga masu yawaita yin sa.

An taɓa samun wani bawan Allah da ake bin sa bashi. Alƙali ya shaida masa cewa idan ranar shari'a ta yi bai biya bashin ba, za a ɗaure shi, domin yana ganin kamar da gangan yake ƙin biya.

Da ranar ta zo, sai ga mutumin ya bayyana da kuɗin bashin cif, sababbi ƙal. Lokacin kuwa zamanin kuɗin Murtala ne, waɗanda a wancan lokaci manyan kuɗi ne.

Alƙali ya tambaye shi:
"Yaya aka yi ka samu wannan kuɗin?"

Mutumin bai ce komai ba, sai Alƙali ya ce:
"Malam, ka ba mu labarin yadda abin ya faru."

Sai mutumin ya ce:
"Salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) na riƙa yi. Daga bisani na ga Annabi (SAW) a mafarki, ya ambaci sunan wata unguwa, sannan ya ce in je wani takamaiman gida. Ya ce zan samu wanda zai ba ni kuɗin."

Ya ci gaba da cewa:
"Da safe na tafi daidai wurin. Ina isa sai na ga wani mutum tsaye, yana kallona. Da ya gan ni sai ya ce, 'Yauwa, ka ƙaraso.' Nan take ya miƙa mini kuɗin a cikin kwali cif, bai ƙara cewa komai ba, sai ya juya ya tafi."

Da jin wannan labari, Alƙali ya ce cikin raha:
"To Malam, ai sai ka ba ni wani abu daga cikin kuɗin nan, ni ma in sami albarka."

Wannan Alƙalin da abin ya faru a gabansa shi ne da kansa ya ba ni wannan labari. Har ma ya ambaci sunan unguwar da abin ya faru a cikin birnin Kano. Idan na faɗi sunan Alƙalin da kuma unguwar, mutane da yawa za su san su.

Iyayen mu da kakannin mu, idan mutum zai yi sallah s**aji ya fiya karanta Tabbat yada Abi Lahabin, sai su kwaɓe (hana) s...
03/08/2026

Iyayen mu da kakannin mu, idan mutum zai yi sallah s**aji ya fiya karanta Tabbat yada Abi Lahabin, sai su kwaɓe (hana) shi, saboda girmama Annabi Alaihissalam.

Wannan ne Wurin da Manzon Allah ﷺ Ya Wuce Lokacin Hijira zuwa Birnin Madinatul Rasul.An gano wani tsohon rubutun Thamuda...
30/07/2026

Wannan ne Wurin da Manzon Allah ﷺ Ya Wuce Lokacin Hijira zuwa Birnin Madinatul Rasul.

An gano wani tsohon rubutun Thamudawa a Ain Darij (عين ضارج), da ke kusa da Al-Abwa' a kudancin Madina.

Masana tarihi suna ganin cewa wannan shi ne Ain Darij da aka ambata tun zamanin Jahiliyya, kuma yana daga cikin wuraren da Manzon Allah ﷺ ya bi ta cikinsu a lokacin hijira zuwa Madina. An kuma ambaci wannan wuri a cikin waƙoƙin mashahurin mawaƙin Jahiliyya Imru'ul Qais, abin da ke nuna tsohon tarihinsa da muhimmancinsa.

Lallai waɗannan wurare suna tuna mana da tafiyar hijirar Manzon Allah ﷺ da kuma tarihin ƙasashen Musulunci."

Allah ubangiji madaukakin sarki ya bamu albarkacin wannan wuri, ya biya mana bukatar mu. Amiin

Daga: Fityanu Islamic Centre
29 July, 2026

29/07/2026

farfesan Ilimi 💥💥💥 Part 9

29/07/2026

farfesan Ilimi 💥💥💥 Part 8

29/07/2026

farfesan Ilimi 💥💥💥 Part 7

Address

Bakin Kasuwa
Chafe
632101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam karafi sani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Imam karafi sani:

Shortcuts

Share